PART 14

3K 86 3
                                    

23. MAKABARTARMU~~KHADIJA AMINU~~
Batula dai ta gama kukanta tayi Bacci. Salim dai da ya koma Gida Karya yayi a gida kawai wai ogan sa ne ya kira shi shiyasa Bai dawo da wuri Ba. Suka Gaisa da popsyn shi ya Kara Gaba. Ya tafi Daki yana ta tunanin Batula da irin Shirmen da take MASA. Da tunanin ta ya kwana ya Tashi.
General ne Da ya lura da irin Hawayen da ke fuskan sergent sai ya yi sauri yazo wajen shi yana son jin Dalili Amma Sergernt ya kasa Magana sai kallon Hotunan yakeyi yana kokarin Magana Amma Ina ya kasa. General ma ya saukar da idon sa sai yaga hotunan da Yake kallo. Ido Daya ya saka sai yaga Hoton Auren Hafsat ita Kadai a Zaune. Wannan jinina ne wannan Hafsat dita ce, yana Kallon Hotunan daya Bayan daya yana Neman Mafita. Innalillahi wa inna ilaihirrajiun kawai Yake Furtawa sai yace Batula 'yata ce, 'yatace. 'Yar Kanwa Tace Fa.
Sai dai abun Tambaya Ana shine 'yarkace Batula ko 'yar Dan uwanka? Ina zan samu Batula Ta Fada mun inda Hafsat take Dan in share mata Hawaye. In Rage Mata Bakin cikin Tashin Iyaye. Allah!! Ka yafe Mun sautin Fushi da sauri yanke hukunci ya janyo mun korar 'yata Ahmad. Allah ya aiko Mana ita cikin sauki Amma Mun Kore ta. Na koreta a gidan, Wani Hali take ciki yanxu?.
Bakin ciki Ba kadan ba General HAFIZ ya shiga a lokaci daya ya juya da tuno da abun da suka shude Wanda a lokaci kankani ya rame, ya zama kamar Karamin Yaro.
*** shekaru ashirin Da biyar da suka wuce idan Baku Manta Ba a kauyen Luggudi, abubuwa da dama Na Mutuwa da rayuwa sun Faru. Hafizu yana shiga dajin nan Dan nemo Maganin nan saiBai samu ba Kuma yana tsoron kar kafan 'yar uwarshi Hafsat ya samu Matsala wajen tafiya, kawai sai yaga Gwara ya tsallaka Babban titi ya ciro wannan Ganyen Da ake Maganin dafi. Ya tsallaka Titi ya ciro ganyen. Ya dawo kenan don yaga Magariba yayi sosai, gudu yakeyi sosai, ko lurada titi Baiyi ba ya tsallaka Kuma dai dai nan motar da tadoso da gudu Dan Baiyi tsammanin samun Mutum takan hanya ba tun da dai Ba cikin gari bane.. Motar ce ta wurga Hafiz gefen Titi, Bayan ya Fadi, wasu wurare a jikin shi sun karye Amma tashi yayi Kuma Da gudu Dan ya kai Wannan Maganin a yar uwarsa. Mai motan da yaxo abun yabashi Mamaki Dan ya lura yaron akwai karfi, bai zata zai iya tashi ba, Dan irin wurgashi Da mota yayi. Amma sai yaga sabanin Hakan. Rage gidu yayi, ya saita Motanshi yana bin yaron, Kara gudu Hafiz yayi Amma Ina, kafin Nan ya fadi kasa da kunkumin sa ya daina jin shi a jikin shi. Mai motan nan sai yayi sauri ya je Gefen shi Dan ya Dauko shi sai ya lura da Kan Hafiz ya tsage Har jini yana yi. Kawai sai ya daga shi ya bude Mota ta baya ya kwantar dashi. Shima ya nufi Hanya. Dama Hanyar kano ya dosa. A haka Har suka isa kano, Tausayin Hafiz ya dinga ji yana cewa Wannan Wani irin abu ne za'a bar yaro by this tym yaje jeji. Kai Bafulatanan jejin nan sai a Hankali. Shi dai Addu'anfa shi Allah yasa Yaron bazai mutu ba Ta sanadinshi ba. Dan kar yayi azumi Har sittin Wanda Allah yayi Magana akai. Asibiti direct ya kai shi Wanda ya aka Karbeshi a emergency. In takaice Muku Bayani dai Dan kar ya cinye mana lokaci. Hafizu Saboda Taurin Kan da yayi lokacin da aka buge shi Ashe abun Kara worst yayi Wanda ya taba Mai kunkumin shi. Haka dai aka ta Gama Har aka kai shekarunsa biyu yana ciwon Kuma yanaasibiti. Dan Ma ya samu Gata sosai a wajen wannan Alhajin da ya buge shin Mai suna Alh. Ibrahim. Ya nuna mASA so sosai har shima ya saba dashi. Idan ya ce a Ina Yake Ina Hafsan shi da inna Hauwan shi sai a ce Mai idan ya samu Lafiya za'a kaishi gida. A haka Har aka kai shekaru biyun nan.
