PART 12

3.3K 78 0
                                    

18. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU~~
Ammi ce Zaune tayi tagumi, sai yanxu da taji shirun nata yayi yawa, take yawan tunanin Batula. Ko Wani motsi tayi sai taji ta a ranta. Kullum addu'anfa Allah ya dawo Da ita da Alkhairy Kuma ya fitar dasu a wannan ukubar da suke ciki na zama kamar a MAKABARTA. Abubuwa da dama sun shine a rayuwarta, Ammi yanxu a kalla tana da shekarunta talatin da uku yanxu rabuwarta da mijin ta shekarunta sha uku kenan. Bata da Wani hope din Kara ganin sa. Yanxu kullum addu'anfa shine Allah ya dauki ranta ta huta. Duk da cewa zaman da takeyi yanxu ya bambanta da na da, yanxu takanji hayanigar wasu Biladama. Amma yarata na zuwa Makaranta. Itance dai kawai bata da Aiki sai zaman gida, wankin yara, guga, da wankin ta da girki, da wanka. Ko kwalliya bata yi dama dai tana da kyau dinta. Jikin nan nata kullum a cikin taushi Yake Kara wa. Kunsan mata idan sun zauna guri daya abin ba dama dan kuwa Kara haske suke da freshness. Sai dai ita zama guri dayanta da cutarwa Wanda shi kadai ne bazai barta tayi kiba ba.( maxa bance fa ku kulle Matanku ba Dan kuna so suyi fresh).
shigowar su hassan da husaina da Hafiz ne ya sanya ta daga kai da tunanin da takeyi. Suka dawo kawai sunanta suka kira ba Wani walwala kamr yanda yara sukeyi idan sun dawo daga Skul. Ana Mama oyoyo. Basu iya duk wannan ba. Kawai suka ajiye kayansu suka zauna kamar yanda ammin ma ta zauna. Abinci taje ta zubo musu sannan ta koma daki ta cigaba da sana'a wato tunani. Kullum dai haka rayuwarta Ammin Batula Ba Dadi.
***** a gidan general Kuma batula da Amatullah sun gama exam na juniro waec ta shiga kitchen ta daga musu indomie. Tana gamawa sai ta zubawa Amatu a kwano daban Dan bata son jagwalgwalon Amatu. Sai tasa nata ta ajiye akan dining. Zuwa tayi kitchen ta dan saka ruwan zafi Dan tana son shan Lipton, Daddy yayi yayi ya hanata Amma taji. Mommy ma kullum idan ta ganta tayi sai ta mata tsegumi, har ce mata takeyi wai shiyasa kullum bata Kara kiba. Abun yata bata dariya. Yanxu kam Batula is very friendly.
Taje gun dining table don taci abinci kawai sai ta tarar da empty plate Kuma ba kowa a wajen. Mamaki tayi Dan tasan ba kowa a gidan Momy bata nan dan taje biki Garin su Gombe, daddy ma ya fita aiki. Amatu Kuma bata gama cin na gaban ta ba. Haushi taji kawai ta figi plate din sai takai kitchen da ta dawo falo Kuma Dan Tasha Lipton din tana kumbure kumbure ji takeyi kamar ta wapce na Amatu ta cinye. Dama Amatu ma Mayyar indomie ce bata rage koda tsilli daya ne. Tunani takeyi kawai sai ta juya ko zata hango mutum a falo. Ai kuwa sai taga sergernt ya kipa kanshi da gwiwan shi. Tafiya tayi da gudu wajen shi sai tace da zan maka oyoyo ne Amma na fada Dan ka cinye mun indomie na Kuma Ina jin yunwa. Ni sai ka biya ni Indomie na. Tashi yayi yana kallonta kawai sai yayi mata murmushi yanda tayi ma dariya ya bashi. Sai da yayi Mai isarshi sai yace, kinga daga filin yaki nake, nayi wata biyu banci abincin daughter ta ba. Da na dawo Kuma sai naji Kanshi. Dama yunwa nakeji. Shine na cinye Ashe nayi laifi, marairaicewa yayi a gabanta sai abun ya bata dariya sai tace toh Abbyna bakayi laifi ba. Amma dai tunda kai kaci ka koshi ni Kuma karfin aiki na ya kare sai nima ka shiga kicin ka girka mun Indomie. Toh Daughter yace sai yayi gaba. Ai kuwa kyaleshi tayi yana kicin yana girki can sai taji tausayin shi take ga karba tace Da kayi mun musu da sai kayi Amma tunda bakayi ba kawai ka barni inyi. Bata ita karban girkin a wajen shi  ba Dan yaki yana cewa bazai bar Daughtern shi ta wahala ba.tunda tana jin yunwa.
