America

8.4K 642 7
                                    

Na jima sam babu bacci a idona, yanzu mai zan ce wa Daddy idan ya kamani da katoton namiji a dakina? Wato sultan shi bai san bari ba ko? Babu ruwan shi da what is right and what is wrong shi dai kawai in zuciyarsa ta raya masa yayi abu shikenan sai yayi kayansa babu ruwansa da consequences? Shi yanzu bai san cewa in aka gan shi a dakina a kwance akan gadona shikenan munyi hannun riga ni da shi ba?

Sai kuma na kara jin haushin kaina da yadda na kasa daukan wani kwakwkwaran mataki akan sa, na tuna maganar da Amira ta gaya min na cewa ya fini taurin zuciya kuma ina son shi da yawa dan haka zai yi matukar wahala in juya shi sai dai ya juya ni. And that just happened!

Dole in san abinyi. Amma na kasa aikata komai instead of inyi wani abu sai kunnuwa na baza cikin tsoro ina sauraron ko zanji motsi, ko motsin Sultan ko motsin wani daga waje amma shiru banji komai ba, a haka har bacci barawo ya dauke ni.

Dai dai sanda na saba tashi kafin assuba na farka, jikina duk sai ciwo yake yi sakamakon kwana a kasa da kuma takurewar da nayi a guri daya. Nayi mika ina addu'ar tashi daga bacci, Sultan ne ya fado min a raina nayi sauri na mike na kalli gadon. Babu shi babu alamunsa, babu alamun ma mutum ya kwana a gadon saboda gadon a gyare yake tsaf, to ko mafarki nayi ne? Kai ba mafarki bane tabbas Sultan ya shigo dakina jiya da daddare, na karasa gaban gadon sannan naga rose flower a ajjiye a saman wata farar takarda, na dauka na bude na karanta "na dade banyi bacci mai dadi irin na jiya ba, thanks for the night" da sauri na yayyaga takardar ina rarraba ido gaba na yana faduwa, yanzu idan wani ya karanta wannan ai sai yayi tunanin wani abu, lallai sultan, da ace bangani ba na tafi school Mommy ko wani ya shigo ya ga wannan takardar kuma fa? Rose flower din na dauka na kai hancina na shanshana ina lumshe ido tare da murmushi, lokaci daya ina jin haushinsa da nake ji na abinda yayi yana barin zuciyata son sa yana kara cikata, na tafi da baya na fada akan gadon irin yadda yayi jiya sai dai ni banji gadon ya amsa ba irin yadda ya amsa sanda shi ya faɗa, gadon naji gabaki daya kamshin sa yake yi. Sultan is special, he took a special place in my heart.

Ina gama shiryawa na fita palour muka yi breakfast da duk family din. Ana yi ana hira amma ni kam hankali na har yanzu ba'a kwance yake ba ina tsoron ko wani yaga sanda Sultan ya hau window na ko kuma anga fitarsa, har muka gama breakfast shiru babu wata magana mai kama da wannan, sai a lokacin na fara sakewa ina dariya.

Daddy yace "Moon supervisor din ki ya aiko min da takarda akan project dinki. Yace da akwai wani experiment da zaki yi amma sai kinje John Hopkins hospital ko?" Ni fargabar Sultan ma ta saka na manta da wannan maganar nace "eh Daddy, dama ina son inyi maka maganar bansan ya za'ayi ba" Mommy ta ajiye spoon din hannunta tace "john Hopkins? Wai kuna nufin America?" Nace "yes Mommy" nan da nan Mommy ta fara daukar zafi tana girgiza kanta "wanne irin experiment ne ba za kiyi shi a duk girman UK ba sai kinje USA? Wa kika sani a America ma tukunna? Gaskiya dear kayi magana a chanza mata wani experiment din, ai a ko ina ana substitute, gaskiya ni ban yarda kije America ba"

Daddy kawai kallonta yake yana murmushi ita kuma murmushin nasa ne yake kara kular da ita. A karshe Yace "babu abinda zai same ta in taje America, it will be an experience to her, kuma abinda na fahimta shine ba ita kadai bace suna da dan yawan su za'a tura daga makaranta, dan haka in sunje tare zasu yi komai su dawo tare. Shi asibitin John Hopkins shine number one a duniya a harkar neurology dan haka zuwanta can din yana da muhimmanci sosai" Mommy dai har yanzu kai take girgizawa alamar bata gamsu ba, Daddy ya kuma cewa "look, shi kansa director na pediatric neurology department na assibitin is a friend of mine, Benjamin Carson, kafin su tafi zanyi masa waya, in hada shi da ita, mutumin kirki ne sosai, shi da matarsa Candy, idan ba kya son ta zauna a cikin students sai taje gidansu ta zauna acan, na tabbatar zai kula da ita sosai. Mutum ne mai dimbin ilmi dan yana daga cikin top knowledgeable mutane na America"

Nan dai Daddy ya dauko wayarsa yayi wa Ben waya yayi masa bayanin zuwana da irin aikin da zamu yi ya kuma roki dan Allah ya sa idonsa a kaina. Da yake weekend ne shima Ben din yana gida sai bawa matarsa suka gaisa da Mommy. Har suka gama wayar dai Mommy bata saki fuskarta ba.

MaimoonWhere stories live. Discover now