The News

9K 722 4
                                    

Moon's POV

Na jima da wayar a kunnena ina lissafa maganar ta amma na kasa bata amsa saboda wani irin shock da naji, har saida tace "Moon kina jina kuwa?" nayi sauri nace "ina jinki Hafsat, bara in duba pictures din"

Na katse kiran na shiga WhatsApp, hannuna har rawa yake yi "oh dear God, let it be" na fara downloading picture din amma gani nake yi kamar ba zai gama budewa ba, sau biyu yana failing ina sake trying. Finally ya bude, sai da na dauke numfashi na saboda mamaki abinda na gani, hoton balarabiya na gani, amma kuma kamar Sultan da siffar mata, the eyes, the nose, the lips, the eye lashes duk irin na sultan ne, hatta murmushin da tayi a hoton irin na Sultan ne, farin fata kawai ta fishi sai kuma kasancewar ta mace ce, amma kuma anya wannan ce ta haifi Sultan? She looks too young to be his mother, amma kuma har sunan iri daya.

Na kira Hafsat, tana dauka tace "kin ganta ko Moon?" Nace "na ganta Hafsat. A ina kuka hadu?" Ta fara min bayani "cousin din baban Zayed ce, kanwar babansa, to irin bata shiga mutane sosai shi yasa tun da muka zo bamu ganta ba, sai dazu baban Zayed yace masa lallai yau ya kaimu gidanta mu gaishe ta. She lives alone a gidan nata ma. Wato Moon kudi ne da ita kamar banza, 'yar kasuwa ce sosai, babu ɗa babu jika, babu kuma miji, ina ganinta gabana ya fadi, nayi ta kallonta ina tunanin dawa take yin kama? Kawai sai da tayi murmushi na gane Sultan ne, kuma na tuna cewa mamansa balarabiya ce. Amma ban tambaye ki sunan maman Sultan ba"

Na sauke ajjiyar zuciya nace "Sunan ta Khairat" da sauri Hafsat tace "Allah da gaske? Moon ita ce mamansa kenan?" Nace "I don't know Hafsat, amma baki ganin tayi yarinta da yawa?" Tace "ke dalla can hutu ne fa, kinga sisters dinta data girma kuwa?" Nace "amma me Zayed yace miki a dangane ta ita? Ta taba aure a nan ko kuma ya labarinta yake?" Hafsat tace "it is all mysterious Moon, Zayed bai san komai a kanta ba, da yake shi kinsan ba'a Riyadh ya tashi ba kawai abinda ya sani shine rayuwar ta take yi ita kadai bata shiga mutane, kuma tunda ya santa bata da aure"

Na danyi shiru ina tunani nace "please Hafsat can you get her to talk to you?" Hafsat tace "I think so, kinsan hali na da bin kwakwkwafi, kuma daga gani na ta fara sona bansan dalili ba, ga kuma Khairat mai sunan ta" sai kuma tayi shiru sannan tace "wai dama sunan ta kika sakawa Khairat?" na danyi dariya nace "eh sunan ta ne" Hafsat tace "Munafuka, shine kika saka wa yarinya ta sunan surukarki ko?"

Nayi dariya nace "to ai gashi nan kema maybe surukar taki ce" Tace "show Sultan the picture ki ji abinda zai ce, ni kuma zan fara tambaya inji labarin ta, ko a gurin ummeen Zayed ne, daga nan sai mu gane ko ita ce ko ba ita bace ba" na danyi shiru sannan nace "Hafsat bama tare da Sultan yanzu" kamar bata ji sosai ba tace "what?"

Na ce ina jin hawaye yana taruwa a gefen idona "ina gida yanzu" tace "subhanallah Moon wannan wanne irin muguwar magana kike fada min hakan? Sultan din tafiya yayi kika zo gida?" Nan hawaye ya balle min nayi tayi, tana jina bata ce min komai ba, sai da na gama dan kaina sannan na fara bata labarin abinda ya faru gaba daya, na kara da cewa "Hafsat ban san ya zanyi ba, Sultan zafin zuciyarsa yayi masa yawa Hafsat, shi kuma Ibrahim ban san me yake so inyi masa ba, nayi aure kuma ina ruwansa dani?"

Hafsat tace "to ai ni Sultan yayi min dai dai, cin ubansa ya kamata yayi yadda gobe in ya hango ki a guri da gudu zai fita. Yanzu kina nufin akan Ibrahim din kika baro gidan mijinki?" Na girgiza kaina Nace "Hafsat ba'a kan Ibrahim bane ba, akan Sultan ne, akan bakar zuciyarsa, Hafsat kisan kai fa yayi niyyar yi, da Ibrahim ya mutu me kike ganin zai faru da shi? Me kike ganin zai faru dani? Sannan zargin da yayi min shi yafi komai kona min rai, he should have trusted me"

Hafsat tace "tayaya kike tunanin zaiyi trusting dinki bayan ko cikin da kike dashi baki gaya masa ba? Idan da ace yasan da cikin da duk haka ba zata faru ba, idan kakar chocolate kike so zai fita ya sayo miki, in ma ya ganki da Ibrahim din yasan ba purposely kika hadu dashi ba. Idan kika yi la'akari da rayuwar Sultan dole yana da trust issues, he is scared of loosing you, gani yake yi kamar kowa is against him"

MaimoonWhere stories live. Discover now