What You Sow

7.2K 611 0
                                    

A 'yalleman kuwa tunda Munir yayi wa Hajja waya da sassafe ya hada mata karya da gaskiya ya gaya mata. Suna gama wayar ta fita daga part dinta ta tsaya a compound ta rafka wani uban salati "na shiga uku ni Zuwaira yau wanne mugun labari zanji haka" a tare Baffa da Inna suka fito daga part dinsa suna tambayarta "lfy? Me ya faru? Waye ya mutu?" Ita kuwa kuka take tana fyace majina da bakin zanin ta, "dama babu abinda ban fada ba aka ki daukan magana ta saboda bani na haifi Muhammadu ba kuma shine dan gatan gidan nan, dama gata ai mugun abu ne, babu abinda yake haifarwa sai nadama. Wanda duk baiji bari ba ko ai zai ji oh'oh"

Inna tana jin zancen Muhammadu ta ja da baya ta tsaya tana jiran taji alkaba'in da zai biyo baya. Baffa ma bari yayi sai da Hajja ta gama sambatun ta sannan ya kuma tambayarta "me ya faru da Muhammad din" Hajja ta duba taga duk yaran gida sun taru a compound suna sauraren abinda ake yi sannan tace "yaran nan babu yadda banyi ba akan ayi musu aure aka ƙi, aka nuna min ban isa ba, to yanzu gashi nan abinda ake gudu ya faru. Manniru ne yayo min waya dazu hankalinsa a tashe, yace tunda yarinyar nan ta dawo kasar nan ta juya masa baya, in yaje gidan nasu sam ba'a barin shi ya ganta, in ya kira ta a waya bata dauka, to jiya da daddare wajan karfe daya ya fita neman abinci saboda yaje gidan sun hana shi abinci shi kuma yunwa ta dame shi, kawai yaga yarinyar nan a titin Allah tana yawo da dan skirt, ta sha giya tayi mankas ko tafiya bata iyayi sai wadansu maza ne suka rirriketa, shima kansa da kyar ya gane ta, kuma ya kira Walid ya gaya masa, ashe sun riga sun san halin da yarinyar take ciki shi yasa basa barin ya ganta. Daya bisu gidan ya na tada maganar saboda ayi wa tubkar hanci sai Walid da Habibu suka taru suka yi masa dukan tsiya suka ce in dai ya sake ya fada wa mutane sai sun nakasa shi"

Wani irin jiri inna taji yana neman daukan ta, wannan wanne irin sharri ne Munir ya shirya wa Maimunatu? Palourn ta ta koma ta zauna kanta yana bala'in sara mata, yaran gidan kuwa tunda suka gama jin abinda Hajja tace suka fara fita daya bayan daya suna shiga makota kai rahoto, Baffa kasa cewa komai yayi dan shima jirin ne yake dibansa, Ma'aruf dan autan Hajja wanda kuma shi kadai ne ya rage a gidan ne yayi saurin dauko kujera ya zaunar da Baffa. Sai da baffa ya mayar da numfashin sa sannan yace "Hajja kin tabbatar Munir ba karya yayi miki ba?"

Hajja ta matso kusa dashi tace "yaya zaiyiwa yarinyar da yake so karya? Ita fa ya zaba ta zama uwar 'ya'yansa ta yaya zai yi mata sharri kuma? Ban taba ganin so na gaskiya irin wanda yaron nan yake yiwa yarinyar nan ba, duk da abinda ya gani da idanuwansa fa cewa yayi shi so yake yi ma a gaggauta auren ko Allah zai sa auren ya gyara ta" still zuciyar Baffa taki yarda da maganganun Hajja, yana kallon fuskar Maimunatu a zuciyarsa, duk acikin jikokinsa yana son 'ya'yan Muhammadu, kuma duk a 'ya'yan Muhammadu Maimunatu ta daban ce, ga tarbiyya, ga ladabi, ga fara'a, ga shiga ran mutane sannan uwa uba ga son 'yan'uwanta. Sam bata da girman kan wai babanta wani ne, duk sanda tazo sai ta zaga 'yan'uwa kai hatta 'yan aikin gidan nan kawayenta ne dan wani lokacin a cikin su zai ganta tana wasa.

Hajja ta tankwashe kafar ta ta cigaba da zuba zance "ya gayamin ai ba laifin ta bane, wani yaro ta hadu dashi lalatacce shine ya bata ta, su kuma iyayen sun dauki son duniya sun dora mata shi yasa suka kasa raba su, dan ce musu tayi ko yanka ta za suyi ba zata rabu da yaron ba. Ni dai shawara ta shine, ka kira Muhammadu ka gaya masa maza maza ya kawo mana yarinyar nan gurin mu, tana zuwa sai mu sata a lalle ayi auren nan kowa ya huta. Shi kuma wannan yaron da yace yaji ya gani zai aure ta a haka Allah yayi masa albarka"

Baffa da har yanzu kansa bai gama juya masa ba ya aika ma'aruf ya dauko masa wayarsa, amma maimakon ya kira Muhammadu kamar yadda Hajja tace, sai ya kira Aliyu, Aliyu yana dauka ko gaisawa basu yi ba yace "Aliyu kaga abinda ka jawo mana ko? Taurin kanka ne ya hana ayi auren nan da yanzu duk wannan abin bai faru ba, to kasani ni babu ruwana, tunda kai ka jawo sai kasan yadda zakayi ka warware" yana kaiwa nan ya kashe wayar ya mike ya shige dakinsa.

Hajja ba haka taso ba dan tasan Aliyu sam ba zai taba goyon bayan Munir ba, saboda kamar yadda take fada tace ya tsane shi saboda ba uwarsu daya da wanda ya haife shi ba. A bangaren Inna kuwa tana shiga dakinta ta dauko wayarta ta kira Mommy, sai da ta katse ta sake kira sannan Mommy ta dauka, itama ba tare da sun gaisa ba tace "Fatima me ya faru tsakanin Manniru da Maimunatu?"

MaimoonWhere stories live. Discover now