PART 10

3K 90 1
                                    

14. MAKABARTARMU ~~KHADIJA AMINU.
Sun shigo Abuja, kunsan motan sojoji ba'a taresu, ko holdup ma idan ana ciki matsa musu akeyi. Batula kam kalle kalle takeyi, a zuciyarta tana cewa anya kuwa a duniya nake, wannan guraren sun hadu. Kallo kawai take bin gurin da. Ta rasa inda zata saka kanta dan Farin ciki. Tana ta addu'an Allah ya kawo Mata Mafita.
****sun shigo cikin headquarters Nigerian Army, wuse 2,abuja da misalin karfe biyu. Fitowa drivers din sukayi dan sun sauka ne a gurin parking space din sai suka je bayan motan dan su dauki bindigan su kawai sai suka ga abu na motsi a cikin leda, ledan kamar ledan katifa yake. Daya daga cikin sojojin ya janyo ledan ai kuwa sai ya ga 'yar karamar yarinya tana kwance amma ta bazo musu ido kamar marar gaskiya. "laalaalaa, kaga wata yarinya a cikin mota". Mamaki ne ya debe su duka suka kalli juna sai dayan yace "wannan itace yarinyar da mutumin nan ya ke nema da daddare. Ashe tana bayan mktan mu bamu ma sa ni ba. Ikon Allah". Dayan yace " bari in kira mutumin kawai ince mishi ganan 'yarsa nan."
"Maza Sakko , meyasa kika shigo motannan kuma kinaji ana neman ki baki fito ba?" Amma mu da zamu je wajen general yaya zamuyi da yarinyar nan?  Gaba daya Hankalinsu ya tashi.
Ana cikin haka ne sai General ya fito daga Office tare da abokin shi. Su na sallama sai suka ga yarinya ta tsuguna a gaban su tana rokonsu "dan Allah kar ku kirashi, sace ni yayi shine na samu na gudu, Dan Allah kar ka kira shi Dan Allah." Dayan ne yace "Toh idan bamu kirashi ba yaya zamuyi dake, ni ba aure nake dashi ba bare in kaiki gidana gashi ni ba dan kasarnan bane Ma. Ai cewa yayi shi Babankine. Kuma ai naji ma da bakin ki kikayi ihun kiranshi Abba! Zo ka taimaken" dayan ma yace "hakane kam dole ki koma gurinshi". Kuka takeyi kawai.
General ne yazo kusa dasu dan yaji duk abin da suke cewa, a take da suka ganshi sai suka kakkandare su na cewa "moh sir!!". Zuwa yayi ya janyo 'yar karamar yarinyar da take kuka wato Batula, yana rarrashinta yana cewa "kiyi hakuri baby, baza'a mayar dake ba, kinji?" ya dauko hankerchif ya share mata fuska. Ya barsu a kakkandare. Janta yayi suka shiga office sannan ga juya yana kallon sojojin nan yana cewa ku kuma ku jira punishment dinku. Duk ku biyo ni, " yes sir! Sukace sai uka biyo shi.
ya shiga da ita office dinshi yana kallon yarinyar wacce tayi masa kama da wanda ya sa ni a da. Ganin tana ta lumshe ido kawai sai yace kina jin yunwane? Daga kai tayi ta amsa da Eh. Zuwa yayi da kan shi gurin dining table a can office din ya hada mata tea mai kauri ya dauko bread ya bata. Ta karba tana cewa Nagode. Murmushi yayi yanda tayi maganan yaso ya gane wacece amma ya kasa.
***kiransu yayi a waya yace ku shigo, suka shigo suna Kakkandare jiki sai yace ni ba wannan Nace kuyi mun ba, ku da ya kamata ace kun kare hakkin kasa sai na kama ku a cikin masu son Wulakantawa. Yanxu yarinyar nan dubeta baiwar  Allah bata ci ba bata sha ba Amma tana rokon ku kun kasa taimakon ta." sorry sir sukace sai Yace musu fada mun dalilinku na yin hakan. Dayan ne yace "Dama ni tsorata ma nayi da ita dan na ganta kamar Aljana". Rufe mun baki general yace sai dayan yace "dama a bauchi ne muka kwana a gidan mai sai ta shige mana mota. Bamu ma hadu da ita ba sai da muka shigo nan muka lura akwai mutum a cikin motanmu.........." ya bada labarin duk yanda akayi a can din. General ne yace" da zan baku punishment Amma kuje na yafe muku. Kuma ku dinga taimakon mutane, kunji?. Ni kuma zan Taimaki 'yar nan In Allah ya yadda. Anan ya fada musu abun da zasu mishi ya juya gurin Batula ***ummulkhairy****

