Skeleton in the Closet 2

8.7K 692 4
                                    

Like I always say and always emphasize, things are not always what they seem. Duk abinda kake zargi, karka yanke hukunci a kansa sai kayi bincike ka tabbatar, duk abinda aka gaya maka akan wani indai har ba kaine da kanka ka gani ba, kar kayi saurin yanke hukunci akai, kayi bincike sosai first. Never and never judge a book by it's cover, in ba haka ba you might spend the rest of your life regretting.

How far will you go to protect your family?

Hakan kuwa akayi. Daga nan sarki Abdallah ya saka akaje dakunan da Khairat ta zauna aka kwashe duk kanin kayanta aka rufe dakunan. Gari yana waye wa yasa aka tara masa duk mutanen gidan tun daga kan iyalinsa har bayinsa ya ce ya hane su da ko da ambaton sunan Khairat ne a gidan ballantana labarin ta ko wata magana data shafeta.

A lokacin da Prince Sadiq ya tashi daga bacci jin kansa yayi fresh, babu abinda yake damunsa, kamar bashi da wata matsala a duniya. Ya danganta hakan da bacci mai nauyi daya samu. Yayi wankansa ya shirya ya tafi gurin mahaifinsa, ya tarar dashi yana cin breakfast, ya gaishe shi ya zauna gefe, mahaifin nasa kallonsa kawai yake yana studying dinsa, sannan yace "Sadiq yau baza a fita gurin abokanai ba ne?"

Sadiq ya dan shafa kansa yace "Ranka ya dade yau gida zan zauna, sam yau bana son hayaniya" Sarki Abdallah yaji babu dadi har cikin ransa. Sadiq ne za'a ce masa ya fita gurin abokanai yace shi ba zashi ba? Sadiq din da kullum in yana gari gidan a cike yake da mutane saboda shi? Bayan ya baro mahaifin nasa ne ya tafi cikin gida gurin Yaya, yana shiga palourn ta yaga wani yaro yana ta kuka a hannun Baba Gaji, kallo daya ya yiwa yaron yaji wani irin tsanarsa a ransa, ji yake kamar ya hada daga baba gajin har yaron yayi musu duka ya kore su daga palourn amma ya daure zuciyar sa ya wuce ciki.

Tunda ya shiga Yaya take kallonsa da mamaki har ya durkusa ya gaishe ta, ba zai iya jure kallon yaron ba dan haka ya mike ya fice, ga mamakin sa sai yaga yaron yana yunkurin zuwa gurin sa dan haka ya kara sauri ya fita in ba haka ba zai iya kwada wa yaron mari.

Babu shiri Yaya ta dau mayafinta ta tafi gurin mai martaba, ta tarar har yanzu abinci yake ci ga Nani a kusa dashi, babu kishi a tsakanin Yaya da Nani dan haka a gabanta tayi magana, "Ranka ya dade me akayi wa yaron nan ne?" Ba tare daya kalle ta ba yace "Abinda yafi alkhairi a tare dashi shine abinda nayi masa" hawaye ya fara zuba a idon Yaya tace "Allah ya taimake ka ko dansa fa bai gane ba ya zakace hakan shi yafi alkhairi a rayuwarsa? Wannan ba Sadiq din mu bane ba, wani ne daban ba dan mu bane ba"

Bai ce mata komai ba, Nani ta tambaye ta ta fada mata abinda ya faru, itama Nanin kukan ta fara yi dan duk sun fahimci abinda mijin nasu ya aikata, Nani tace "ayi mana afuwa, amma muna ganin wannan ai ba shine mafita ba, a zaunar da yaron ayi masa nasiha, asaka malamai suyi tayi masa adduoin nutsuwa, babu abinda yafi karfin addu'a, a hankali komai zai warware. Amma yanzu ba Khairat aka raba shi da ita ba, rayuwarsa aka raba shi da ita gabadaya"

Sarki Abdallah ya ajiye chokalin hannunsa ya juyo yana kallonsu, a hankali yace "ku tashi ku bani guri" babu musu suka tashi suka bar gurin, ya jingina kansa a jikin kujerar dake bayansa, har yanzu ya kasa tantance cewa abinda yayi dai dai ne ko ba dai dai bane ba, odds din sunyi yawa, Sadiq yana da taurin kai kuma tunda yace sai yaje to sai yaje din ko me za'ayi masa, yes addua tana maganin komai amma tana taking time, Sadiq ba zai jira ba. Yanzu addu'ar da zaiyi shine Allah ya karya abin wata rana, bayan komai ya lafa, yadda ko Sadiq yaje Riyadh maganar ta riga ta wuce.

A ranar da yamma ya aika aka kira Sadiq, ya mika masa takardu guda uku yace "wata takarda nake so ka rubuta min, kayi copy uku, daya da larabci, daya da turanci daya da hausa" ba musu sadiq ya dauki takardar da biro ya fara rubuta abinda mahaifin nasa yake fada masa kamar haka

"Bismillahir rahmanir rahim. Assalamu Alaikum wa rahmatullah. Ni Sadiq Abdallah, na saki matata Khairat Faysal Abdallah saki daya, idan ta samu miji tayi aure. Bissalam"

MaimoonWhere stories live. Discover now