Maldives 1

10.5K 716 9
                                    

Riyadh;

Three weeks after the gender reveal party.
Sosai Takawa yake putting pressure a kan Sultan, Sultan ya kara saka ni nayi wa Ummee magana amma wannan karon ko kallon kirki ban samu daga gareta ba. Sai ma ce min tayi in gaya wa wanda ya turo ni yazo ya same ta da kansa. Sam yanzu Sultan bashi da cikakkiyar nutsuwa, yana son komawa gurin babansa kuma baya son ya bata wa ummeen sa rai.

Ina yin iyakacin kokarina gurin kwantar masa da hankali amma nasan Sultan is a busy person, zaman banza da rashin aikin yi shi yake irritating dinsa, duk da ya samu Ahmad sun kulla abokantaka, kullum zai zo ya dauke shi su fita amma hakan is not enough for Sultan. Yanzu har ya kai matakin in Takawa ya kira Sultan sai yaki dauka, he is out of excuses.

Rannan ina shiryawa zan shiga gurin Ummee Sultan kuma yana kwance akan kujera ya rufe idonsa, nasan ba bacci yake yi ba, sai da na gama shiryawa sannan na durkusa a kusa dashi na hura masa iska a fuskarsa, ya dan bude ido yana kallona, nace "zan shiga gurin Ummee" ya mayar da idonsa ya rufe yace "zan shigo an jima" na tashi na tafi jikina babu dadi, bana son ganin Sultan cikin damuwa sam, sai inji duk nima na shiga damuwar. I must do something about this.

Ban sha wahalar hada Sultan da ummeensa dan in cigaba da ganinsa cikin damuwa ba, amma kuma menene abinyi? A harkar da ta shafi iyaye dole mutum yayi taka tsan tsan. A bedroom na sami Ummee tana zaune a kan gado da system a gabanta, na shiga da sallama, ta amsa min idonta akan screen din system din, sannan tayi min alama da hannunta na inzo in zauna kusa da ita, ina zama ta juyo min da screen din system din, fuskarta dauke da murmushi tace "what do you think of this?" Na kalli abin da take nuna min, model ne na dakin baby, with complete furniture, crib, drawers, night stand, changing table da komai, dakin yayi kyau sosai, amma kuma Sultan ya gama tsara mana baby room din mu tun sanda yake zana plan din gidan mu a Abuja.

Na kasa bawa Ummee answer, ta cigaba da magana "ina tunanin bedroom din tsakiya na part dinku za'a mayar nursery, Sultan sai yayi mana dan renovating dinsa kadan, yayi closet a ciki, sai mu fara order kaya kuma, furnitures first, sai electronics sannan sai mu dawo kan clothings" tayi ajjiyar zuciya, "we have alot to do, list ya kamata mu rubuta..."

Sallamar Sultan ce ta katse mata maganar ta, muka amsa masa a tare, yana kallon mu yace "yau hirar ta daki ce kenan" ta dan bubbuga kan gadon kusa da ita tace "come Abubakar, sit with us" ya karaso ya zauna yana satar kallona, tace "we were just talking about the baby, nursery muke so mu fara shiryawa, muna bukatar taimakon ka gurin renovating dakin" ya dan dafe kansa kamar mai ciwon kai yace "Ummee babyn nan fa yana da atleast wata uku kafin yazo, besides already yana da room dinsa a Nigeria" take naga murmushin fuskarta ya kau, tace "Nigeria? I tot I made myself clear cewa babu zancan komawa Nigeria ko?"

Sultan ya bata rai, he has reached his limit. Ya saka hannu ya dauko wayar sa yana dialing, kawai sai gani nayi ya ajiye ta akan table din gaban gadon, tana kara sai kuma mugaji an dauka, muryar Takawa, yace cikin fada "Sultan wato ina ta kiranka shine kaƙi dauka ko? Wannan wanne irin aikin banza kake aikatawa haka? Kawai ka dauki iyalinka ka tafi dasu can wata uwa duniya ku zauna a can? Zaman me kuke yi har yanzu? Aikin da ka bari wa zai yi maka? Wa kake tunanin zai ke kular maka da companyn ka?"

Sultan yayi gyaran murya yace "barka da yamma" Takawa yace "bazan amsa ba, me ya hanaka dawowa har yanzu?" Sultan yana kallon Ummee yace "bani na hana kaina tahowa ba, Ummee ce tace bazan dawo Nigeria ba a Riyadh zan cigaba da zama, na saka ka a speaker phone yanzu tana jin abinda kake cewa, sai kuyi magana a tsakanin ku" na kalli fuskar Ummee naga wani mixed emotions, sama sama take numfashi, ta kasa magana, Sultan ma ita yake kallo ita kuma wayar take kallo.

An jima a haka sannan Takawa yace "Khairat, kin san dai bai kamata kice zaki hana yaron nan dawowa gidan su ba ko?" Ta hadiye yawu ta kara bata fuska tace "why not? Nan ma ai gidan su ne, kamar yadda yake da iko da gidanka haka yake da iko da nawa. Kamar yadda kake da iko dashi haka nima nake da iko dashi, in fact na ma fika iko dashi, nace ba zai dawo ba and that is final"

MaimoonWhere stories live. Discover now