Alh. Ibrahim Babban Mutum ne sosai Kuma soja ne a birnin kano a lokacin Kano Garin akwai cikowa da komai. Ko dame kazo an fika shine kirarin kano.
Yana son Harkan soja sosai Dan Haka Yake burin 'ya'yanshi suyi soja amma Allah bai bashi Haihuwa ba kwata kwata. Da ya samu Hafizu kimuma sai duk ya saka Mai concern Mai kyau.yana son shi sosai kamar shi ya Haifesa.
Bayan shekarun Hafiz biyu da rabuwa da su inna Hauwa da Hafsat, while su inna hauwa sun dade da komawa Misau Sai aka sallami su Hafiz a asibiti sai suka koma gida. Kafin ma a sallame shi dama Alh. Ibrahim ya kimtsa ma Hafiz Dakin shi, Anyi mishi Hadadden Gado dai dai na zamanin.
24. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU~~
Hafiz duk da bai gama warkewa ba Amma kullum idan Alh. Ibrahim yazo gurin shi sai ya nuna mASA son ya koma gida Amma Alh. Ibrahim sai yace Mai idan ya huta Kuma ya Kara karfin jiki zai kaishi. A haka har ya kai wata biyu a gidan. Hafiz Wanda a lokacin shekarunsa sha hudu a duniya ya lura da yanayin zaman da Alh. Ibrahim yakeyi da Matarsa. Ba Ta taba Haihuwaba, Amma yaji labarin kauye aka bawa Alh. Ibrahim auren Yarinya Mai kimanin shekaru sha hudu. Akayi auren a kauye sai daga Baya ya Dauko amaryarsa. Shine Har ta haifi Yaro Namiji duk a kauye ba tare da sanin uwargidan ba. Yaronma yana da shekara hudu yanxu. Sunan yaron Ahmad amma ana kiran shi da Salim. Tun daga lokacin zaman Lafiya ya Kare a gidan.Kuma Gashi sai Amaryar ta dau ciki, murna a wajen Alh. Ibrahim kamar small Man. Can Kuma Babba ne a cikin sojojin Airforce. Ya ma kusa retire. Har ma yana da burin idan ya gama aikin Airforce ya koma aikin Bank.
