Not The End

17.9K 1.1K 165
                                    

One Year Later

Daddy yayi retire daga ambassadorship, yace lokaci yayi kuma da ya kamata ya dawo Nigeria ya zauna cikin 'yan'uwa da abokan arzikin sa, tunda dai yasan ya tara da yawa, ya kafa kansa ya kafa 'ya'yansa, ko da ace bai tara dukiya ba 'ya'yansa kadai sun isa su rike shi zuwa karshen rayuwarsa.

Yaya Walid yana aiki a kamfanin hakar man fetur na SHELL a matsayin engineer, sosai yake samun kudi kuma da yake shi mai nutsuwa ne sosai da tattali, nan da nan ya fara shiga layin wadanda za'a kira da masu kudi.

Yaya Habeeb yana aikin banki, duk da cewa shi mai yawan kashe kudi ne amma yana samun cigaba shima. Ni kam da ni da Hafsat medical doctors ne, duk da dai har yanzu babu wanda ya fara aiki a cikin mu amma mazajen mu sun ishe mu duk bukatun mu.

Faruk ya gama service dinsa ya koma masters, tun kafin ya tafi yace a nema masa auren Huda amma Daddy yace sai ya gama karatu ya samu aikin yi sannan za'a yi masa aure, an dai shigar da maganar manya sun sani. Daddy yana dawowa Nigeria ya aika 'yalleman aka dauko inna da Hajja ya dawo dasu Abuja su zauna tare dashi, tunda 'yalleman din kusan babu kowa sai uncle Rufa'i, shi kuma ba mazauni bane sosai.

Tunda labarin retirement din Daddy ya bazu a Nigeria, nan da nan aka fara aiko masa da offer din aiki, federal government, ministries, companies amma duk yaki karba yace hutawa yake so yayi. Amma bai dade a gida ba kuma sai yaji zaman gidan ya ishe shi, tunda babu kowa a gidan sai su Inna da 'yan aiki, Mommy har yanzu tana aikin ta, dan haka rana daya Daddy yace ya karbi offer din da university of Abuja ta aiko masa akan ya zama next VC idan tenure din wanda yake kai ta kare. Dama shi Daddy harkar siyasa ce baya so, amma yana ganin as a VC zai taimakawa kasarsa without getting involved in politics.

Bikin su Ya walid yana da wata goma Zainab da Fadila, wadanda yanzu sun zama kawaye sosai, suka haihu kusan a tare, Zainab ce ta fara haihuwar baby girl aka saka mata Mommy, ranar sunan ta Fadila ta haifi Daddy, dan haka yaran suka tashi kamar tagwaye, small Mommy da small Daddy.

Hafsat ta juye ta sake dauka. Lol. Ta haifi danta namiji watanni biyu bayan haihuwar Al'ameen. Mukaje England muka sha suna, yaro yaci sunan baban Zayed, AbdulMalik, muna kiransa da Ayaan. Watannin Ayaan biyar a duniya Hafsat ta kira ni tace min wani cikin ne da ita, nace "kai Hafsat, wannan ke ai har kinfi Mommy ma" tace "ai dama haka ake yi, idan ka koyi abu a gurin mutum sai kazo ka fishi iyawa kuma" mukayi dariya, tunda dai duk ita da yaranta lafiya lau suke to babu wata matsala.

Anyi bikin Amira da Mahdi, mun je kano munsha hidima. Duk da dai Sultan ya hana ni kwana yace Al'ameen yayi kankanta da shiga biki, ni kuwa nasan bata Al'ameen yake ba, ta kansa yake, dan Sultan yana nan yadda kuka san shi babu abinda ya ragu sai ma ince karuwa yayi. Mahdi ya samu aiki a asibitin malam Aminu kano. Last wayar da mukayi da Amira itama ta gayamin ta kamu. Suna zamansu lafiya lau from all indications.

Ibrahim da Jewel dinsa Amina kam soyayya sai abinda ya kara gaba. Dan ko ziyara mutum yaje gidan su sai ya fahimci suna kaunar junan su. Maman Ibrahim ma ta dauki son duniya ta dora akan Amina dan tana ganin itace sanadiyyar dai daituwar dan ta. Ita kuma Amina ta rike little Moon tamkar ita ta haife ta, in baka sani bama ba zaka ce ba ita ta haife ta din ba. Kullum kaga Ibrahim zaka ganshi cikin farin ciki, alamar cewa hankalinsa a kwance yake. Sosai suke zumunci shi da Sultan, dan wani lokacin ma har yazo gidan mu ya tafi bana sani, sai daga baya sannan Sultan ya gaya min. Sai dai kuma har yau, duk ranar da muka hadu da Ibrahim muka gaisa sai naga kishi a idon Sultan, sai dai baya nuna wa har wasu su gane. I guess some things will never change.

An samu karuwa a gidan Amir shima. An samu namiji wanda a take Amir ya saka masa sunan Sultan. Abubakar Sadiq Abdallah. Kuma ake kiransa da Sultan. Sultan yaji dadi sosai amma sai ya bata fuska yace "ko kara ma babu? Sultan zaku ce masa kamar wani sa'an ku? Ina lefin ma ku ringa ce masa Yaya?" A raina nace 'ho, Sultan akwai son girma'.

MaimoonWhere stories live. Discover now