PART 4

4.2K 94 0
                                    

5. MAKABARTARMU ~~ khadija Aminu~~~
"Kabir Ina son ka zauna da kowa lafiya, ka rike Maraicinka dan Fisabilillahi, Ganan mota nan ina so duk sanda Na fita aiki da wuri ka dinga kai Matata makaranta" kuma ka kula da motan sosai dan Motan sarauniyatace, ko bakaji mena fada maka bane?" Aliyu ke magana da kabir wanda shi kuma kabir duk maganan da ake masa bayama ji, kallon Hafsat kawai yakeyi da kowani mitsin da tayi, sai da yaji an tanbaye shi sai ya ke ta sunne kai wai Eh, ai yaya ko kullum kace in dinga kaita ai zan ina kaita.
yaya Ahmad kuma ya juyo yana kallon hafsat sai yace mata Babyna zo ki zauna kusa dani, bayan ta zauna sai yace mata Ina son ki yawaita yiwa kabir Nasihanki Masu dadi, kuma ki dinga zuba mai abinci dan bana son yana saya a restourant, kin gane?kin, sai tace mai eh. Shi kam a rayuwarsa yana son Hafsat saboda saukin kan ta. Yasan da watace da tace da nace maka baxan na samasa bane, mata kudin ga sanin me kuke gaya wa mijin ku Dan Fadin kyawawan kalamai ma kadai yana kara mai sonka a cikin zuciyarsa. Allah yasa Muyi koyi da haka, Amin.
Zuciyar Kabir bello Fari tas, dan yaji dadi sosai. Ranar Farko Ahmad ne ya sauke Hafsat a makaranta, tayi mishi Addu'an Allah ya kiyaye hanya. Ta shiga cikin skul. Bayan An gama classes sai ta tsaya a gindin wata bishiya tana jira a zo a dauketa, ji tayi an rufe mata ido ta baya kuma an ki sakin ta sai ta zata ahmad ne, sai murmushi takeyi. bude mata mota akayi, a ka sakata a gefen sit din mai zaman banxa, saboda ya rufe mata ido da dan yadi, sai ta fara cewa dan Allah My love ka bude mun ido na, plz!!!sai sakalci take zubawa kamar jinjira. shi kuwa ji yayi kamr kar ya bude mata dan tana bala'in burgeshi. dan duk 'yan matan da ya latsa bai taba ganin mai kyau irin ta ba, natural beuty Allah ya bata. zagayowa yayi sannan ya bude kofan dazai shiga ya fara tuki, bude mata ido yayi Mai zata gani, sai taga ashe kabiru ne, Ranta har ya baci sai tayi kokarin Hana ranta Masifar, sai ta ce Kabir meyasa kayi mun haka,ni fa Matar yayan ka ne ba Matar ka ba fa, kaji tsoron Allah fa sai yace kai anti hafsa Wasa ne fa kuma ni kanin mijin ki ne ni, ai al'ada ce wanda an dade da yinsa tun zamanin kakanni, kin manta wakan da akeyi ne? wasan kanin Miji akwai dadi, idan ana daka ya hau baya. Hafsat ce tace Allah ya kiyaye, kuma ya hanani yin wasan nan, ni Gaskiya Bana son wasan kanin Miji dan Akwai Hatsari a ciki, kawai dai take note, bana so. Murmushi kabir yayi yace nifa zan iya zama mijinki fa kar ki manta. Na dade da fada miki ke kadai ce Matar da nake so Bana son kowa sai ke, kishine ke kamani a duk sanda na ganki da yayana sai inji kamar in kashe shi wallahi in huta, Salati Hafsat tayi tace Dan Allah kabir ka daina irin wannan Maganar Dan Allah. Dariya yayi mai isarshi sannan yace Mata wallahi idan kika sake kwanciyar aure da Yayana sai na kashe shi, kinji Na rantse Miki. Amai ne yazo mata tayi kokarin bude kofa kawai sai kabir ya janyo ta ya zata guduwa zatayi kawai sai ta kwara aman a jikin shi. Bayan ta gama Mai isarta sai sannu yake mata. Tambayanta ya darayi Ne ya faru ko baki da lafiya ne? sai tace Mai Dan Allah ka kaini gida, haka ya kunna motan ya fara tsala gudu bai tsaya a ko ina ba sai a asibiti.