A lokacin ne da Alh. Ibrahim ya lura da yawan tunanin gida da Hafiz yakeyi yayi yawa sai yayi deciding ya kaishi gida Amma idan ya dawo sai ya nema Mai skul Kuma ya tambayi iyayenshi su bar mishi su. Amma Da sukaje garin har yau yana nan yanda Yake sai dai canjin da baza'a Rasa ba a garin Luggudi. Hafiz bai manta da Hanyan gida ba. Haka ya ta nunawa Har suka ISO. Ya hango bukkar Alamun ba mutane. Jikin shi ya Fara Rawa Ganin Ba Alamun 'yan Adam kawai sai Alhaji ya janyo shi jiki yace kwantar da hankalinta. Plz son!!! Haka ya kwantarr. Sukayi sallama a kofar gida. Da aka Amsa MASA sai yarinya Ta fito da Dan shigan Fulaninta sai idonshi Yake ta mASA gizo sai yaga kamr hansai ce, duk da yarinyar shekarunta bazai kai 7 ba. Sauri yayi ya janyo ta yana cewa, Hansai na, kina Lafiya? Ina inna? Yarinyar ne ta tunkuda sa da karfi tana ihu wai Dan iska ya taba ta. Ai kuwa duk jama'an rugan nan suka fito daga bukkansu. Kowa yazo harta Goggonta ta fito daga gidan Tana Fada sai yaga kowa ya tsaya Yana kallon Hafizu. Duk sun Gane shi Amma basu tabbatar ba.
Hafizu dai Tambaya yayi Ina inna Hauwa da Hansai? Sai kowa ya kasa Bashi Amsa. Sai kowa ya koma gida. Matar Baba karamine tayi kokarin kiran Hafizu suka shigo gidan ita Kuma Goggon yarinyar yar nan ta biyo su Tana Mai kuka a ido tana cewa Hafizu kadawo Gida, ka dauke mu iyayen ka. Innarka tayi mun abun da Ba Wanda ya mun shi a duniya tun da Ta ban gurin Kwana. Amma Bata Fada Mana inda zataje ba kawai sai muka nemesu muka Rasa a garin nan. Dukkan mu ba muji dadin Rabuwarsa mu ba. Dan Mutuniyar kirki ce. Haka sukayi ta tausan hafizu Har ya daina kuka. Ya tambayi inda Baba karami yaje akace yaje gona. Zuran Takalminshi yayi ya tafi gona. Yana isa da gudu yaje ya rungume Baba karami, baba karami ma Hawaye ya fara. Tuni ya ajiye komansa suka koma gida tare. Hafizu ya bashi labarin abunda ya Faru dashi, ana n shima Labari ya tsaya Dan bashi da idea. Ya Fada MASA cewa shima baya nan suka Tafi.
A rugar Luggudi ranar Hafizu ya kwana Alh. Ibrahim Kuma ya shiga Garin Misau Bayan ya sanar dasu zai Dawo Gobe.
Washegari kuwa Alh. Ibrahim ya roki a bar mASA Hafiz zai saka shi a makaranta. Bayan yayi musu Alkawarin zai Ina zuwa gurinsu idan yayi hutu ko zaiji labarin Inna Hauwa da Hansai. Da kuka suka Bar Garin kowa yana tausaya mASA.
Bayan sun dawo kano, Aka sa Hafiz a Makaranta a SS2 shekarunshi sha shida ya Gama secondary. Kuma da Yake Makartun da Hausa suke koyarwa bai bashi wahala ba, Kuma ma an Sama mishi Mai koya mishi a gida. A cikin shekaru biyun Dama amaryan Alh. Ibrahim ta haifi 'ya mace Mai suna Ruqayya, Bayan wata daya da Haihuwan ta auren su ya Mutu sanadiyyar Sharrin da uwargidan ta kulla Mata. Da ta tashi tafiya sai ta tafi da 'yar da take shayarwa Kauyen Misau, Itama ta auri Wani mutum Alh. Muhammad Mustapha Wanda yayi Mata Alkawarin rike 'yarta tsakanin shi da Allah. Haka Yarinyar ta Girma da sunan da Ba na asalin Mahaifinta ba. Shi Kuma Ahmad Salim Yana Makaranta A kano tare da Mahaifin sa.
