PART 19

5.2K 202 59
                                    

32. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU
General da Batula da Sergernt ne a mota suna Hira akan Labarin Su a gidan da suka Tashi kamar Makabarta.  Ya Tausaya musu sosai. Sun isa Garin Bauchi Da wajajen Karfe sha Daya Na safe. Suna isa Batula Ta Fada Musu sunan unguwar Dan Bata Manta ba Gida Dubu ne sai dai Layin gidan ne zai Bata Matsala. Duk da Haka Bata Cire rai ba suka isa suna Ta Neman gidan Amma basu Gane ba. Sai da suka Dawo sai suka Ga gida duk da ya canxa sosai sai dai Da bishiyan Mangoro Wanda dama Batula tasan cewa gidansu akwai wannan Bishiyar. Da sauri tace zata shiga ta duba. Tana kwankwasa wa sai Mai Gadi ya bude Sai ta zo shiga Mutumin yace shi tun da Yake bai taba Ganin Bako ba a gidan Dan Haka Bazai barta ta shiga ba. Tayi Tayi Ya barta ihu Ta Fara tana Ammi Ki Fito Ammi!!! Batula ce Ammi!!!!.Hafsat Wanda take zurfin tunanin inda yau da sassafe Kabir ya dauki su Hassan suka Fita Ba tare da yamata Sallaman Inda zasu Ba. Da ma Ban Fada Muku Mutuwar Hafiz Kabir a wancan shekaran Ba.
Firgita tayi da jin sunan da ake kiranta dashi Ta Dauko Dan kwalinta ta nufi waje. Tana isa Da sauri tace Batula sai ta isa wajen ta ta rungumeta su General Ma da Sergernt suka sakko daga Mota, Dama da kayan yaki suka zo Dan sun so kama Kabir ne idan ya Hanasu Hafsat. Bata Gama jin dumin 'yarta ba ta daga ido zata juya sai su General da Sergernt sukazo shiga Gate Dan binsu cikin Gida Amma Da Mai Gadi ya Gansu tsoro ya sa ya ki Hanasu wucewa ciki.
Idon Hafsat karaf a idon Sergernt Ahmad Ta kasa daga idonta a kansa shima Haka, Hawayen kauna kawai sukeyi Tace Ahmad!!! Yace Hafsat!!!! M I dreaming or its true?
General ne ya tsoma Bakin shi yace "My Twin Its Real,"
Daga ido tayi Mamaki biyu ta Farayi ganin Fuskan da Bazata taba Mantawa bawato fuskan Hafizu da sauri taje tana shafashi ko da Gaskene. Ta rungume shi Tana kuka Sosai yana ce mata "dnt cry my twin sis, bazamu taba Barinki Ba we will always b 2 geda. Dan Allah kiyi shiru. Idan kina kuka zaki samu yin kukan zo muyi Hiran yaushe Gamo.
Hafsat ne tace "Dan Allah ku gudu dani daga gidan nan bazan iya zama ba, duk da ban San Rayuwa a cikin kabari ba Amma Ina jin Labarin cewa Ba Wanda ya shiga baya Fita. ynda kuka ga Makabarta haka nake zama".
General yace" bazamu gudu ba we must Face Kabir."
Hafsat tace ka tambayi Batula yanda Kabir yake ya wuce yanda kake tsammani zai iya cutardamu gaba Daya. Yanxu dai kawai mugudu Ni na yafe Mai tunda mijina Bai Mutu Ba kamar yanda kabir yace, Kuma Batula Ta Dawo. Alhmdlh"
**** mai Gadi ya shigo gidan yana huci yana cewa Hajiya Polisawa ne ke waje suna son Tafiya da Matar gidan Nan wai Mai gidan yayi Hatsari. Da sauri Ta tashi zata bisu sai su general Ma tare Da  Batula suka bi Bayanta suka shiga Mota suna bin motan policawan zuwa asibitin. Ita kam Hafsat Ba kabir din take tunani ba 'yan biyunta take tunani, Hassan da husaina.
**** Hafsat ce Take kuka A gefen gadon Asibiti inda kabir yana kwance a Kan Gadon asibitin Kafanshi daya a guntule Dayan Kuma An daure da Karfe a ciki. Hannunshi daya a Yanke Dayan Kuma da Lafiya, Habanshi ya tsage inda kana ganin wasu Namomi a Fili. Tunda Hafsat ta shigo wajen Tare da Police din da suka Fito da ita daga gidan ta Wanda tun shekara uku da Rabuwarta Da Batula Bata Taba Fita Ba Sai yau. Bata kalli Fuskan Kabir ba sai Yanxu Wanda tana Ganin Fuskansa Ta Razana Sosai da karfi take tambayanta "Ina ka kaimun yarana Kabir? Bazan yafe Maka ba idan Baka Fada Mun ba". Bai iya ko Magana ba yana dai jin sa Hawaye na zuba a idon sa.
Irin ihun da tayi a asibiti yasa polisawan shigo zasu fitar da ita daga dakin. Batula ta rike Hannunta tana Hawaye sai Tace "Ammi, Ammi, zo Muje kiga abin da ya Faru dasu"
Tare suka isa gurin da aka lullebe su da zani.
Hassan da husaina a kalla yanxu shekarunsu Tara a duniya Allah ya Dauki Abunsa Badan Baya sonsu ba. Allah ya jikansu.
***** sergernt Ahmad ne ya shiga Dakin da aka kwantar da kabir, da sauri yaje gefen shi yana kallon shi yana Hawaye "meyasa? Meyasa? Kawai Yake Furtawa a kabir.
Kabir ya daga Jajayen idon shi sai yayi yunkurin sauka daga kan gadon sai yaga ya kasa. Da karfi ya fashe da kuka. Sai sergernt Ahmad yace, " ban so ace Haka ya Faru da Kai ba kabir". Da karfi kabir yace " Amma Yaya kana da zuciya Mai kyau, Mai duniya zatayi da Mutum Irina? Wanda yayi Sanadin rushewar Rayuwar Dan uwansa sannan ya Rabashi da Matarsa sannan ya Fifita son zuciyarsa akan son Danuwan sa. Ashe kana raye Yayana Baka Mutu Ba? Ban taba tsammanin zaka iya Rayuwa Ba. Nagode wa Allah da ya Bayyana ka a lokaci dai dai da Mutuwar Rayuwata. Nasan kana son Hafsat ko ba dade ko ba juma. Nasan za ka kula da ita sosai dama Ita Matarka ce Tunda kana Raye. Nasan cewa Ban kyauta Ba Yayana Amma Ina Neman Gafaraaaaaa...... Tari Kabir ya fara sai Ahmad yace "ni ba Haka nake nufi ba, Naso kana da Lafiyan ka zamu shiga kotu sabida abin da kayi mun Nayi niyyar sai an hukunta ka dai dai da zaluncin da kamun."
Fado wa kasa kabir yayi yana shure shure Sergent Ahmad yayu saurin Fita daga dakin ya fita waje yana kuka.
Hafsat ma kuka takeyi akan Gawan 'ya'yanta, Batula tana Shafa kanta, general Kuma ya na Tafiya yana Tunani, Saboda bai Ga Sergent ba a gurin Hafsat sai ya koma Room din da aka kwantar da kabir Ai kuwa sai ya Taddashi a kofar dakin yana kuka yana buga kanshi da Bango. Da sauri yaje ya rike shi yana cewa "Haba senior, meyasa zakayi Haka, Nasan abunda kabir yayi bai kyauta Ba Amma bai Kamata ace Kaima ka nuna Mai kamar kai karamin Yaro bane, ka girmeshi fa sosai, u Have show him dat u re better Dan him. U have to show him that u re not ignorant, I knw dat u can Forgive him, bcoz the one who Forgive first is the most strongest one, u have to forgive him, u re blood brothers dont forget please, u re the only one he have in his life, if u ignore him nw and he died like this, u will not forgive ur self, stop crying senior please". General Hafiz ya cigaba da buga Mai baya yana bashi Hakuri, shima dai Hawayen yakeyi.
