Save The Date

8.5K 699 12
                                    

Wajan azahar su Sultan sukaje 'yalleman. Sun samu tarya sosai dan dama an sanar da Baffa zancen zuwan su, kusan duk uncles din Moon sun zo taryan manyan baki. Kofar gidan Baffa kam cika yayi da mutanen gari da suka zo kallon sarki, a cewar su. Hakimai uku ne suka tafi tare da Galadima, Sultan kuma cousins dinsa guda biyu da Amir ne suka raka shi.

A palourn Baffa aka sauke su, aka gabatar da Sultan ya gaishe da Baffa da sauran uncles din Moon da suke wajen, Baffa yana ta tsokanar sa wai yazo har gida zai kwace masa mata, daga nan aka sallame su suka tafi gidan Nuraddeen suka bar manya zasu yi magana a tsakanin su. A gidan Nuraddeen suka ci abincin da akayi ta kawo musu kamar babu gobe, Sultan ya zauna yayi ta shan fura yana santi wai dama abinda Moon take sha kenan in tazo 'yalleman shine bata taba gayyatar sa ba. Nan da nan suka saba da Nuraddeen, yana ta bashi labarin Moon sanda tana yarinya.

Suna zaune Moon ta kira shi, Nuraddeen ne ya dauka, "ke wato yau kadai din ma ba zaki bar mana shi ba ko? Sai kin dame mu da waya?" Tayi dariya "kai Yaya, kira nayi fa in ce ya bani kai mu gaisa" yayi dariya "ni zaki yiwa yawo ko? Har da wani yaya sai kace da yayan kike ce min" suka yi dariya gaba daya sannan ya bawa Sultan, tace "so...how are you?"

Yayi murmushi yace "ke dai ki fadi gaskiya, kin kira kiji yadda nake ko kuma kin kira kiji me ake ciki?" Tayi dariya tace "yanxu shikenan bani da right din da zan kira ka? I just want to know ya kuka je" yace "lafiya lau muka zo Love, and maganar kuma da kike so kiji ni ma ban sani ba, suna can suna maganganun su" tace "ni ba wannan ne yasa na kira ka ba, so nake inji ya akayi aka saka maka hular rawanin nan da wannan gashin na kanka?" yayi shiru bai bata amsa ba, ta fara dariya, tace "don't tell me aski aka yi maka" ya bata rai yace "don't laugh, give it a week zai dawo ne. Besides, ba du aka aske ba ai" tace "can I see it?" Yace "never, ba zaki taba gani ba har sai ya dawo yadda yake"

A wajen su Baffa kuwa sosai suke ta shan hira abinsu, da yake Baffa mutun ne mai barkwanci nan da nan bakin suka saki jiki da shi suke ta hira. Sai bayan sunci abinci sunyi sallah sannan galadima ya gabatar da maganar data kawo su, suna nemawa dansu Abbakar Sadiq Abdullahi auren Maimunatu Muhammad Dikko, daga nan ya aika aka shigo da wata karamar jaka cike da kudi, aka ajiye aka bude, mint ne 'yan 1000, galadima yace "ga kudin aure nan, muna fatan zaku karba" kowa ya saki baki yana kallon kudin, uncle Aliyu ya kalli kudin da yasan zasuyi daga miliyan biyar zuwa sama, ya saka hannu ya dauki rafa guda biyu ya ajiye a gefen sa yace "mun gode sosai amma wannan ya isa, albarkar auren muke nema, wannan ma mun dauka ne saboda al'ada ne"

Tafida ya matso zai yi magana, Baffa yace "abinda zamu iya karba kenan. Tun sanda labarin yaron yazo mana na tura Aliyu yaje har Abujan yayi mana bincike akan yaron, kuma yace min ya gamsu da abinda ya samu, dan haka tunda shine waliyinta na yarda da maganarsa. Na bawa Abbakar Sadiq auren Maimunatu, Allah yayi musu albarka baki daya Allah kuma ya sanya alkhairi" gaba daya aka ce "Ameen"

Uncle Rufa'i yace "to sai maganar sa rana kuma, yaushe kuke ganin za'ayi?" Tafida yace "ni ina ganin kar aja kwanaki da yawa, matsalar dai kawai yaron bai kammala ginin sa ba, dan haka ina ganin a bashi wata uku insha Allah kafin nan ya kammala, ita ma amaryar kafin nan tayi shirye2n hidimarsu ta al'ada" kowa yace "wannan yayi, Allah ya kaimu" daga nan nan akayi addu'ar neman alkhairi aka tashi.

Sultan kam da aka gaya masa me aka yanke ji yayi kamar ya tashi sama dan daɗi, at the same time kuma yana jin kamar ya dora hannu aka yayi kuka. Tun a hanya yake mita "wai wata uku, ko garin Abuja zan gine gaba daya ai iyakacin kwanakin da za'a bani kenan, aikin ginin nawa da a cikin sati biyu zan gama shi, aikina ne fa" Ahmad, cousin dinsa yace "why are you whining ne Sultan? Tunda ance an baka ba shikenan ba? Me kake yiwa sauri ne wai" Sultan kawai tsaki yayi yace a ransa 'ba zaku gane ba'

A Abuja kuwa kiran gaggawa Daddy ya samu daga fada, nan da nan ya tafi, yana zuwa mai martaba sarki ya nemi a basu guri zasu gana, yace "Muhammad dama abinda kake shiryawa kenan? Dama dalilin da yasa ka dauki yaron nan kenan" Daddy yace "Allah ya taimakeka sam ba haka bane, mayar da Sultan gida na daban da alakarsa da yarinyar wajena" Takawa yace "bakasan halin yaron nan ba labarinsa kakeji, duk inda tunanin ka ya kai to ya wuce gurin. Ina tausayawa yarinyar nan, she have no idea what she is in for. Ka taimaka mata ka janye maganar auren nan. Bana son abinda zai bata zumuncin da yake tsakanin mu. Nasamu labarin irin tarbiyyar da ka bawa 'ya'yanka, sam yarinyarka bata dace da yaron nan ba. He don't deserves her"

MaimoonWhere stories live. Discover now