Amira 2

7.4K 701 18
                                    

Cikin tsananin mamaki nace "what? Waye ya gaya maka haka" gani nayi yana kallon office din kamar me neman wani abu, nima na taya shi dubawa, sai a lokacin na tuna cewa tare da Amira muka shigo office din, babu ita babu alamar ta. A zuciye naga yayi hanyar kofa yana cewa "I will murder that bitch" jiri naji yana kokarin dibana, nayi sauri na zauna a kujera, nasan da za'a gwada jini na a lokacin za'a tarar ya hau, Amira? why? Me yasa zata yi min haka? I trusted her. Babu abinda banyi mata ba kuma babu abinda ba zan iya yi mata ba.

Ina zaune rike da kaina da yake juyawa Ibrahim ya dawo cikin office din idonsa kamar garwashin wuta, ya fara zagaye office din da alama jinin yarabawan ne ya motsa. "She told me lokacin da Daddy ya san alakar mu ya hada ki aure da wani cousin dinki a 'yalleman, she even showed me the wedding invitation, after a year tace kin haihu" sosai kaina yake juyawa dan sama sama nake jin maganar sa, lokaci daya kuma naji wani realisations yayi hitting dina, Hafsat, oh dear God no, not Hafsat, I can take betrayal from Amira but not from Hafsat, na juyo na kalleshi nace "kaima ance min kayi aure, ka auri Lati" ya tsaya a zagayen da yake yi, yazo ya tsugunna a gaba na, expression din fuskarsa na kalla naji wani dadi a raina, at least Hafsat gaskiya ta fada.

Yace "yes, na auri Latifat shekara daya bayan rabuwar mu, amma ban karbi auren ta ba sai bayan da na samu labarin kinyi aure tukunna..." Na katse shi nace "and kawai daga Amira ta gaya maka nayi aure you just believe her? ba zaka bincika ba? ask around? ba zaka kira ni ba kayi confirming daga baki na ba?" na danyi shiru ina controlling temper dina, sannan na cigaba "you switched off your phone, you didn't even call me, you just left without a second look...." Maganar ta tsaya a makogwarona saboda tuno irin dacin zuciyar da nayi fama da shi a wancan lokacin.

Ya mike tsaye ya koma ya zauna akan kujerar da take kallon tawa, har yanzu bai ce komai ba, na dago kai na kalleshi muka hada ido na mayar da ido na kasa, a hankali naji yace "kin chanza sosai, you look more beautiful, more beautiful than I kept imagining you would be" a hankali nima nace "it doesn't matter, abinda nake so kawai in sani shine 'why?' Dama tun farko bada gaske kake sona ba ko kuma bayan ka tafi ne ka chanza ra'ayi?" Ya kara jawo kujerar sa kusa da tawa yace "Maimunatu kema kinsan amsarki, I love You, more than life itself. Ki tsaya ki saurari labarin abinda ya faru bayan tafiya ta, ina tabbatar miki da cewa zaki yarda cewa it hurts me more than it hurts you. I was fooled by your friend, totally fooled" na sake dago ido ina kallon rinannun idanunsa da suke kaina. Nace "OK. Ina jinka, tell me, what happened?"

"Bayan na bar gidan ku a ranar nan, na koma makaranta, ina zuwa na kashe wayata na ajiye saboda nasan zaki kira ni, ni kuma a lokacin gani nake yi as long as ina jin muryar ki I couldn't stay away from you. I thought I was strong, na dauka zan iya zama babu ke har sai na samu abinda nake nema, har sai nasan na isa in zo in nemi auren ki. I had your number in my memory, dan haka plan dina shine duk sanda naga cewa it's OK to return sai in kira ki. Ranar sam banyi bacci ba, washegari na tashi da rashin lafiyar da har sai da aka kwantar dani a clinic din school. Sati da daya ina jinya sannan na dan samu sauki nace su sallame ni, suna sallamata na shiga office din PC na bata takarda ta ta barin aiki, bana son duk sanda na tashi dawowa neman aurenki ya zamanyo ina jingine da babanki ne. Kayan da suke gidana duk na hada na sayar na dau jakar kayana na fita daga makarantar, gidanku na fara zuwa na bada sakon CD a gurin mai gadi sannan na wuce tasha, bazan iya misalta miki yadda nake jin raina ba a lokacin Maimunatu, ina jin haushinki a lokacin sabida ƙin gaya min gaskiya da kika yi kuma ina jin wani irin sonki a raina, sannan ga alhinin rabuwa dake kuma, ji nake kamar na chire wani bari na jikina na ajiye. I was tempted to call you then, na dauko waya ta na saka sim na kunna, sai kuma na sake kashewa na cire sim din na jefa shi ta window din motar. Da muka je ibadan ma na jima shima ina rashin lafiya a can, hatta Mama bata san abinda yake damuna ba ballantana su Munirat, na gaya musu na ajiye aikina na Abuja, kawai dai sun fahimci cewa it had something to do with you"

MaimoonWhere stories live. Discover now