15. MAKABARTARMU ~~khadija aminu. ~~
Zuwa General yayi wajenta yace "baby, ya sunanki?" Tace sunana Fadimatu amma ana kirana Batula.
Yace daga ina kike? Tace Dan Allah kar ka tambayan daga inda nake dan idan ka tambayen bazaka gane amsan ba. Dan ni daga MAKABARTA nake. daga wajen da ba'a fita nake, muna can kulle.
"MAKABARTA kuma? Abun da ya fada kenan". Yace baby kinsan garinku? Su waye iyayenki? Shekarunki nawa da zaki baro gida? Kuma meya kaiki har kika shiga mota kika taho da sojoji cikin dare? Meya hada ki da mutumin da yake neman ki?. Duk a take ya jero mata tambayoyin nan. Ta rasa amsar da zata bashi kawai sai ta fashe da kuka. Daga fuska yayi sai ya gane irin kukan da takeyi Mai hade da zuciya ne wanda zai iya illa a dan shekaru kamar shekarunta....
Ji yayi kamar tana taba mai zuciyane a lokacin da take kukan zuciyan nan.
Ganin hawaye a idon ta yasa yace bari in gama in kaiki gidana.
Kiran secretary dinshi yayi, yayi mishi order ya rike hannun Batula suka fita daga office din. Ya danna abin budewa tun daga nesa, motarshi mai suna Camry, baka ce mai sheki. Ya bude sit din mai zaman banxa ya saka batula ta shiga cikin motan, shima ya rufe yayi nashi gurin.
Yana tafiya yana kallon Batula, zuciyarshi na kirgo masa abubuwa da dama.
General mutum ne wanda ya taka Matsayi daban daban saboda Rikon Gaskiya da Amana ya wuce matsayi tundaga abin da yayi corporal, specialist, sergernt,Sergeant Major, Command Sergeant Major,Sergeant Major of the Army, Chief Warrant Office, Chief Warrant Officer, Second Lieutenant,FirstLieutenant,Captain,Major,Brigadier General,Major General, Lieutenant General, yanxu kuma haka yana Major, matsayi daya ne ta rage ya hau Major of the Army. Kuma dududu Shekarunsa 29 zuwa 30. Yana da kirki sosai kuma yana aikin sa tsakani da Allah. Shiyasa ma duk wadannan ci gaban a cikin shekaru sha biyar ya samu. Mutane suna respecting dinsa sosai.
****General ne ya gama parking. Ya fito daga mota sai ya bude ma Batula kofa. Wani soja ne yazo yana kakkandare mai, zai karbi jakansa sai yace masa a'a ya barshi kawai.
Shiga yayi gidan hannunsa rike da Batula, sai janta yakeyi ita kuwa tsoro ma har ya kamata Dan bata saba ganin Mutane ba. Shiga sukayi da sallama wata yarinya karama tana gefen wata mata daga gani Mamanta ne, tashi tayi tana cewa Daddy oyoyo, Daddy oyoyo. Daga ta yayi, ya sake hannun Batula, wacce hakan sai ya burge Batula, taji inama itace. Matar dake Zaune a kujera tana ta zumbure zumbure Baki wai ita a dole taji haushi ba'a zo an mata oyoyo ba kamar yanda akayi wa Babyn nan. Sauke Babyn general yayi yana cewa. Yau ba oyoyo ne?, tuttura Baki takeyi tana kunkuni, sai da yayi mata oyoyo, sannan ta lura da wata yarinya ya shigo, sai ta daina salon da takeyi ta maida hankalinta ga Batula.
Cewa tayi Daddy waye wannan yarinyar?, sai yace Mata daughter tace. Kema Daughter ki ce daga yau ke momynta ce. Ki dauketa kamar yanda kika dauki  yar da kika Haifa Dan Allah. Nasan ki Rukayya Muhammad Mustapha(sunan da idan aka kirata dashi Yake burgeta sosai) ta. Nasan ki Mai Hakuri da iya kula da Mutane, Nasan ki da Sona da kaunar abun da nake kauna. Plz ki kula da yarinyar nan.
Babyn general ne tazo tana tafiya tana gwalaben magana a Batula wai ita tana da daki pink, komai pink, Kuma momynta Nada daki Mai kyau, haka daddynta ma. Ke Wani daki zaki zauna. Ki zauna a daki na Ina sonki sosai. Mamana tana mun waka wai "tun tun Ina sonki fa, tuntun Ina sonki fa, sonki sonki sosai". Batula dai ta tsura wa yarinyar ido, yarinyar tana kama da ita sosai, har da amminta ma yarinyar tana kama.
Momy ne ta janyo su duka, tace Amatullah kin iya surutu. Adda ne sunanta daga yau kinji? Momy tace wa Batula suje daki ta nuna Mata komai. Hakan kuwa akayi. Momy ma yanayin Batula yayi mata Dan tana son mutum Mai nutsuwa, duk da abubuwa dayawa na yawo akanta akan Batula. Dan ita ko zata rantse, zata rantse cewa sun hada jini da General. A ranar Batula kwana tayi tana sallah duk da karancin shekarunta. Tana gode wa Allah. ****ummulkhair****

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang