A Step Further Away

5.6K 563 0
                                    

Basu dawo ba sai daf da Magrib. Suka dawo da kaya niki niki. Hafsat ta zauna tana bani labari kamar zata ari baki "gaskiya Moon kin yi missing, kowa yazo kuma kowa sai ya tambaye ki"

Nayi murmushi kawai, a raina ina cewa Hafsat ba za ki gane ba. A lokacin ne Mommy take cemin an bawa Amira scholarship award dina, na tambayi Hafsat nace "ya Amira tayi kuwa da aka bata?" Hafsat ta tabe baki tace "kema kinsan ya tayi ai, she first said it was a mistake, sai da pc ta kira su ita da maman ta tayi musu bayani cewa it is a gift from you, baki ga maman ba har da hawaye tana yi wa Mommy godiya. Ni fa banji dadi ba Moon, you are too soft wallahi, wai duk abinda yarinyar nan tayi miki amma shine zaki wani bar mata scholarship award dinki"

Mommy ta dan bata rai tace "me Amiran tayi wa Moon?" Hafsat tayi sauri tace "it is nothing mommy, wani small girls issue ne kuma munyi solving tun a school" daga gani kasan Mommy ba ta yarda da bayanin Hafsat ba, kawai dai tayi shiru ne.

Nan suka dauko min gifts dina suka nuna min. Duk a ciki guda biyu sunfi birgeni, na farko medal din da school ta bani, na glass ne me kauri, a ciki anyi rubutu da golden colour kamar haka:
    
*Award of Excellency*
           *To*
*Maimoon Muhammad Dikko*

*For being the most talented student this school has ever had.*

Na biyu kuma students ne suka bani, shi kuma da wood suka hada shi, a tsakiya sun yi zanen moon, a kasa kuma suka rubuta:

*Thank you Moon for brightening our lives. We will forever miss You.*

Kawai sai naji hawaye a ido na. Hafsat ta dauko wayarta ta nuna min video da 'yan set din mu suka yi suka ce a nuna min. Duk sunyi kwalliya kuma they are all laughing and talking at the same time.

"Moon ashe baki da lafiya?
We miss you today, kinga gifts dinki?...... "

ina dariya kuma ina hawaye at the same time, can wata a videon tace "Moon shine kika rike mana uncle kika hana shi zuwa ko? Hafsat tace yana can yana jinyar ki, ki gaishe shi kice we miss him also" na kalli Hafsat ita kuma ta daga kafada.

Wato karya tayi musu tace muna tare da Ibrahim shi yasa basu ganshi ba. Class monitor din mu Hamidda ta hada min take away na duk abinda aka ci a gurin party da handwritten note na get well soon.

A ranar da daddare sai ga Amira da mamanta sunzo yi min godiya har gida, Mommy ta kaisu gurin Daddy shi ma suka yi masa godiya. Daga nan muka tafi dakinmu muna hira, anan muka ba ta labarin tafiyar mu England, nan take  fuskarta ta chanja kamar zatayi kuka. Nace mata "Amira ni ina ganin ki nemi admission ke ma a Oxford kawai sai mu tafi tare, kinga sai ki zauna a gidan mu muke zuwa makaranta tare"

Ta girgiza kanta idonta fal kwalla tace "I can't. Mama bata da kowa a garin nan sai ni. Bazan iya barin Nigeria in barta ita kadai ba. University of Abuja zan nema saboda in zauna a gida. I wish you guys best of luck in England, in kun je please ku kira ni saboda in samu number dinku ta can" nace mata "insha Allah, you will be among the first ones da zan kira"

Haka muka yi ta hira har sai da suka zo tafiya. Casually ta tambayeni "ya labarin Uncle din mu kuwa? Naga shima bai je partyn mu ba" na kalleta sai ta sunkuyar da kai. Hafsat ce ta gaya mata directly "yayi resigning daga aikin sa ya koma Ibadan" ina kallon fuskarta ta chanza kala lokaci daya "but you are in contact right?" Hafsat tayi sauri tace "What is it to you, in suna da contact?" Na dakatar da Hafsat da naga ta fara daukan zafi, nan na bawa Amira labarin duk abinda ya faru, na kara da cewa "I believe He will come back like he promised" Hafsat ta ja tsaki tace "wahala da rai" tun daga nan Amira bata kara cewa komai ba har suka tafi"

Washegari muka tafi 'yalleman, satin mu guda acan kamar yadda daddy yace. Amina cousin din mu da muke kusan sa'anni sati daya na bata, ta dage lallai sai ta bimu England da kyar daddy ya lallabata yace ta bari in ta gama sec sch itama sai a kaita can ta yi karatu.

MaimoonWhere stories live. Discover now