The Message

6.3K 599 2
                                    

Kowa a palon yayi shiru, hatta ni da nake kuka nayi shiru ina assessing me Daddy yace. It then dawn on me suddenly cewa yana nufin bazan je Nigeria ba. Ai kuwa da gudu na mike na nufi kofar dakinsa ina kuka ina cewa da filatanci "Daddy dan girman Allah kayi hakuri, Daddy na tuba please" amma ko motsin sa banji ba, nan na durkushe a gurin ina faman gumurzun kuka.

Hafsat ce tazo ta kamani ta mayar dani falo. Na zauna a kasa na kifa kaina a cinyoyina ina cigaba da kuka. Hafsat tace "Mommy please do something" Mommy wacce itama daga dukkan alamu hukuncin na Daddy ya bata mamaki, tayi ajjiyar zuciya tace "yayi fushi sosai, and she deserves to be punished" ya Walid yayi sauri yace "amma Mommy kunsan fa yarinyar nan ba lafiya ce ta ishe taba, ta yaya za'ace mu tafi mu thousands of miles away? Ni dai Mommy idan Daddy yaki yarda a tafi da ita zan zauna anan nima, kice masa ina harkar wani project and I need to stay in town"

Mommy ta harare shi tace "kana tunanin he will buy that, duk harkar karatunku babu abinda bai sani ba, yasan cewa babu wani project da kake yi"

Ya Habeeb yace "at least Mommy try something, ba za a bar maganar nan kawai ace shikenan ba" ni dai duk ina jinsu bance komai ba, kuma ban daina kuka ba.

Mommy ta mike tace "ina zuwa" sai da naji Mommy ta shiga dakin Daddy sannan na dago kaina ina goge hawayena. Tun muna yara nasan sau da yawa mu na cewa Mommy tana da magic, duk sanda ka tambayi Daddy wani abu yace no, to in ka samu ka lallaba Mommy tace yes, daga ta shiga dakin Daddy ta fito shikenan sai kaji shima yace yes din. A lokacin yarinta sai muke cewa magic ne take yi masa irin abracadabra din nan shikenan ta chanja mind dinsa, but now we know better.

Mun jima a zaune ba wanda yake yin magana, ni dai in banda sunayen Allah babu abinda nake kira "please God intervene, bana jin zuciya ta zata iya daukan wannan hukuncin" it had already been a year rabo na da Nigeria, da Ibrahim, I just wanted to know if he is ok.

Bude kofar Mommy ne ya dawo dani daga tunani na. Fuskarta kawai na kalla nasan cewa wannan magic din baiyi nasara ba. Tana zama na rarrafa gurinta na dora kaina a chinyar ta na cigaba da rusa kuka na. Bata rarrashe ni ba ta fara magana. "Moon, you will be left behind. Zaki zauna kiyi karatu for two months, zai shiga makaranta ya karbo miki textbooks na courses din da kuka yi last session wadanda zaki karanta. Kowanne textbook in kin gama karantawa zaki rubuta formal report akansa in mun dawo zaki wa Daddyn ki submitting shi kuma zai kai department din ku with hope zasu kara miki grades dinki. Za'a bar securities, you are not to leave this building har sai mun dawo, za'a bar miki David, chief bodyguard din Daddy, duk abinda kike so a cikin gari ki gaya masa zai siyo miki. Cooks da sauran servants duk zasu zauna suna kula da ke da gida. Za'a dauko miki nurse din da zata ke zuwa tana kwana dake, kuma zata ke gwada bp dinki daily"

Ta juya wajan ya Walid tace "bai yarda da zaman ka ba anan. Saboda bai yarda ya barku daga kai sai Moon ba. Nima kuma ban yarda ba" tana gama fadin haka ta mike ta shige daki. Knowing Mommy, nasan kuka zata je tayi.

Haka abin ya kasance, textbooks kwali biyu daddy ya lode min wai duk ni zan karanta kuma cikin wata biyu. Ina kallon su suna ta shirye shiryen tafiya banda ni. Da assuba jirgin su zai tashi dan haka tun cikin dare su ka tashi suna ta wanka da shiryawa. Inajin Hafsat ta na shiryawa nayi banza da ita nayi kamar bacci nake yi. Ta zo ta tsaya a gaban gadon da nake tace, "Moon I am going" na kalle ta kawai bance mata komai ba. Ta sha bakaken kaya da wani bakin glass a fuskar ta, sai naga fatar ta kamar ta kara haske kuma tayi kama da irin bodyguards din nan marasa dariya. Nasan ta saka glass din ne dan kar inga kukan ta, she is too proud to let me see her tears.

Tunda aka haife ni muke tare da Hafsat, bana jin mun taba sati daya ba tare ba. Yanzu gashi zamuyi two months ba tare ba. Tace "zan yi iyakacin kokarina inga na samo miki news" na gane maganar da take yi, a hankali nace "thank you" daga haka ta juya ta fita tare da rufe kofa. Ina nan dai a kwance naji anyi knocking kofar sannan aka bude a hankali. Kamshin turaren Daddy naji nayi sauri na rufe idona. Ya jima a tsaye yana kallona sannan naji ya hawo gadon yayi kissing dina a goshi sai kuma naji ya sauka ya rufe kofa. Hawaye naji yana zuba daga idona masu zafi. Next ya Habeeb ne yazo da dariyar sa yana ta tsokana ta wai Daddy so yake na zama professor kafin su dawo. Sai da ya fahimci cewa am not in the mood for wasa sannan ya rabu dani sai ga Mommy nan ta shigo itama, complete ta gama shiryawa dan harda handbag dinta a hannunta. Ina ganin ta naje na rungume ta ina cewa "Mommy dan Allah kice Daddy ya bar ki su su tafi" ta girgiza kanta tace "kema kinsan hakan ba zai yiwu ba, kiyi abinda yace miki shine mafi alkhairi a gareki, kinsan dan yana sonki yayi hakan ba wai dan yana ƙin ki ba, in mun barki ƙinƙiyin karatu ai ba mu yi miki gata ba. Kuma yace in dai har ba kici 70% a reports din da zaki rubuta ba to next holiday ma ba zaki je ba. Take care of yourself, do as you are instructed and you will be fine" daga nan tayi min kiss a both cheeks dina ta fita. Na durkushe a gurin zuciyata tana yimin zafi, ina jin tashin motar su amma na kasa lekawa har suka tafi.

MaimoonWhere stories live. Discover now