The Awakening

11K 751 6
                                    

Sultan's POV
A lokacin da su David suka ajiye shi a kusa da motar sa, kasa tashi yayi daga gurin, wani irin zafi da wani irin radadi zuciyarsa take yi masa dan ba karamin illa kalamanta suka yi ga zuciyar ba, jira yake mutuwa ta karaso ta dauke shi, dan shi a ganinsa bashi kuma da sauran rayuwa a gaba. To menene sauran rayuwa in babu Moon? Dama itace farin watan data haskake rayuwar ta sa da hasken ta, to yanzu tunda babu ita kuma menene yayi saura in banda duhu? a cikin duhun zai yi ta lalube har yaje ya afka ga halaka, he was sure that he will be lost without her.

Yana kwance yaji tsayuwar mota a kusa dashi, a tunanin sa ma robbers ne zasu yashe shi ko kuma ma su karasa shi and he didn't care. Sama sama yaji muryar Amir yana yi masa magana, ya dan bude idonsa ya kalle shi ya mayar da idon ya rufe. What is this man doing here? Me ya kawo shi?

Yana jin Amir ya fara kokarin tashin sa, ya kwace, Amir yace masa "Sultan menene hakan kake yi wai? Moon ta kira ni tace inzo gurin ka, me ya faru? I really hope you are not drunk kuma? Sultan ya bude ido ya kalle shi sosai sannan yace cikin murya kamar ba tasa ba "Moon ce tace kazo nan?" Amir yace "eh, me ya faru haka?" Sultan ya fara kokarin tashi Amir ya taimaka masa ya bude masa mota ya shiga suka tafi.

Me yasa Moon ta kira Amir? Shin hakan yana nufin she still care about him ko kuma just tana so a dauke mata shi daga kofar gida saboda bata son ganin sa? Ya lumshe idonsa yana tunanin abubuwan dasu ka faru tsakanin su, she even said zata tabbatar da cewa dan da yake cikin ta bai san cewa shine mahaifinsa ba, she hates him that much kuma bai ga laifin ta ba, koma menene ya faru laifinsa ne.

Na farko ta ya akayi ma zuciyarsa ta raya masa cewa Moon sun hada plan da Ibrahim zasu hadu? How did he even think that? Kishinsa ya rufe masa ido kawai ya fadi magana without thinking kuma wannan maganar ita ce tafi komai bata wa Moon rai. Shi shine mai bad past, amma ita ko yaushe tana kyautata masa tsammani, ya tuna case din Khulsum, tun kafin ma moon ta tuntubeshi da maganar har ta yanke hukuncin karya suke masa, amma shi bai showing mata the same courtesy ba.

Wannan shine babbar nadamar sa a lokacin ba wai ture Ibrahim ba, that bastard deserves that, uban wa yace ya biyo su? Har cikin gidansa ya shiga gurin matarsa and he let him go, sannan kirikiri ya ganshi ya rike hannun matar sa a cikin store and he still ignored him, duk da cewa da kyar ya danne zuciyar tasa ya yi ignoring din nasa, dan a lokacin babu abinda zai bashi satisfaction irin ya ga ya zubar masa da hakoran da yake using yake smiling at his wife, amma ya danne zuciyar sa saboda a lokacin yana ganin laifin Moon ne kamar ita ce ta bada hanya, bayan sun fita kuma ya biyo su, why will he follow them in ba rainin hankali ba, waye suna tafiya da matarsa zai ga tsohon saurayinta yana binsu a baya kuma ace ransa ba zai baci ba? Laifin sa daya a lokacin, bai kamata yayi playing with rayuwar Moon ba, kamata yayi yayi packing motar ya fito da Ibrahim da ga tasa motar ya babballashi ya zubar a gurin sannan suyi tafiyarsu.

Suna zuwa gida a part din Amir suka tsaya. Amir ya fito ya zagayo ya fito da Sultan sannan suka shiga ciki, shi Amir duk a tunanin sa Sultan a buge yake, yana zuwa ya kwantar dashi a kan gado sannan ya debo ruwa mai sanyi ya kawo masa, yana fara sha yaji ruwan kamar madaci, ya furzar ya ajiye cup din a gefe. Amir ya zauna a gefensa yace "Sultan why do you do it? Ka samu good life with Moon why will you throw it all away saboda giya?"

Wani takaici Sultan yaji ya kama shi, ya juya masa baya yayi kwanciyarsa. Amma babu bacci babu alamarsa sam, yadda jiya baiyi bacci ba haka yau ma da alama ba zai yi baccin ba. Wata biyar kenan da aurensu da moon amma bai taba kwanciya ba tare da ita ba sai yau, bai taba tunanin kuma zai kwanta ba tare da ita din ba, amma yau gashi basa tare kuma duk suna raye, suna kuma gari daya.

She hates him, she even called the security on him tasa suka fita dashi ko kallon sa kuma bata yi ba, wannan ya tabbatar masa da cewa she meant what she said, rabuwa zatayi dashi kamar yadda wadda ta haife shi ta rabu dashi, kamar yadda wanda ya haife shi ya rabu dashi, bai damu ba ko ya mutu ko yayi rai.

MaimoonDove le storie prendono vita. Scoprilo ora