Hafiz Kuma aka Sama MASA admission a kaduna a NDA Dan shi yace bazai yi sojan Sama ba kamar Na Alh. Ibrahim. A lokacin da suke Makarantar ne da shekaru biyu aka tura su kowa ya zabi inda Yake so yayi Bincike akai sai ya zabi wudil Local Govt area. Dan yasan abubuwa Na Faruwa da Mutane a wajen. Yana Zaune a bakin kogi Mai zurfi ne yana tunani kawai sai ya lura da alamar mutum acikin ruwan ko kifi, sai ya tura abun kama kifi shi ciki sai yayi sauri dai dai yanda zai lalubi kifin Amma sai yaji abun yayi nauyi, tsoro ya hanashi sbd kar dai Babban kifi ya kamo, sai ya Fara kiran taimako, azo a taya shi Jan Babban kifin nan kowa yana da kaso a ciki, Kan kace kwano mutanen gurin duk sunzo. Su na janyowa duk sai suka Ga Mutum. Abun Dukaya Basu Haushi, wasu suka fara komawa inda sukafito wasu Kuma suna cewa idan bai basu kasonsu ba sai sun mishi duka. Mike wa yayi ya kira 'yan uwanshi Wanda suke project din nasu Tare. Lura sukayi da alamu soja a hannunshi wato Karamin bindiga duk sai suka koma da gudu.
Juyawa yayi gurin bawan Allahn nan da ya ciro a cikin ruwa Wanda ya lura da dukan da akayi mishi. Tausayinta ya kamashi. Ya mammatsa cikin shi duk ruwan dake cikin shi ya fito. Lokacin 'yan aikin suka iso. Suka taimakeshi ya daga bawan Allahn nan. Asibiti suka tafi dashi Wanda a can ma sunga Matsalolin da ke damun gurin sosai Dan Harda tashin security.
Bayan sun Gama project din su da zasu koma, lokacin Hafi yana kula da bawan Allahn nan sosai Dan ya samu Matsala sosai. Ko magana Baya yi. Sai da akayi transfer dinsa zuwa kano, Hafiz shi yayi MASA komai. Abokanan tafiyansa har sun koma skul, Hada kai suka yi Dan su saka a kori Hafiz basa son yayi graduating sai sukayi karya a Commandernsu Ai kuwa har yaji haushi, Amma and yana ji da Hafiz saibl bai Yanke hukuncinci ba sai da yaji daga Bakin sa Wanda a dalilin Wanda ya taimaka duk da yasan risk ne lokacin skul ne shine aka yafe MASA Kuma yasamu Babban Matsayi, shi yasa tun daga lokacin ya dau Alkawarin Taimakon Mutane Har karshen Rayuwar sa. Bayan Dan watanni Dama ya mayarda Wanda ya tsinta Gidan Alh. Ibrahim, ya roke shi Kuma dama kun San Alh. Ibrahim da taimako. A haka suka zauna dashi har Hafiz ya gama training dinsa ya zama cikakken soja. Aka bashi Babban Matsayi, a haka yayi Rayuwarsa. Bayan ya kai Wannan bawan Allahn da ya tsinta a ruwa an cire mASA ruwan da ya shiga dodon kunnensa, ya fara ji ya fara Magana anan ne Yake sanar da Hafiz sunan shi Ahmad Kuma shi Dan garin Misau ne iyahen shi sun Mutu sun bar musu dukiya Mai tarin yawa shida Dan uwana kabir......, Ana ya gama bashi Labarin Rayuwarsa Kuma yayi MASA godiya akan Alkhairin da yayi MASA shi Kuma Hafiz Wanda yasan cewa Ahmad ya girmeshi nesa ba kusa ba, ya girmama shi Kuma ya fada mishi Ai shima Dan Misau be a rugar Luggudi..... Shima duk ya bashi Labari. Sai yace Mai idan sun koma Gida zasu Tambayi Alh. Ibrahim ya bar su suje Misau. Hakan kuwa akayi. Bayan wata biyu Da Aikin da akayi wa Ahmad sukaje Misau Tare inda Shima Alh.Ibrahim yaje anso 'yarsa Amma sai ya tarda Matarshi Tayi aure Kuma tare da 'yarsa Ruqayya ta tafi. Dama yayi Rashin Amaryar sa dan ya gano duk kullin da uwargidan sa tayi mASA ya saki Amaryarsa.
