PART 13

2.6K 88 3
                                    

21. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU~~
Momy ce ta kira wayan general bai daga ba, duk da irn abun da takeyi a ranta da Kuma cikin ta Wanda ale tunanin haihuwa yau ko gobe Amma bai hanata Dauko makullin mota ta Fara gudu har ta bar cikin Barrack din. Dama already tasan cewa A FEREPROD ake kai Sergernt Ahmad. Hakan ya sakata Kara gudu akan titi. Tana ta lura dai ko zata ga Batula Amma Ina Batula tayi Mata Nisa. Kawai sai ta cigaba da tafiya har zuwa FEREPROD. Bata ma gama parking da kyau ba, da rufe kofan ta tafi ba tare da ta saka key ba sai Reception, Tana isa Ta tambayi ward number di aka Fada Mata Dama bata tsaya ta ji room Number ba kawai sai ta kama tafiya. Tana isa Har Za ta shiga Room 1 kawai sai tayi Room two. Da shigan ta sai ta ga Mace a kwance Ana dura Mata drip, Kuma doctors sun zagayeta......

Kuna jirana ne Sai ku biyo Ummulkhair Dan jin lavarin gobe Dan Ina jin bacci. Gud nyt!!!!

22. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU~~
Rufo kofan Momy tayi da sauri ba tare da ta lura da fuskanta wacce ke kwance a wajen ba. Ta nufi room 2, Tana shiga ta nufi gurin Daddy tana cewa Ban ga Batula Ba, ka Kiri Batula. ( Fashewa da kuka tayi tana sheshshekan kuka).
Daddy ne ya fusata yace Haba Rukayya, Na zata zakizo ki kwantar mun da Hankaline akan yanda kika saba, Amma kina tuna mun da wata yarinya da tayi sanadiyyar jefa Dan uwana a Wani Hali. Toh kema ki bi ta idan Haka ne ( Ran maxa ya baci).
Motsin da sergernt yayi shi ya Mayar da Hankalin su duka sukaje gurin shi duka a take suka tamvayeshi Yaya jikin?. Anan ya kalle su duka yace Ina Batula?. Shiru ne ya biyo Baya sai yace kar ku barta ta tafi Dan Allah General kayi Hakuri, Amma yau zan fada Maka Gaskiya, tun ranar da naga Batula, ban San meye a game da ita ba da naji Ina son ta ba. Kawai naji Baxan iya rayuwa ba ita ba. Daga Farko Ina ganin cewa tayi mun karanta Amma yanxu Gaskiya Ina sonta, kar ka gani kamar akan yaudarane, kar ka zata Baxan iya auren yaruwar ka ba idan mun sameta ba. A'a. Ina son ta Har yau har gobe. Ita na Fara so Kuma ita zan ta so. Amma Dan Allah kar ka Hanani auren Batula.....
Sai da ya gama Maganar shi, Momy ma ba ki a bude a ta Rasa da fushin Mijinta zataji ko Da shirmen da sergernt. A take zata bude Baki tayi Magana sai general ha tsayar da ita cewa Baya son jin Muryarta Kuma ta koma gida Dan ta bar Amatullah ita kadai a gida, idan Kuma baza ta koma ba Ta bi Batula.
Bata son ta Bata Ran Mijin ta sannan Tace shi kenan zan tafi Amma idan Baka nemi Batula Ba kai da kanka zakayi kuka, ni zan koma gida, Kuma ka kallo wadannan Photunan zaka Gane wacece Batular da ka kora. Ajiye hotunan Tayi a gefe ta fita Ba tare da ta sake cewa komai ba. Ta bar asibitin. Bai yi Niyyan duba Hoton ba Dan Haka daukan su yayi ya saka a dust bin din asibitin.
***** Salim ne popsyn shi Yake kiranshi a waya yaki daga wa. Abu daya ya Lura da ya tsaya yana kallon Batula. Ya Lura Da photo Enlargement din da Yake rike a hannunta duk da irin wahalan da Tasha Amma bata sakeshi ba.
Salim ne yaje gefen ta yana kallonta ya lura da ita yarinya ce sosai ya ka idan ce Mata shekarunta sha hudu a duniya, sannan ya Ga ita doguwa ce, Mai Hasken Fata, tana da Manyan ido. Tana da Gashi Dan hijabin jikinta ma an cire mata yana gefe. Hoton Hannunta ne kawai ba a iya cirewa ba Dan ta rike shi Gam Gam.
Salim ne ya bia hankali Dan ya cire hoton a hannunta kawai sai ta bude idon ta. Ihu ta sanya sai da ya Lallabeta sannan ya tashi ya dau waya Dan Fada wa nurses cewa ta tashi. Kallonshi take tayi ta Rasa me zata ce Dan kanta na tayi Mata ciwo. Komai a ka Fada shi take tuna wa. Komai taga Anyi shi takeyi. Gani tayi Salim ya daga Hannun sa Sama, itama sai ta daga, nurses ne suka shigo, suke Tambayanshi abin da Tayi yana Fada musu details din. Sai sukaBashi assurance cewa zata samu sauki. Gobe Ma idan doctors sunxo zasu dobata su gani. Yanxu kam ma by this tym karfe 11 na dare ne. Ko abinci bai ci ba Allah ya hada shi da Jarabawa.
Sallama yayi musu yace Dan Allah wata ta kwana da ita Amma shi zai koma gida. Sai gobe zai dawo. Komawa Dakin yayi yana kallon Batula Wanda duk abin da yayi shi take imitating. Abin ya so ya tashi dariya. Ai kuwa Murmushi yayi itama tayi Murmushi. Cewa yayi wonderful itama sai tace wonderful. Yace Gobe zan Dawo kiyi Bacci Lafiya, itama tace Gobe zan Dawo kiyi Bacci Lafiya. Yace Allah ya Kara sauki itama tace Allah ya Kara sauki. Ya je kusa da photon Hannunta yace Dan nuna mun wannan Mana, itama ta maimaita d same thing da yace. Yace in gani mana, tace in gani Mana. Ya janye a hannunta zai kalla itama ta janye a hannunta. Haka suka dinga yi har ya hakura da Ganin Photon. Yayi Hanyar waje yana Daga Mata Hannu itama ta Daga Mai Hannun. Ya juya ya wuce itama tashi tayi ta bi Bayan sa. Yana tafiya da sauri itama tana binsa a baya. Ko Wani irin Taku yayi sai Tayi. Yana isa bakin kofan Motan sai ya duba key din Mota sai ya tunada ya barshi a daki. Yana juyawa sai yaga Batula Na binsa a baya. Janyo ta yayi yace meyasa kika fito? Itama tayi yanda yayi da fuskanta tace Nima meyasa kika fita, har da lankwasa kai yanda yayi.
Da gudu ya tafi dakin Dan Dauko keyn yaga still kome yayi sai tayi sai ya kirawo nurse din da ya roka ta kwana da ita. Nurse since taja ta suka tafi Amma Ina kuka takeyi tana ihu, Tana ihu ne kawai. Bata San kome Mutane ke cewa ba. Salim kam ya ta tafiya abunsa ko juyo wa baiyi ba yayi tafiyansa, Dan baya so Fadan da za'a MASA yayi mASA yawa. Batula kam hanyar da ya wuce kadai take nunawa. Haka Mutane ke ta shigowa suna kallonta Wanda Hakan ne yayi sanadiyyar Barin General dakin, at d same time, cleaner ya shigo zai juye dust bin Dama idon sergent a bude ne Kuma yaji duk abin da ya faru tsakanin momy da Daddy. Daurewa yayi yace wa cleanern ya miko Mai Hotunan dake cikin dustbin din Ai kuwa cleanern sai ya mika wa Sergernt hoton. Yana bude Hoton, kallo yakeyi cikin Mamaki da rudani. Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Yake furtawa. A sanda ya ga hotunan. Hoto Na Farko Hafsat ce a hoton Aurenta da Ahmad, na biyu Sergernt Ahmad ne da Hafsat, Na uku GENERAL ne da Hafsat. Na hudu Hafsat ce Da su Hajiya iya da kowa a Gidan da ta zauna na Misau, Haka ya dinga Ganin hotunan Wanda a take ya General ya gano wacece Batula. Batula 'yarsa ce Ta cikin sa. Ammaa Ina ta bar Hafsat ta Taho ita kadai? Meya samu Hafsat Bayan Rabuwarsa da ita. Wannan Amsa kawai a wajen Batula Yake Neman su.
shigowan General ne ya sa ya dago kanshi daga kallan hotunan, idon shi cikin Hawaye.***ummulkhair****

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now