Part 5

3.2K 111 5
                                    

7. MAKABARTARMU
Salati kawai yakeyi yana sanar da ubangiji, ya ma rasa yanda zai yi kawai sai ya zauna a wajen yayi su.an zaune.
Kabir ne ya fita daga gidan ya dauko wata tsohuwa, yayi mata karyan cewa Matarshi ce tayi bari ta taimaka mishi, ya dauko kudi dubu biyu ya mika mata. Dama neman kudi takeyi, ai kuwa ta bishi har da tambayansa ko ya saya Pad Na mata, sai ya tambayeta inda ake sayar wa ai kuwa sukaje chemist suka saya, ya biya ta wani shago ya debo mata doguwar riga baka da turare. Sai ya sayo abinci. Sannan suka je gida. Hafsat kam in banda kuka ba'a bin da takeyi. Ta shiga toilet anan ta fadi ta suma dan tasha wahala ba kadan ba.
Tsohuwarce tayi wa Hafsat wanka ta tas, har ta saka mata kayan duk bata san inda hankalin ta yake ba, ta saka mata chunko. Tsohuwa kam abun ma Mamaki yake bata dan kuwa bata ga wani alaman Bari ba, dan bata ga gudan jini ba. Bayan ta gama sai tayi mai sallama tace mai idan ta tashi a bata abinci taci, tsohuwa da bata jiran bakin ta sai tace Anya kuwa cikin ta ya zube kuwa? Sai yace mata Ba damuwarki bace, sai taja bakin ta tayi shiru. Daukan ta yayi ya kaita gida sannan ya dawo.
Shigowan da yayi sai yaji Alamar mutum a gidan, yana bi inda yaji kamar tafiya sai yaga Hafsat ce ta tashi , sai yace My One kin tashi? Ihu tayi mai tace ka mayar dani gida nace, sai yacd mata ai nan ma gida ne kuma gidan da zaki zauna kamar Makabarta, bake ba fita ni kadai ne naki. Hhahahaaj!!!! Sai tace kabir baka da hankaline, nifa Matar aurene,. Bushewa yayi da dariya sai ya zagaye ta sai ya kama hannunta ta baya, ya jata har zuwa daki, sannan ya daure hannun yace my luv Nasan kina jin yunwa, asali ma baki da lafiya kuma kinga kamata yayi ace kin ci abinci, kinga bana son in rasa ki, plz kici abinci. Dama kuma yhnwan takeji karfin hali ma tayi tayi masa ihun. Sai ta ce toh ina abincin. Miko mata kwano yayi ya fara bata a baki. A haka dai ta daure ta ci abinci. Bayan ta gama sai ya bata ruwa sai kuwa gashi ana kiran wayan sa. Sai ya dauka, yaya Ahmad ne ya ce Dan Allah kabir ka daiba tsokanata, kasan kuwa Matata baxan iya rayuwa ba ita ba ko? Plz stop. Ka fito mun da matata. Dariya yayi mai isarshi sai yace kana son kaji muryan Matan ka na Karshe? Toh bari in baka ku gaisa, a kunne ya sakamata, sai ta fara cewa plz kazo ka daukeni, Kabir ya kashe danka, kuma yana son kashe ka. Idan baza ka iya zuwa dauka na ba ni zan kashe kaina. Dan Allah!!! A muryan kuka take fada, nan da nan zuciyar sa ta fara bugawa sai yace Bazaki Mutu ba In Allah ya yadda. Dan Allah ki kula da kanki kiyi ta Addu'a a duk halin da kika tsinci kanki. In Allah ya yadda bazaki wulakanta ba, kinji? Daga kai tayi kamar tana gaban sa Kishi ya kama kabir sai ya wapce wayan sa sai yace kamar yanda na ce maka wannan shine Ranar karshen ka najin Muryar ta, nima hakane, dan wannan shine Ranar karshe Na jin Muryata, sai anjima, nan ya kashe wayansa ya fara dan Hawaye. Hafsat ce ta ce Meye amfanin hawayen Naka bayan ka biye wa son zuciyarka? Ai baka da imani, baka ma san inda imani yake ba. Tsawa yayi mata Mai gigitarwa yana cewa" kiyi mini shiru, nima fa ina son dan uwana, amma sonki ne yasa dole in hakura dashi. Kasheshi zanyi Hafsat." Hawaye ya fara ita kuwa tace ba haka ake so ba, idan kana son mutum zaka iya sacrificing all ur happiness ka bashi bawai duk happiness dinshi ka kwace ba.
Tashi yayi ya fita ya kulle gidan da hannunsa dan kar ta fita, duk hanyar da yasan zata iya bi sai da ya kulle, sannan yayi ma Mai gadi Kashedin kar ya bari kowa ya fita.
**** misalin karfe sha biyu na dare kenan yanxu. kiran ahmad yayi a waya yace kazo wudil yau da karfe hudu zan baka Matarka, ka sameni gurin babban tekun garin. Kuma kazo da duka takardun dukiyan da iyayenmu suka bar mana idan ba haka ba kuma Bazan baka ita ba.
A lokacin ya kira wayan wani dan sholishon ana kiran shi da dan tijara, sai yace musu su sameshi a gurin round about din fita daga gari, hakan kuwa akayi yana isa wajen ya dauke su. Kowannensu yana dauke da bindiga, abin shaye shaye da wukake.
Da misalin karfe hudu na uku na dare suna bobboye a jikin duwatsu suna leken ko Ahmad zai iso Amma shiru har karfe hudu ma shiru, sai da biyar Nan Ma shiru sai kabir ya fara jin haushi yana cewa Ai tunda ya bata musu lokaci sai sun bishi har cikin gida sun kasheshi. Su Dan tijara sai huci sukeyi suna hura taba wai su a dole sunji haushin rashin samun Nama, duk sun fara nufan titi inda suka ajiye motan sai sukaji ana kwala ma hafsat da kabir kira. Sai suka koma inda suke. Abokin Dan tijara ne wanda ya iya muryan mata ya fara cewa, kar kazo nan zasu kashe ka idan baka kawo musu takardun ka ba, wayyo mijina kar kazi nan. Magana ya sakeyi Nazo dashi Hafsat kawai dan in ceci Rayuwarki, zan hakura d komai na duniyarnan idan dai kina tare dani, jabir ina matata? Ganan takardun. Zagayeshi sukayi suna tafi, Miko takardun inji Kabir, dan tijara kuma ya rufe mai ido, Dan Shege kuma sai dukan cikin sa yakeyi, suka daga shi cak sai kabir ya nuna musu inda zasu jefa shi Ai kuwa Ba inda suka jefa shi sai cikin ruwan nan wanda idan Motama ta fadi ba'a jin labarinta ballantana Mutum shi daya. An ce ma ruwan nan idan Mutane suka fada marmie water cinyeshi takeyi.
Dariya suka bushe sai suka ce kabir congrat, har ya fara hawaye sai suka fara bushar mai da zuciya sai suka ce yanxu nawane kasonmu? Sai yace sai mun hadu next. Haka suka kama hanya sukayi birnin kano bai tsaya a ko ina ba sai gidan da yakai HAFSAT. Dama ba gidansa bane, haya yayi na rabin shekara dan dama ya gama plan din yanda zaiyi.
Yana shiga gidan sai ya duba dakin da ya kulle ta Amma bai ganta ba, ya duba ko ina a gidan amma bai ganta ba sai ya tafi gurin mai gadi sai yace masa akwai wanda ya fita sai yace A'a ba wansa ya fita dan yanda ya tafi bai maji motsin kowa ba. Ya kara komawa a karo na biyu, still bai sameta ba, hankalin shi yayi matukar tashi dan idan bai sameta ba bai san inda zai sa rayuwarsa ba dan yana gani kamar Hafsat ce kadai Rayuwarshi.... .**** taku Ummulkhairy Aminu***Nagode Masu bina kuyi Hakuri bana muku typing dayawa. Tnx alot masu comment.

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now