Ihu sukaji da ga cikin Dakin sukayi sauri suka shiga. Kamar Mai Farfadiya suka tarda Kabir, da sauri General yaje ya kira doctors suka shigo aka daga shi zuwa Kan Gado akayi mishi Emergency treatment.
Kafin a Gama general yaje akayi wa su Hassan da Husaina wankan Gawa aka kaisu, Hafsat da Batula dai kuka kawai sukeyi, suna kofar dakin da aka kwantar da kabir, Ahmad Na kallon ta. A zuciyarshi yace Yanxu Meye Hukuncin Aurenmu da Hafsat? Anya kuwa zamu iya karasa Rayuwarmu Bayan irin zaman da ya shiga tsakaninsu da kabir? Wani hukunci ne ya hau kanmu?
Da tunanin nan da Ahmad yakeyi ni Kuma Na gaji da typing. ****ummulkhair****
33. MAKABARTARMU ~KHADIJA AMINU~~~
wata nurse CE ta fito daga room din da kabir ke kwance sannan tace, patient din yace yana so yayi magana da Ahmad, da Hafsat.
Tare suka shiga cikin dakin harda General Hafiz.
Kallon kallo sukayi wa junan su sannan sai kabir ya bude baki yace Ahmad tun da kaki ka yafe mun yanxu zan fada Maka abun da baka Sani ba. Nine sanadiyyar mutuwar iyayenka. Kuma ni na yarda da cewa Nine. Ahmad ne ya kalle shi yace yanxu Dan iyayenmu sun mutu kake cewa iyayena? Ni kadai suka Haifa? Ai tare suka Haifa Mu.
Kabir yace "ka tsaya kaji riban labari, ranar da iyayenka zasuyi tafiya, INA wasa da wani keke ta bayan Tagar dakinsu, kawai sai naji Hajiya (mahaihiyar Ahmad) tana magana sama sama. Sai nayi sauri dan naji kome ya hada su da Baban namu kawai sai naji tana cewa wai ita zuciyanta yana bata cewa Ni kabir kyan Dan Maciji ne dani, Dan ita tun da aka same ni bata taba sona ba, wai ita kan ta gaji da irin wannan rikon Dan da ba ita ta Haifa ba. Sai naji Baban namu yana cewa Dan bamu muka haife shi ba sai Mu tsane shi? Mu koreshi kike son muyi a gidan nan ko kuwa?
Meyasabazaki dauki Kaddara Bane ? Meyasa bazaki dauke shi hannu bibbiyu ba?. Ni dai saga yau bana son in karajin wannan mitan, Dan Fisabilillah.
Ina jin Haka Ahmad nasan cewa Ni Dan tsuntuwa ne a lokacin raina ya baci Nayi sauri nabar wajen ba tare da jin karashen ba. Sai na dauko kusa na coka a jikin tyren nayi ma tyren motar da zasu tafi dashi hanyar Fashe. Sai na je gefe INA kuka. Ko da suka fito kallon su kawai nayi sunyi sunyi in bisu naki sai Baba yace ka zauna tare da ni, duk da na lura Fuskan Hajiyarka a daure yake amma ta daure bata nuna mun kiyayya ba.
Naji bakin cikin rashin tafiya da kai da akayi.
Bayan an kawo mana labarin mutuwarsu Kuma na gane cewa babu Wanda yasan cewa ni ba Dan su bane sai kawai na cigaba da rayuwa na.
Matarka kuma, Hafsat kaunar tace yayi mun yawa sai na gane bazan iya barinta ba akan ka gwara in rasa ka, Dan nafi Sonta a raina a kan ka.
