The First Night

12.6K 701 6
                                    

Hmmm let's talk about something kafin mu ziyarci lovers din can. Abinda nake so inyi magana akai shine auren dole. Dan Allah iyaye mu kula mu rage yiwa 'ya'yanmu auren dole. Ni 100% ina goyon bayan auren soyayya gaskiya. Saboda soyayya ita take kawo sacrifice, forgiveness, juriya da kuma jajircewa a cikin relationship. Idan da akwai soyayya babu abinda mutum ba zai iya yiwa partner din shi ba.

Na danyi shiru ina kallonsa ina lissafin anya kuwa ina da sauran abinci a gidan nan? Dan duk warmers din abincin an mayar dasu cikin gida. Dabara ce ta fado min a raina, na dan bata rai nace "aren't you forgetting something?" Yace "No" nace "kara tunawa dai" ya danyi shiru har yana sosa kansa alamar tunani sannan ya sake cewa "ni babu abinda na manta" na marairaice fuska nace "Kaza" ya maimaita "kaza?" Nace "yes now, ba ango yana shigowa da kaza ya kawowa amarya ba?" shima ya marairaice yace "please don't tell me yanzu sai na fita siyan kaza" nace "sosai ma" ya harde kafafuwansa yana kallona ni kuma na dan bata rai ina kada kafa irin lallai sai anyi min abinda nake so, dariya naji ya dan yi sannan yace "just tell me babu abinci a gidan inje in siyo, ba sai kin wayance da zancen kaza ba, I know you can't cook, but what you are forgetting is that, I can"

Ya mike tsaye ya miko min hannunsa yace "zo muje muyi girkin tare" babu musu na kama hannun na mike muka tafi kitchen, muna zuwa ya daukeni chalak ya dora akan worktop din kitchen din yace "sit here and watch" sai kuma ya tsaya yana tunani, ya bude fridge ya juyo yana kallona yace "kaza kika ce kina so ko? To kin samu, kazar amarcinki bata siyarwa bace ba, ni zan gasa miki da kaina" ni dai kallonsa kawai nake yi naga ya fito da kaji manya guda biyu a cikin wadanda aka zuba dazu, ya wanke su yazo ya hada spices sannan ya shafe su dashi, ya ajiye su a gefe, ya dawo ya dauko attaruhu da tumatir da albasa ya wanke ya miko min yace "yanka min wadannan kanana kanana" nace "with pleasure" na dauka na fara yayyankawa. Ya kunna gas ya dora ruwa kadan, ya zuba mai, yana tafasa ya zuba taliya. Sannan ya dauko kajin ya sakasu a griller ya kunna yayi setting time.

Har lokacin yankan attaruhu nake yi, ya tsaya yana kallona, nayi sauri na karasa na mika masa. Nan da nan ya hada sauce, yayi draining taliyar, ni kam ina zaune ina ta zuba masa surutu, ina bashi labarin bakin da suka yi ta zuwa yau. Kafin ya gama tuni kajin sun fara kamshi, na sauko ina leka cikin griller din yace da sauri "karki taba, zaki kone" a raina nace 'ko baka fada bama ba tabawa zanyi ba' danni babban dalilin da yasa bana son girki shine tsoron kar in kone.

Kayan da ya bata na hada na wanke na mayar dasu inda suke, sannan na hada abincin daya gama na kai dining room, shi kuma ya biyo bayana da drinks, tare muka shirya dining din sannan yace "zo mu zagaya gidan kafin kajin su karasa" tun daga babban palour muka fara wanda yake hade da dining room shi kuma dining room din ta nan ake shiga kitchen, muka shiga part dina wanda yake da dan karamin personal palour na sannan ka shiga corridor inda bedrooms dina guda biyu suke, a cikin palourn kuma akwai kofar da zata shiga da kai inda swimming pool yake da kuma gym, inda anan ne aka shirya partyn jiya amma an bude kofar da za'a iya shiga daga waje, daga nan kuma akwai kofar da zata shiga zuwa part din Sultan. Sannan muka shiga part din baƙi mata wanda yake dauke da bedrooms biyu kowanne da toilet, daga nan muka shiga nasa wanda yake exactly irin nawa sai dai shi yana da extra palour wanda yake da kofa daga waje inda yake kira "great room" anan zai ke saukar baƙin sa da ba zai kai cikin gida ba, ta nan muka bi muka fita waje muka zagaya part din baƙi maza wanda yake daga waje yana kallon kofar great room din Sultan, daga nan muka zagaya zuwa daya side din gidan inda boy's quarters suke, guda biyu ne, na mata dana maza, amma babu kowa a ciki tunda bamu dauki 'yan aiki ba tukunna. Muka koma gidan ta cikin kitchen.

Muna zuwa muka tarar kajin mu sun karasa, ya saka hand gloves ya bude griller ya dauko su ya yayyanka kanana akan plate, sannan ya miko min yace "ga kazar ki nan, amarya" ina dariya na karba nace "thank you ango, it looks delicious".

Tare muka ci abincin, tare kuma muka ci kazar, ina ta zuba santi yana yi min dariya, sanda na tashi daga kan kujerar ji nayi cikina yayi min nauyi saboda koshin da nayi, shi kam sai dariyar mugunta yake yi min. Ji nayi ya daina dariyar ya zagayo ta gaba na yana kallona "ko ba zaki iya tafiya ba sai na dauke ki ne?"

MaimoonWhere stories live. Discover now