Da ya gama ya mata komai ya kai mata dining tana biye dashi a baya. Murna take tayi har ta gama cin abincin tana ta gwada dadin abincin. Yana kallonta ta tana abu Amma tunani kawai yakeyi.
Dama Ramadan za'a Fara lokacin Ai kuwa a kwana a tashi an kusa gama azumi sai General yace munyi shekara uku kenan bamuje Sallah gida ba. Ina son muje gida duka tare. Sergernt general ya kira yana cewa yana son suje gida tare wannan sallahn. Sergent dai bai ji Dadi ba Dan shi a rayuwarsa Baya son a tuna Mishi da gida. Dan yasan bashi da sauran Gata.
***ummulkhair******
19. " Batula zamuje gida ranar Ja jubere( gobe sallah kenan)" Batula ne tayi Murmushi sannan tace  Daddy Nagode da irin rikon da kuka mun duk da baku tabajin daga inda Nake ba."Allah ya biya ku duniya da lahira. Zanyi missing dinku Dan bai kamata ace in zauna a cikin gata ba Mahaifiyata Kuma da kannena suna cikin MAKABARTA ba. Dole in Naima Musu Mafita, kullum da tunanin su nake kwana nake tashi. Da a tunani na sai na zama Mai kudi tukun na in nema a Ammi na gida, in kaita. Da a tunani na sai na saya mota tukun na in Dauko ta a ciki in kaita gidan da na saya mata sai mu zauna tare har karshen Rayuwar mu. Amma jiya Nayi Mafarkin Ammi na tana kuka, tana kirana, tana Neman Mafita, sai ta na ta kuka wai Allah ya dauka Ranta. Kwai sai naga zata Fada Rijiya, Ina zuwa sai na riko ta. Daddy Dan Allah ka yafe Mun Narashin Fada Muku Rayuwarta ta baya. Dan ina Gani kamar zaku Mayar dani ne. Kawai Wani abun da Ammi ta ta bani Lokacin da Nake shirun guduwa. Ta bani Laalita yana dauke da kudi a ciki, da hotunan ta. Nasan ba abunda kuka rageni dashi, shi yasa banyi amfani da kudi ba. Kuma hotunanta da ta saka a ciki Bana bude wa Dan yana sakani kuka Kuma bana son ko momy ne ta gani Saboda kar ta Gane cewa Ina da Wasu dangi. Banyi hakan Dan Munafurci ba Dan Allah ku gane, ku yafe Mun." Kuka takeyi Mai tsuma zuciya kowa da abin da Yake tunani. Daddy kam tashi yayi kawai yayi gaba Dan Ranshi ya baci. Sergent kuma baya son kukanta kawai sai ya janyo ta ya rungumeta, shima yana ta tausayinta. Sai da tayi kuka Mai isarta sannan ta tashi, ta koma daki. Shiryawa tayi cikin shiga ta kamala, da Yake tana da tsawo sai ka zata 'yan mata ne yan shekara shashidan nan. Ta Dauko hijabinta Mai hannu ta saka. Ta janyo wannan Laalitarnan Wanda tun shekara uku baya bata taba bude wa ba sai dai boyewan da tayi a karkashi carpet din dakin. Cewa tayi zama Bai kamani ba. Duk karantata bazan bari Ana cutar Mahaifiyata ba. Hawaye fuskanta ta gama sharewa sannan ta hango babban hoton da ke Makale a jigin bango, itace da Amatu da Momy da Daddy da aby( sergent) . Hawayenta ta goge sannan ta hau kan kujera ta janyo hoton sai tace ko baza a ban komai ba Ina son a bani wannan hoton Dan dashi zan Ina tuna ku har in gama rayuwarta. Idan ma MAKABARTARMUN zan koma sai inta kallo.
Ji tayi kanta ya Sara ta fara kukan rabuwa Dan bata son Fita a gata Amma Yaya zatayi? . Ta gama Mai isan ta sai ta tashi, ta Dauko Laalitarta zata bude kawai sai Taji Daddy ya kira sunanta. Ta daga kai zatayi hawaye kawai sai yace Mata hawayen karya kukan karya, sai kin Fada min Task din da ya kawo ki gurina, bayan kin saka mana sonki Kuma kinzo kina tunanin tafiya, gashi yanxu Abbynki ya Fadi ciwon shi ya tashi Wanda ya dade bai tashi ba. Kin ga abun da kika jawo mana ko?. Fita yayi a dakin.