Shi Kuma Ahmad inda ya Fara zuwa da suka isa Misau shine gidan Sarkin Malamai, Dan yana son ji ko tazo ko say daya ne. Da sukaje ya Hadu da su Hajiya iya, Gaisuwa sukayi ya fara basu labarin abun da ya Faru dashi da kaninsa. Duka gidan sai da sukayi kuka, Dan kowa yayi Mamakin Rashin zuwansu. Suka Tausaya mASA. Ya sanar dasu cewa zai ta Neman su, Kuma har hukuma zai Fada wa, Kuma a taya su da Addu'anfa. Hafiz dai tun da suka shigo Yake ta kallon Hoton da ke Manne a jikin Bangon Dakin. Duk basu lura Dashi ba a falon, kowa na kimanin Batan da Hafsat tayi da rabuwa da tayi da Mijinta.
Dauko Hoton yayi, inna Hauwa ne da Hafsat, Hawaye yakeyi ya fara Tambaya, Ina ku Kasan Innata? Da Hafsatu na. Dan Allah ku Fada mun Dan Allah. Kowa juyowa yayi yana kallonsa. Harta Ahmad Mijin Hafsat sai da yayi Mamakin wannan ikin Allahn. Da Kyar aka kwantar mASA Da hankali. A takaice dai in Fada Muku, duk an bayyana MASA abun da ya Faru. Mutuwar tsaye yayi da yaji labrin. Amma dai Ahmad Mijin Hafsat ma sai Hakamuri Yake bashi. Dukkansu sukayi Alkawarin Neman su Har inda karfin su ya kare.
Lokacin shekaran Hafiz sha tara Kuma sojane Amma corparal. Shima Ahmad da dama sun gama exam na level 400 da komai abun ya same shi. B. U. K yaje ya karbo certificate dinshi, since zasuyi posting dinshi bautar kasa Amma yace Musu NDA Zaije yayi short service idan ya dawo sai ayi posting dinsa bautar kasa, hakan kuwa akayi, ya yi applying, Alhmdlh Kuma ya samu ya yi shekaran shi daya ya zama soja.
Bayan shekaru bakwai Alh. Ibrahim ya umurci su Hafiz da Ahmad da suyi aure Amma Ahmad yace Bazai yi aure va Dan zau jira Hafsat, shi Kuma Hafiz yace Matar da zai aura tayi karama Dan yanxu shekarunta ta basu fi sha biyu ba, Dan Ma tana da girman jiki. Amma duk da Haka ba'a karbi nashi uzurin ba Alh. Ibrahim ya ce Ai ta kai aure zai nema mASA Aurenta, Ai kuwa da aka Tambayeshi Wanda Yake so sai yace Yana dai ganin Yarinyar Idan yaje Misau a gidan Hajiya iya Amma bai San 'yar gidan wacece ba. Da sukaje sai aka Tambaya akanta suka ce auren ta suka zo nema. Sai suka ce dole a nemi Mahaifinta Dan ita Agola ce, ita ba 'yar Mai gidan bane, Gashi Mahaifin nata ma da ya rike ta Allah ya Amshi abun sa. Ya rasu. Yanxu Kuma bata dade da gane cewa shi ba Mahaifin ta bane. Gadon da Maman ta ta samu ne kawai ya taimakesu suka samu gurin zama tun da dai bata Taba Haihuwa ba. Aka yi masu Hafiz da Alh. Ibrahim kwatancen gidan ai Sunji tausayinta sosai lokacin da aka basu labarinta. Suka bi kwatance suka isa gidan da sallama ai kuwa Yarinya ce Amma Mai girman jiki ta fito Da hijabin ta suka Gaisa, sai duk ta birgesu, Dama ta gane Hafiz Dan idan ya Ganta yana kulata a gidan Sarkin Malamai. suka tambayeta ko Mahaifiyarta tana nan, ta Amsa musu sannan Ta shiga ta fito tace musu zasu iya shiga, Da sallama suka shiga gidan. Ummanta ta fito daga cikin Daki da hijabinta Tana sunkuyar da kai, tace bata gane su