Da karfi Ahmad yace "shut up!!!! Wa ya gaya Maka ban San cewa ba iyayena suka Haife ka ba? To bari in Fada Maka, baba Da kanshi da ya Karbe ka yayi Mana magana cewa kai kanina ne in rike ka Amana. Duk da INA karami amma ta wajen Hajiyarmu na gane cewa ba ita ta haife ka ba. Wata Mai aiki ne tazo gidan Mu ba tare da ansan mijin ta ba, Ashe da ciki tazo, sai ta haifeka, daga nan mahaifiyarka ta Mutu, ba tare da ta fadi komai a kan Mahaifinka ba. Haka iyayena suka rungume ka hannu bibbiyu Dan su ceto rayuwarka Ashe Kaine me Halakasu? Bazan yafe Maka ba Kabir, azabar Allah duk su tabbata a gareka" kuma ka Sani ko Gadon da Aka bani Nawa aka bani. Nine dai nayi niyyan Baka Amma kayi mun kwace. Wanda kasan cewa tsakanina dakai akwai hisabi. Kuma cin Gadon wani Haramun ne, duk wanda ya zama daya daga cikin me cin Gadon Maraya wutar Allah zataci shi. Allah ya isa.
Kabir yayi wani irin ihu Har Lahira, sai dai Fatan Allah ya karemu daga Rike irin su. Allah ya hadamu da mutanen Arziki duniya da lahira Ameen.
Sergeant Ahmad ya fita yana share hawayen shi, General Hafiz ma ya zo da nashi hawayen ya daura hannayen sa akan bayan shi yana mai bubbuga bayan a hankali yana bashi Hakuri. Hafsat kuma tazo gaban shi ta tsugguna zata bashi Hakuri yayi saurin dago ta ya ce, Badan Mutuwanshi nake kuka Ba sai dan Kashe mun iyaye da yayi ya barni Maraya sannan ya Rabani da duk abun da Na Mallaka, matata da dukiyata kuma Har yana kokarin Raba ni da rayuwa ta. Akwai Allah. Kuma baki taba mun laifi ba. Ba ke bace sanadiyyar hadamu ba, Dama tun can asali kabir Mai son zuciyarshi ne, Har yayi sanadiyyar Mutuwan iyayena. Baki da laifi ko sanadiyya. Banso ace kabir yayi irin wannan Mutuwar ba. Naso ace hukuma CE zata yi mishi daurin rai da rai. Amma sai dai kash, Allah yayi ikon sa. Babu yanda muka iya sai dai addu'an Allah yasa Hakan ne Mafi Alkhairy.
Police ne suka zo da information akan irin Accident din da suka yi. Wai kamar yana cikin 'yan kungiya, Dan irin text din da aka turo masa a last Message dinshi shine "idan guduwa zakayi da yaran nan Dan son da kake musu, toh kasani zaka hadu da oganmu, kuma kasan cewa Talauci zaka shiga ko?" Ana ta karanto musu text Masu tsoratarwa wai shine dalilinsu Nayin Accident din. Daya police yace Tunda ance ya Mutu, Gawanshi Ma muna so, Dan hukunci da bincike za'ayi wa gawar.
Babu musu sergeant yace Ku dauka. Ya juya tare da rike hannun batula Wanda tuni ta Manta da inda Hankalinta yake, general kuma ya kamo Hannun Hafsat zuwa Mota. Dukkan su sukayi settling a mota sai General ya tambayi Hafsat ko akwai kayan da take so ta dauka da sauri sergeant yace Dama ita kadan ta tazo, bai bari ta shirya ba Da haka Bazamu koma gidan nan ba.
Dukkan su sukayi shiru. Sai suka ga fa Ashe dare yayi. Sai sukayi shawaran zuwa Misau Amma gidan su General Hafiz Dan washegari suke son wucewa  Abuja.
Dan Allah kuyi Hakuri Masu karatu. Karatune yayi Mana yawa. I love u all. Tnx 4 d messages, and also thanx 4 everything. Baku San irin Far in cikin da nake ji bane idan kunyi mun comment. Nagode. Sai kunji ni.

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن