PART 15

2.9K 113 4
                                    

25. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU~~
SadiyA yayi Batula ta Farka a barci tana waige waige sai taga babu kowa a dakin, Gashi tayi tana leke leke, kawai sai ta bude Toilet din asibiti, sai ta hango gurin wanka, ta shiga ciki Ai Kuma dama ruwan kamar jira yakeyi kawai sai ya balle a jikin ta, abin sha'awa ma ya bata Dan taga shower yana ta zuba a jikinta sai ihu take tanaa murna.
General ne ya dawo asibiti sai ya tarar da Salim a reception sai suka gaisa. Salim ya lura cewa general kamar baya kanshi sai suka haura Sama tare, shima ya shiga ya gaisheda sergent da jiki. Sergent ya tambayi Batula Amma General sai yace Mai ya bayarda cikiyanta Amma Har yanxu shiru. Sai dai ya Kara Hakuri. Salim ne yace bari yaje Dakin da ya kawo yarinyar, general ma ya bishi yace bari yaga yanda yarinyar tayi Dan baiji dadin yanda yace Mai yarinyar ta samu Mantuwa ba, Dan ya tausaya mata. Sai suka fita tare, suna shiga dakin sai basu ga kowa ba, ihun mutum sukaji a toilet kamar Ana wasa da ruwa, Salim ya miyar zata fito Amma sun jirata ya kai minti goma bata fito ba har general yaga zaman bazai masaba ya fita. Salim Kuma da yaji shiru sai yayi sauri ya bude Toilet din hangota yayi ga kika jaqwab, Kuma da kaya a jikinta take watsa ruwan. Tana hango shi ta fito da gudu ta rungume shi tana Murnar ganinshi Amma ba halin Magana sai zazzara ido takeyi. Janyo hannunta yayi suka fito yace Mata, ya kike kallo na kamar wata zara'u? Itama tace Yaya kike kallonta kamar wata zara'u? Murmushi yayi itama ta Mayar Mai. Cewa yayi daga yau sunanki zahra Dan wannan zazzara idon da kika iya yi. Ni bana son kina maimaita Maganar da nayi kinji? Itama yanda yayi haka tayi. Abun har ya soma bashi dariya. Abinci ya bata taci sai doctors suka shigo suka yi mata bincike sai sukaje zasu iya tafiya Amma ya kaita inda zata huta Dan bata son stress yanxu.
Da yamma aka sallame su suka kama Hanya. Har yanxu bata bari yaga hoton da Yake hannunta ba har shima bai damuba, Dan yana gini kamar shirmen ta ne. Salim ya Rasa inda zaisa kansa. Har yayi Hanyar gidansu kawai sai yayi tunanin bazai iya kai ta gida ba Dan za'a gane abunda ya aikata. Kawai sai yayi tunanin Gwara ya kaita gidan shi a cikin Barrack, Hakan kuwa yayi, idan ya kaita gurin kanwarshi Rukayya Muhammad zata tona Mai asiri ne shiyasa ya Yanke hukuncin kai ta gidan sa.
Yana isa da ita ya kunna wutacen gidan dama komai sabo ne a gidan Dan shi sabon Ma'aikaci ne a nan, sati daya kenan da aka bashi Aiki anan ko farawa ma Baiyi ba Dan hutun da aka Bashi ne na two weeks da ya Fito daga Barrack din ya buge Batula Wanda yanxu zahra Yake ce Mata. Tare da ita ya tafi gurin sayayya, yayi mata shopping Dan kome yafada shi take Maitawa, idan ya dau English wears sai ta Kara daukan iri daya haka Jallabiya ma da hijabi, da ya dauka sai da ta dau irin sa. Komai yayi shi take Mai Mai tawa. Dazu yayi tun tu be ma da suna tafiya yace subhanallah itama ta Fada. Muryanta ma dariya ya ke bashi Wanda yake saka shi cikin Fara'a kamar ba soja ba, dama dai Salim Kowa yasan shi da kirki da Kyauta da tausayin Talakawa. Amma Babban Matsalanshi shine baya son Fada wannan dalilin shine ya hana shi kai Batula gida. Kuma yasan cewa General bazai yi Maganar shi ba a popsyn shi Dan shima yana da nashi problem din.
Tun daga Haduwan sa Da Zahra ya fara saka Mace a gaba yayi dariya Dan duk abun da takeyi sai ta burgeshi.
Dama Tunda ya gane Ruqayya kanwarshi ce sai ya ta daure fuska wai Popsynshi ya rage sonshi Saboda ita. Shine Yake huci. Baya ma son zuwa gidan ta dan Haushi take bashi. Amma ita tana son shi.
*** zahra! zahra! Yashigo gidan yana kiran sunan ta dan ya neme ta ya Rasa bai kula da tana biye dashi ba a baya, tsugunawa yayi Dan ya cire Takalminshi Canvas dake kafan shi kawai sai Zahra ta Dane Bayanshi tana dariya. Ya gane dariya takeyi sai ya Fara yi kamar zai yi kuka, yana wayyo Bayana, kina da nauyi wayyo! Itama abun da yayi shi tayi kawai sai ya daga ta suna tafiya, yana Murmushi. Yanxu kam idan da sabo ya saba dan yau kusan Wata guda kenan yana renon Zahran shi. Yasaba da ita sosai har yanaji gwara yayi tazama da ita a haka dan baya son ta Dawo Hankalin ta tace batasan shi ba. Yana goye da ita ita Kuma sai dariya takeyi, yace Mata zahra Anya zan iya rayuwa ba ke kuwa? Itama Tace Salim Anya zan iya rayuwa ba kai kuwa?. Maganar ta ya yi Matukar Bashi Maamaki duk da yasan yanxu jifa jifa takan kira sunan shi tun da dai yana ce mata itace zahra shi Kuma Salim. Ya Kara da cewa Ina sonki Zahra Itama Tace Ina sonki Zahra. Bata ga damancewa Salim din ba. Sauke ta yayi yace idan bata kirashi Salim ba bazai goyeta va Dan tayi girma. Ai kuwa taki Fada yana gudu tana binshi. Bata yi wata wata ba kawai sai ta buga kanta jikin Bangon, bata San San da ta Fada kasa ba tana rike da kanta. Salim ko Daga juyawan sa sai yaga ta Fadi kasa yayi sauri ya dauketa ya shiga da ita daki ya kwantar da ita. Yana Mata Fiffita, da yaga ko Alamun Motsi Bata yi sai ya debo ruwa ya zuba Mata, tayi kamar zata farfado Amma shiru. Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun kawai Yake Furtawa ya Rasa yanda zai yi, yanxu idan yarinyar nan Mutuwa tayi yayazaiyi da ransa, Ga rashin ta da zaiyi Gashi Bai San iyayenta ba, Gashi za'a iya cewa shi ya kashe ta tun da dai goshin ta yana jini, ya Rasa Wani abu ke Mishi Dadi. Regrets Kan duk a lokacin yayi na Rashin bincike iyaywn yarinyar da Kuma Rashin Fadawa kowa a dangin shi akan yarinyar. Ya Rasa meke mishi Dadi. Kara komawa wajenta yayi sai ya daga Hannunta Amma yaji ya koma. Hawaye yafara Hankalin shi bai Mafada Mishi cewa ya kai ta asibiti ba. Kuka kawai Yake yi.
**** Yau Wata Guda kenan Ana Neman Zahra Amma shiru kullum Hankalin su General a tashe ne, Barin ma Sergent Ahmad Wanda numfashi shi kullum a Sama Yake,Idan ya sawa Ranshi Hakuri yana addu'anfa sai ya kasa. Sai da Wani Malamin Masallacin Barrack ya daina ganin su Dan ya lura duk sanda sukaje Masallacin tare suke zuwa Kuma idan zasu Fita suna saka sadaka a cikin Box, da ya lura basa na sai ya tambayi inda sukaje a kace mai wai Dayan babu Lafiya Kuma yarinyar su ce Ta bata, sai ya nemi zuwa inda suke yayi musu Nasiha da daukan kaddara Kuma yace musu in shaallah zai saka su a addu'anfa a Masallatai da Dama sannan yace za'ayi dauka Ko Allah zai Bayyanata. A haka suka Rabu da Mutumin.
Malamin kuwa yayi musu sadaka a Masallatai sannan ya ce ayi dauka a Roki Allah ya Bayyana wa Bayin Allahn nan 'yarsu Batula. ** ummulkhair****

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now