His Father's Son

11.5K 708 1
                                    

Washe gari bamuyi missing sallar assuba ba kaman jiya, Sultan ne ya fara tashi, sai da yayi alwala sannan ya tashe ni shi kuma ya fita masjid, ya jima bai dawo ba har nayi sallah na dan taba karatun al'qurani sannan nayi morning azkar dina, ji nayi duk na gaji da kwanciya, I wanted to do something, na tashi na gyara dakin na wanke toilet, na dawo palour ina cikin gyarawa ya shigo, ya tsaya yana kallona "wato matar nan kin warke ko? Shine zaki kama aiki da assubar nan ko?" Nace "na gaji da kwanciya ne kawai, I want to do something"

Ya fara tahowa yana min murmushin mugunta yace "You want to do something? I have got something for you" na ajiye duster din hannuna na fara ja da baya ina jin tsoro har cikin raina dan ban manta azabar da nasha ba. Nace "Sultan, Allah ban warke ba, dan Allah kayi hakuri wallahi na daina aikin zan koma in kwanta" ya karaso in da nake yace "really baki warke ba? Can I see?" Nayi saurin girgiza kaina nace "you are not a doctor how will you know if a wound is healed or not?" Yace "am not a doctor but ni mijin doctor ne, dan haka believe me I will know" idonsa kawai na kalla nasan kona roke shi it will be to no avail, jikina har karkarwa yake yi saboda tsoro, me yasa nayi aure ne wai? A kunne na ya rada min "believe me, it will not hurt".

And it didn't, at least not as I expected. Yana cikin bacci na zare jikina na tashi, a hankali na lallaba na saka kayana na fice, da sauri na karasa dakina ina shiga nayi locking kofar, finally nazo dakina after two days, da sauri sauri na gyara dakin duk da ba wani datti yayi ba, na shiga toilet na shiga shower ina wanka, at last zanyi wanka without Sultan standing and watching. Na fito na zauna na shirya a tsanake cikin atamfa ruwan hoda, nayi 'yar kwalliya kadan na fesa turare na fito.

Ina fita palour na tarar da wata tsohuwa a zaune a kan carpet da wadansu 'yammata su biyar daga can bakin kofa, ina fitowa duk suka mike tsaye kansu a kasa, 'yammatan kamar harda tsoro a fuskarsu, sai da na zauna sannan suka durkusa suka fara gaisheni daya bayan daya, na saki fuskata sosai na amsa musu. Babbar matar ce ta matso tace "ranki ya dade, Allah ya taya miki, Allah ya dora ki akan makiyanki, Allah yaji kan magabata, Allah kuma yasa albarka a zuriya" nace "Ameen"

Ta cigaba da magana "ranki ya dade ai jiya ma munzo, muna nan har magriba bamu samu ganin ki ba. Dama mai babban daki (yaya) ce ta turo mu, tace tana gaishe ki sosai, kuma tace duk mu shidan nan mu dawo nan gurinki mu zauna muke yi miki hidima. Ni sunana Gaji, tun asalin kakanni na bayi ne a wannan gidan, anan aka haifeni anan na girma nayi aure na hayayyafa, 'ya'yana ma suka yi aure suka haihu duk acikin gidan nan, guda biyu daga cikin 'yammatan nan jikokina ne. Kamar yadda aka kawo 'yammatan nan gurinki yanzu haka aka kaini gurin mai babban daki sanda tana amarya, wannan shi yasa nake daga cikin amintattun bayinta, kuma wannan shi yasa ta zabe ni akan in zo in zauna a gurinki, saboda tasan zan rike mata amana. Suma wadannan duka yaran da kika gani zababbu ne dan ni ta saka in zabo mata masu tarbiyya da rikon amana kuma na zabo su. Insha Allah zamu rike ki da amana Allah kema ya baki ikon rike mu da amana."

Kawai naji matar ta kwanta min araina, na tambayi yaran duk sunayensu suka fada min, naga duk sunki sakin jikinsu sai na fara yi musu wasa, ba'a jima ba suka fara dariya. Da kaina na tashi na kaisu har bq din mata na nuna musu komai sannan muka dawo tare. Nace "Ku dauke ni a matsayin yayar ku kunji, dama ni bani da kanne mata kunga shikenan na samu, duk abinda kuke so kuyi min magana in dai ina dashi zan baku, abinda bana so shine kazanta, ku kula da tsaftar gidan nan ku kuma kula da tsaftar jikin ku, ku kame kanku banda shiririta. Allah ya bamu ikon zama lafiya".

Sunji dadin yadda na karbe su, kuma daga dukkan alamu sunji dadin bq din dai sai murna suke sunzo gurin 'yan gayu. Nan take baba Gaji ta raba musu kowa da aikinsa, jikokinta guda biyu su ta bawa part dina, sauran kuma sauran parts din gidan. Banda part din Sultan. A take suka tashi suka fara aikin su. Ina zaune sai ga abinci daga cikin gida, suka je suka ajiye a dining room sannan suka zo suka gaishe ni, wai Hajiya tace tana gaishe ni, na amsa musu, naga suna ta kallon 'yammatana da Baba Gaji da naga ta hade rai.

MaimoonWhere stories live. Discover now