part 7

3.1K 97 2
                                    

9.MAKABARTARMU.~ by khadija Aminu~~
Anyi sunan 'yan biyu inda macen ta ci sunan Mahaifiyar su kabiru wato Fadimatu Amma ana kirant da batula, sai Namijin kuma aka sa kishi sunan babansu kabir Wato Muhammad bello. Murna a wajen kabir ba a magana wai shi a dole ya haifi 'yan biyu. Duk abokanan shi na banxa ya gayyato ranar sunan, suka yi shaye shayen su a wajen. Sai daya daga cikin su yace Ba ka ce mun Watanku biyar da aure ba? Ya akayi har ta samu ciki ta Haifu? Duka yan wajen sai suka fara masa dariya suna cewa ko dai ka Afka Mata ne kafin Auren? Sai kabir a muryan shaye shaye yace A'a ni ban gane me kuke cewa ba, ina dai ashe wata biyar ake rainon ciki? Sai duka suka fashe da dariya suna zagin shi wai inji daya daga cikin abokan daya yace Kai Amma kai Jahili ne wlhy, ashe gwara ni. Wai kaji a iskancin ma akwai gwara. Duk sai ya rude yake tambaya toh wata nawa ake Haihuwa? Sai wani yace Tara. Ai kuwa sai yayi wani tunani yace Ina xuwa.
Shiga daki yayi ya samu Hafsat a gefen Gado tana shayar da Macen Namijin kuma yana bacci akan Gado. Zaki ya fara kudunduma Mata wai meyasa Tayi mishi Karya, kawai sai ya janyo bedshit din Gadon da karfi kawai sai ya wurgar da Muhammad bello a kasa. Sai yaron yayi wani irin kara Hannun shi ya balle Gashi kai ya fara fitar da jini. A lokacin Hafsat tayi kara tana cewa Ka kashemun Dana, Na shiga Uku. Kuka tayi Nai isan ta shi kuma ya koma Falo yana Murna wai ya kashe Dan saura 'yar.
Bayan kwana biyu da suna Muhammad bello Allah ya dauki abunsa, sai dai Fatan Allah yasa Mai ceto ne. Amin.
Ran Hafsat ya baci, ba abunda bata zagi kabir ba dashi. Shi kam Bai damu ba, kawai sai ta yanke shawaran Fara tashi sallahn dare dan Allah ya nema Mata mafita. Haka takeyi. KullUm idan yayi mata asiri sai ya karye sbd ita mutum ce mai ibada. A haka dai kullum zama a waje daya kamar a Makabarta ya kama Hafsat. Kullum sai ta nemi Hanyan guduwa Amma ina, a haka har ta rungumi Kaddara na cewa Watarana idan tana da Rabo zataje ta ga duniya.
Bayan shekara uku har yau bata sami ciki ba gashi kullum sai kabiru yace mata yana son ta haifo masa 'yan biyu. Ita kam bata ma da amsan sa zata bashi. Kullum tana tararradin samun ciki, har gode wa Allah takeyi sa bai sa sun samu raboba da kabiru. Kullum tana mafarkin Mijinta da dan uwanta. Ranar ta tashi da laulayin ciki, da kabiru ya gane yayi murna sosai, komai takee so yanayi mata, taga dan canji a wajensa yanxu dan har yana zama yata neman ta da hira, haf ma yana ikirarin cewa duk kaunarta ya jawo mishi irin wannan rayuwar da ya shiga. Yayi tayi kamar yayi nadama. Dama bai rageta da komai ba kamar canxa tufafi da saka turararruka. Sai dai bazata ga koda Mutum daya ba bayan shi da batula. Bayan wata bakwai ta haifi yaron ta santalelen namiji Mai kama da kabiru. Shine wands batula tace bata Mantawa da ranar da aka haifeshi. Hafsat ta nemi a mayar da sunan Ahmad amma sbd kishi yace bazai iya ba sai dai a sa sunan shi sai tace itama baza ta yadda ba a sa sunan Hafizu sai yace waye hafizu anan ta ce mishi yan biyunta ne ya bata. ya dan tausaya mata sai yasa mishi sunan Hafizu.
Bayan shekara biyu sai ta haifi yan biyu aka saka musu una Hassan da husaina. Har wa yau Hafsat tunda ta shigo gidan bata taba Fita ba, ko falo sai ta kai wata bata fito ba sai dai kitchen da daki. Yaran nema sukan fita Falo. Yau shekaran Batula takwas a duniya Haka shekaran Hafsat Takwas da watanni a duniya Amma kamar a MAKABARTARMU. Wanda Hafiz nada shekara hudu a duniya haka yan biyu suna da shekara biyu a duniya. Hafsat Ta danne duk wani abun da kabir ke mata ba bata fada wa 'ya'yanta ba. Kuma bata taba nunawa a gaban su ba. Ita dai tasan kabir na sonta Amma so da son zuciya. Dan kuwa da ya sota tsakani da Allah bazai Mata dole ba, idan rabonshi ce ita Allah zai bashi. Haka Rayuwar Hafsat take. Anan Hafsat ta gama bawa diyarta Batula labarin kanta sannan tace Mata "Batula ki dauka komai ya faru damu daga Allah ne, amma kabir ya kashe Mahaifin ki Alhalin Ina sonshi, bazan taba daina sonshi ba. Ke Marainiyace kamata sai dai ni Nafiki Maraici dan ke kina da uwa.
Batula Wanda Hawaye ya cika Mata ido kawai sai Tace Ammi na (sunan da take kiran Hafsat dashi kenan) Na dauka miki Alqawarin Idan Allah ya yadda zamu fita daga Wannan MAKABARTAR, kar ki cire rai da jin dadi duk da nasan komai a duniya ake yinsa idan anje lahira ba'a komai. Ni Fadimatu Batula zan fitar da Mahaifiyata daga wannan MAKABARTAR. Allah ya nuna Mana ameen ** ummulkhairy***

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now