.6.MAKABARTARMU~~khadija Aminu
Emergency room aka kai hafsat saboda kafin su isa Aminu kano clinic Har ta fita daga hayyacin ta. kabir kan daya ga abin bana tsayawa bane a bakin kofan room dinta sai yaje mota ya canxa rigan sadan duk ga bata shi da Amai, sannan yaje rest room ya dan wanke jikinsa. Dawowan da zai yi clinic sai ya ga an fito da ita. Nurse ce ta fito tana tambayan wanda ya kawo budurwa? Anan ya tashi ba kwarin jiki yaje gurin doctorn, sai doctorn yace kainedoctorn wanda ya kawo Budurwa nan? ce eh. Toh za'ayi mata test yanxu amma a yanxu an sa mata drip da Allurai da zasu tsayar da Aman. Godiya yayi. Ya zauna a gefen ta yana jiran farfadowanta. Bayan Awa biyar da zuwan su ta farka da kiran sunan Hafizu! Hafizu ! Hafizu. Ai kuwa Dan Bakin ciki Tashi kabir yayi ya je ya kira doctorn, shi a tunaninsa ma Yayanshi Ahmad kadai takeso ashe har da wani ma hafizu, sai yace Gaskiya zan dau babban Mataki akan ki, Dan bake ba wani kato wai hafizu har Ma da ya Ahmad. Dariyan mugunta yayi a zuciyarshi, yana sarawa kansa. Hafsat kuma an kaita dakin test. Bayan an fito da ita aka kawo mata. Result bayan Awa daya. Likitan dai bai fada musu result din ba dan yana ga kamar dukkan su student ne, Dan Hafsat din ma unifoam ne a jikin ta, shi kuma kabir saurayine, bai ma yi kama da Wanda yayi aureba. Kawai sai ya yanke shawaran Hadasu su biyu dan ya musu Magana.
Bai fara da komai ba sai da yayi Nasiha mai ratsa jiki wanda Har sai da kabir ya fara jin haushin likitan sai yace Masa, mu ai ba masallaci mukazo ba neman nasiha, Asibiti ne nan. Anan gurin likitan yaji Haushi sai ya juya Kan Hafsat yace duk da bansan tsakaninku ba Amma Ni nasan cewa kin zubar da mutuncinki, idan aka ganki a ido baza a taba cewa zakiyi abun da kikayi ba Dan gaki kamar kamilallah. Allah ya shirya mana zuri'a. Sai yace kuje ga result din kina da cikin wata uku gashinan.Daram Kabir yaji a zuciyarsa. Ita kuma Hafsat tsayawa tayi Tana gode Wa Allah. Abun ma har sai ya dore wa Doctorn kai. Kabir ne ya fara rokon Doctor cewa Dan Allah Ka cire cikin Nan. Baxan sake abin da nayi ba, Nasan nayi kuskuren bin zuciyata, Nayi mata ciki. Amma bazan sake ba, kar mama na ta kashe Ni Dan Allah ka cire cikin Nan, har da Hawayen sa Na karya. Mamaki Hafsat ta fara yi Har ta kasa magana, Kabir Nason shegenta mata da Danta Dan Halak. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un kawai take furtawa sai Tace Doctor Wallahi Dan Da ke ciki na Dan Halak ne, da Uban sa. Yana shegan ta mun dana. Mahaifinsa ma idan yaji cewa ina da ciki bazai ce a zubar ba, jin dadi zai yi. Shut up!! kabir ya fada da karfi yana cewa, Fada min idan dana yana da wani uba banda ni. Doctor dai da yaji bazai iya da case dinsu ba sai ya sallamesu yace musu allah ya kyauta. ku fita kar in kira muku yan sanda. Kabir da karfi yaja Hannunta, duk da yasan ba wani warkewa tayi ba Har iyanxu da yake janta Hajijiya takeji, sai kiran sunan Ahmad takeyi tana cewa Nidai ka kaini gurin Miji na. Janta YAYI har mota ya sata a gefen sa yanda ma vazata gudu ba. sai asibitin Humairah Hospital Kano. Zuwa yayi gurin Doctorn Yace mai sai ya bashi Maganin zubar da ciki, Bindiga ya nuna mai Yanda ma ba yanda zai yi, Hakan kuwa akayi sai ya rubuta mai Maganin Amma yace mai idan Two month and above ne ba yanda zai yi ya cire. Amma duk da yasan cewa cikin yafi wata biyu sai kawai ya fita daga room din ganin doctorn, kuma ya rike hannunta gam. ya je wani Babban wajen siyan Magani a cikin hospital dinne ya siya, tun da akwai prescription na doctor sai suka bada kawai. a haka har suka isa wani gida. Get aka bude Mai sai kawai ya shiga. janta yayi har gidan a lokacin Ma har jikinta ya gama muyuwa dan bata da wani sauran Karfi. ko magana tayi baya jinta. Haka har ta hakura, shi kuma ya nemo Coke tun da dai ya lura cewa shine best drink din ta, ya hada da Maganin Ya saka. ya rufe da murfi ya ajiye a gefen ta. Ita kuma Tsabar yunwan da takeji dan rabon ta da cin abinci tun safe, ko break ma batayi ba.kawai sai ta dauki coke din nan tasha. Bata dade da sha ba kawai sai jini ya barke, duk abin da takeyi yana ta lura da ita dan ya labe ne yaga abin da zatayi. Shigowa yayi da tafi Yana cewa Buri na ya cika, saura burin Karshen In Mallake ki. Hahahhaha dariya kawai yakeyi sai ya wurgo mata wani leda yace Mata Toh na zubar da cikin da ke jikin ki, saura inje in kashe Mijin ki sai kuma in aure ki........ Ita kawai Maran ta ciwo yake yi bata ma san inda zata sa kanta bama, ihu tayi wani gigitaccen ihu a take yaja ta zuwa bayan gida, murna a cikin shi kamar ya ta zama a duniya.
A can kuma Ya Ahmad ya kira wayan kabir har ya gaji, yaje skul dan jin labarin su amma shiru, hankalin shi duk ga tashi, kuka yakeyi kawai sai yaji an turro masa text, Ka shirya Mutuwarka tazo, dan Na kashe dan cikin Matarka, kuma Ni kadai zan zauna da ita a rayuwa, kuma ka shirya sakinta kafin Mutuwanka, Nine Naka kabir.......

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now