waye ba, can dai Alh. Ibrahim kallonta kawai Yake, ya kira sunanta ta daga kai taba Hada ido dashi Hawaye suka zubo Mata ta tashi tace ku fita mun daga gida Kar In Muku ihu Bana son Kara ganin ka a rayuwarta ta ko kazo ka kwace yarinyar da ka bar mun ne? Bayan ka kwace mun Dayan Farin cikina Ahmad? Kuka takeyi sosai, Da Yake ba Masifa ta iya ba kawai sai ta zauna. Hada ta da Allah sukayi duka sannan ta saurare su. Suka bata Hakuri duka suka bata Labarin irin Neman ta da sukayi Amma basu same ta ba Har akace tayi aure...... Bayan sun Gama bada Labarin Sai suka ce yanxu ma da ta gansu ma auren 'yar ta suka zo nema, sai suka Ganta. Duk ta yafe musu. Sai da Alh. Ibrahim ya sanar da ita Ai sunfi shekara biyar rabonsu da uwargidansa, yanxu Haka Ahmad salim ya kusa gama secondary Dan yana ss2 Kuma shi kadai yake tare da Alh. Ibrahim Dan yanxu Haka ma yayi retire yana aiki a C.B.N Abuja. Da Kyar a wajen ta yarda da tambayan Aurenta da yace zai yi. Dama Tana son shi. Ta yarda.
Alh. Ibrahim Kuma yace ya bayar da 'yar sa Halal a Hafiz.
Murna a wajen Hafiz, sai kallon Rukayya yakeyi wacce take ta sunkuyar da kai tana murnar Ganin Mahaifinta. Kuma tana son Ganin Yayanta Salim. Wata Daya akasaka biki akayi auren Uwa da diyarta duk a shekara guda. Suka Tare a Abuja Bayan shekara daya kuwa aka samu karuwa. 'Ya mace kyakkyawa. Aka saka mata suna Amatullah. Bayan Haihuwan ta ne yayanta salim ya dawo, ya gama kr2 shi a outside, yana ganin bakin Face a idonsa ya Fara huci, wai shi popsynsa ya cika kwashe kwashe, bai san mutane ba Amma sai Tattaro outsiders, fuskan Mahaifiyarsa wanda baya Mantawa ya Gani wanda shi ya dawo Masa daga tunanin da yakeyi yaje gurinta da gudu yayi hugging dinta, yana Mum y do u live me alone? Are u back for me?. Yayi murnar ganinta sosai. Sannan aka nuna Masa sistern sa Rukayya Wanda taki canxa sunan Mahaifinta, tana gani kamar idan ta canxa butulci tayi, Kuma tana alfahari da sunan ta. Yayi murna sosai da ganinta, Amma dai kun San rashin sabo, Bazasu zama daya ba sai nan gaba.
Bayan watanni akayi admitting dinshi a NDA Dan yace shima Army zai yi ba Navy ba Kuma ba Airforce ba. Haka ya fara Har Allah ya sa ya Gama. A ranar da Yake dawowa yayi accident. Wanda Kuma yace Baya son Fada Ma popsyn sa Dan Fada zai mishi.
Haka rayuwa tayi dasu kullum suna bincike akan Neman Hafsat Wanda sai yanxu aka gane cewa wannan Batular da tazo Gidan tayi shekaru biyu Ashe 'yar Hafsat ce. A nan kawai Tunanin Da general keyi Ya Dawo Hayyacinshi. Ana Ta Bashi Hakuri. Sergent Ahmad Ma ya kwantar da Hankalin shi. Ya roki General cewa ya nemo mishi Batula, Dan itace Kadai Last hope dinshi na Neman Hafsat dinshi.
Yanxu Misalin karfe 3:00 na dare ne Amma Haka General ya Bar asibiti, ya tafi gurin 'yan sanda ya sanar dasu irin kalar yarinyar da ta Bata da kayan jikinta da komai da za'a yi identifying din ta.

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now