The Strangers

11.8K 773 3
                                    

Kwanci tashi har muka gama J.S 1. Sanda za muyi promotional examination ban manta da alkawarin da nayiwa Hafsat ba, dan haka da akazo exams sai nayi ta amsa questions wrongly, wata kuma sai inyi jagwalgwalo yadda ba zai karantu ba, wata question din ma sai in barta blank inyi submitting. Na daina zuwa library sam -sam sai dai in kwanta inyi ta baccina. Rannan ina bacci da yamma Hafsat ta dawo daga karatu, ta daka min duka a cinya na tashi a zumbur a tsorace, ta hade rai sosai ta kalleni tace " what is wrong with you?" Na tsura mata ina mamakin nuna caring dinta. Ta taba jikina kamar mai testing temperature dina tace "are you sick or something?" Na girgiza mata kai still ina kallon ta kamar wata robot. "You are behaving strangely this past few days, what is wrong with you?" Ta sake tambaya ta tana me tsareni da manyan idanunta, na hadiye yawun tsoro nace mata " am OK, am just too sleepy these days" tace "but you know we have exams tomorrow morning right?" Nave mata "I have already read enough before the exams sister, don't worry, I will be okay" na yi murmushin tsokana na kuma ce mata "when did you start caring? This is so unlike u? Tayi murmushi itama tare da bude dan karamin bed side fridge dinmu, ta dauko lemo ta zauna a gefen gadon ta sannan ta kalleni tana yamutsa fuska tace "gobe ma rana ce and besides, I just asked to know what to tell Dad in case something happened. You can do as u wish for all I care, but I don't want to be held accountable for your foolishness" Daga haka ta bude drink dinta ta fara sha. Na juya idona sannan na koma na kwanta, mai hali dai baya fasa halinsa.
Babu wanda yasan me nake aikatawa a exams hall, har sai da mukayi hutu, muna 'yalleman principal dinmu ta kira dad a waya ta gaya masa cewa something is wrong, malamai sun kawo mata complain a kaina cewa duk na fadi papers dina kuma daga gani ansan intentional nayi. Muna zaune a dakin Inna, ina kwance a cinyar Inna ina zuba mata shagwaba ita kuma Hafsat tana kan kujera tana karatun wani novel, sai ga daddy ya shigo. Daga ganinsa nasan cewa something is wrong, nan take cikina ya bada kululu saboda nasan abinda na aikata a school. Ya zauna a nutse ya gaida Inna sannan mu kuma muka gaishe shi duka. Direct ya juyo yana kallona da serious face yace min "Maimoon mai yasa kika kayar da kanki a exams?" nan na fara inda inda, nace "am..I ..am sorry daddy, dan Allah kar ka dakeni wallahi bazan karaba?" Hafsat ta ajiye littafin hannunta tana kallon Daddy cike da mamaki. Inna ta jawoni jikin ta tana bubbuga bayana a hankali tana tambayar Daddy me ya faru cikin harshen fulatanci. Inda shi kuma ya kwashe duk yadda sukayi da principal din mu ya gaya mata, ya kara da cewa "ni ba dukanta zanyi ba. I just want to know why tayi hakan cos principal dinsu tana suggesting a mayar da ita school ta sake re-writing duk papers dinta" Cikin muryar lallami Inna ta kalleni tace "memu? Me yasa kika aikata hakan? Ke meson karatu kuma kikayi haka?" Na juya na kalli Hafsat ina hawaye, ita kuma ta harare ni tare da cewa "karki kalleni, I did my best inga kinyi karatu kika cemin you have read enough before exams" ta kalli daddy tace masa "Dad kullum bacci take yi bata karatu, innayi mata magana tayi min rashin kunya, God is my witness, I tried my best" tana gama fadin haka ta koma tayi kwanciyar ta.

Daddy ya juyo yana kallona yace "I know you Moon, nasan koda baki yi karatu ba zaki iya cin exams dinki, and your principal said what you did looks intentional. I just want to know why"
"I did it for Hafsat" nace a hankali, hawaye yana zuba daga idona "I want her to get ahead of me, I promised her zanyi repeating js1, I was just trying to keep my promise"

Hafsat ta mike zaune da sauri "What? Kunji yarinya zata shafa min kashin kaji ko? Daddy kaji rashin kunyar ko?" Babu wanda ya bata amsa amma duk ni suke kallo ana jiran in kare kaina, cikin kuka naci gaba da cewa "Hafsat ba ta sona, ni ban san me nayi mata ba amma bata son kasancewarmu a aji daya, she is always sad and lonely saboda duk ajinmu kawayena ne ita kuma bata son ta zama friend dina, I just want her to be happy ".

A lokacin su Mommy suka shigo falon ita da yaya Walid da Faruk, kallo ta bimu dashi daya bayan daya sannan ta zauna tana tambayar Daddy menene yake faruwa, shiru yayi bai amsa mata ba sai Inna ce ta fada mata brief abinda ya faru. A take Mommy ta dau zafi, daga ni har Hafsat din ta hada ta wanke mu tas. Dama tasan halin Hafsat amma bata dauka har a school bata kulani ba. "She is your only sister, me yasa ba zaki so ta ba? Me tayi miki a rayuwa?" Ta juyo kaina "and you little mouse, ta yaya zakiyi ki yi asarar shekara guda ta rayuwar ki just saboda kina so ki raba class da 'Yar uwarki, why didn't you tell me or your father about what is happening so that we can do something about it, we can put you in separate schools or something"

MaimoonWhere stories live. Discover now