Mutuwar tsaye tayi na Dan lokaci kadan ta rasa abin da zatayi kawai sai ta Fadi kasa a Zaune tana Salati. Dama ta bude laalitar kawai sai abubuwan ciki suka fado kasa. Hotunan ne suka watse a kasa, ta kallo kasa kenan sai ta ga hotunan nan *** ummulkhair****
20. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU~~
dishi dishi ta gani Wanda duk hawaye ne suka cika idon, ta Rasa yanda zatayi. Kawai dai tabar komai a watse a wajen tayi hanyar Falo, sai taga Daddy ya daga shi sai ya saka shi a mota Saboda numfashin shi yana ta daukewa. Batula ce tayi sauri ta iso su sannan ta roki Daddy cewa zata bisu Amma Daddy yace A'a ba tace zata tafi ba, toh tafi kar ta Kara dawowa Tasa musu ciwon zuciya. Kuka takeyi Mai tsuma zuciya tana Daddy kayi Hakuri . plz Forgive me. Be jira ta gama Magana ba ya shiga mota ya ummurci driver da ya tafi dasu FEREPROD Dan anan ne Yake da file Dan Military hospital din basa daukan Manyan case irin na Sergernt. M sry to say Na manta ban Fada Muku cewa sergent ya koma command sergernt major ba Bayan rasuwar commandernsu a cikin shekarunta ukun.
***** Momy tana tsaye duk taji abinda Yake Faruwa, ko Amatullah da bata San abin da Yake Faruwa ba da ta fito da Enlargement na hoton su biyar ta fara cewa Addana( dan haka take kiranta) ,ganan hotonmu nida ke da Daddy, da Momy, da...... Rungumeta Batula tayi sai ta karbo hoton tana cewa Nagode, Nagode, Nagode. Sannan ta sake ta ta rungume hoton a kirjinta tana hawaye. Tafiya takeyi kawai Bata San Hanyar da take ba. Kawai tayi hanyar Bakin gate din barin Barrack. Momy tayi kiran Harta gaji, da Yake lokacin Momy ma tanaji da nata cikin Dan tana da tsohon ciki Kuma Mai wahalar da ita. Da kyar take taka wa, ciki Mai girma sosai Wanda ake tsammanin 'yan biyu zata Haifa. Allah ya sauke ta Lafiya.
****sun isa asibiti emergency room aka kai shi Dan an riga an San shi. An saka mASA oxygen Daddy kuwa sai kuka yakeyi.
Batula Kuma ta fita daga Barrack tana ta tafiya Amma motoci ne kadai Yake wucewa, kunsan Abuja. Tafiya take Amma ta kasa Ganin karshen Barrack din. Abun wasa ta hango yana juyawa a Amuzement park na gurin aso rock, sai ta ce bari tayi sauri ta isa wajen Amma sai ta tsallaka titi. Tana kokarin tsallakawa ne Dan bata hango mota ba tayi da gudun ta ta tsallaka, ko na farko bata tsallaka ba motar da ta tafo da gudu ta buge ta. Kadan. Da kyar yasaka burki, ya tsayar da motan. Ganin ba Wanda Yake Hango shi kawai sai ya dauketa yayi Asibiti da ita. Da Yake ba Wani jini jikinta Yake yi ba kawai dai ta bugu ne sosai. Shine aka Amsheta a asibitin FEREPROD. a emergency room. Dan An San Salim Saboda asibitin suna zuwa saboda Popsynshi yana aiki a CBN Kuma is one of the registered hospital da ake kai patiante dinsu idan sun kasa treating dinsu. Sai a biya su daga baya. Amma if it is a case of emergency ba'a tsayawa tambayan referal letter ko Wani abu. Shi kam Salim Niyyanshi ma a kudinshi zai bada after her treatment.
Salim kuwa( Wanda ya bugetan) ya ga tashin Hankalinta Dan bai San irin Fadan da zai sha ba A waje Popsynshi idan yaji kadan da yayi tunda dai ya Hana shi tuki da gudu.  Hankalinshi yayi mugun tashi. Saka ta akayi mata computerized axial tomography (CAT) scans.  Dan bata farfado ba har lokacin Amma still tana numfashi.
Bayan doctor ya fito sai ya tamvayi a kira mASA Wanda ya kawo yarinyar nan. Salim sai ya bude dakin Doctorn. Yana shiga bai ma zauna ba sai da aka ce Mai ya zauna.
Doctorn ne ya tamvayeshi matsayinsa a wajen yarinyar sai yace brother ne Doctorn bai musa ba Dan kuwa sunyi mishi dibi Dan kamar zubin Fulani suke.
Doctorn Cewa yayi ya akayi ka bar karamar yarinya tana tunani Mai zurfi haka? Wani irin cutarwa ne wannan For God sake. Doctorn bai ma iya Hausa ba Da turanci yake magana. Ta inda ya shiga ba tanan Yake fita ba sai da Salim ya dakatar dashi yace, then tell me what happened. What is wrong with her. The doctor started telling him that  Her memory is Loss, Salim ne ya daga kai hawaye na gangara daga idonshi yana cewa Na shiga uku, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Doctorn ne ya fara mishi Maganar cewa ya kamata ya tsaya yaji Komai akan Memory loss kar yayi sautin karaya. Salim ne yace Wani irin memory loss Kuma? Sai Doctorn yace: memory loss yana Faruwa ne Bayan an buga Kai , mutum baya tuna ko shi waye ko Kuma daga inda yazo. Amma fa kar la damu Dan yana faruw a a ko Ina yanxu. Yana Kuma damun Al umma dayawa. Amma Fa it is Ita nata loss of short term memory ne, zata iya tunawa da kanta watarana. Kawai abubuwa da dama da Yake janyo loss of Memory kamar Magunguna ma suna janyo loss of Memory kamar su, :antidepressants,antihistamines, anti-anxiety medications, muscle relaxants,tranquilizers, sleeping pills, da pain medications given after surgery. Shaye shaye ma kamar Alcohol,tobacco yana kawo Memory loss. Smoking ma yana kawo oxygen din dayake shiga kwakwalwa ya rage shiga har ma ya dawo mutum ya manta da abubuwa da dama. Stress ma yana kawo wan Loss of memory. Sai Wanda ita Kuma yayi mata causing shine Head injury, zai iya zama Accidentally ko Kuma ita ta buga kanta da kanta, shiyasa ta samu mantuwan kwakwalwa Wanda muna tsammanin Short term memory loss ne Wanda zai iya improving.
Bayan ya gama mishi Bayani. Salim ya fito dakin sai ya nufi gurin nurses din ya tamvayi dakin da komai daaka kaita. Bayan yaje Dakin Har lokacin bata Farfado ba. A room 2 ward A aka kwantar da ita.
*****
General ne ya fito daga Room 1 ward A yana daga kai ya rasa yanda zai yi, dai dai nan Shima Salim ya fito yana Hawaye kadan kadan.
Hada ido suka yi Salim bai San sanda ya gyara tsayuwarshi ba irin ta sojojin Nan yana kakkandare wa. General ne yace Nan fa asibitin muke, koi ma da abun da kakeji nima da abun da nake ji. Ni ba kowa bane da zaka sara min anan. Plz ka gyara. Salim ne ya gyara sannan yace sir wa ka kawo ne asibitin da kanka haka Dan banga kowa a tare da kai ba.  Sai yace Sergent Ahmad ne ya Fadi ciwon shi ya tashi. Yanxu haka ance zuciyarshi ta kumbura kuma ciwon nashi ya dade bai tashi ba. Allah sarki kawai Salim yace sannan ya ce nima wata yarinya Na buge a hanya Amma bata ji ciwo ba sai dai internally yayi affecting brain dinta. Kuma Ina tsoron kar popsy na ya mun Fada dama dai can ya hana ni gudu a mota Amma bana ji. Hawaye ne suka zuba a idonshi. Sannu kawai general Yake cewa Dan yasan abunda yakeji.
*  Momy madai kama hannun Amatullah tayi suka shiga gidan tare hankalinta a tashe, ita dai bata so tafiyan Batula Ba, taso ace fa zauna Dan hukuncin da Daddy ya dauka ta tabbata ba a son ranshi bane kawai dai ya fada ne. Hanyar dakin Batula tayi don taga abin da Batula take shirinyi kafin ta fita.
Shiganta keda wuya sai ta tarar da hotunan cikin Laalitar nan. Wanda ya zube a kasa. Kallonta Hotunan tayi daya Bayan daya, hankalinta ta a tashe ta Fara kiran Innalillahi wa inna ilaihir Raji'un. Hafsat, Hafsat ce!!!!!! Ammin Batula Hafsat ce!!!! *** ummulkhair****

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now