His mother's Son

11K 687 3
                                    

Bedroom din Ummee na shiga na turo kofa, na zauna a bakin gado ina ta murmushi ni kadai like an idiot, reaction din Sultan ya bani mamaki kuma ya kara tabbatar min da cewa there is no one like mother. Na san dama zai sauko amma banyi tsammanin saukowar shi da sauri haka ba. Wai kunyar ta yake ji, Sultan ne wai da kunya, abin ma abin dariya.

Na gaji da zama na jawo pillow na kashingida ina jin farin ciki sosai a raina, burina ya kusa cika, nayi wa kaina alkawarin I will totally change Sultan's life around kuma so far babu abinda zance sai Alhamdulillah saboda wannan duk ba yi na bane yin Allah ne.

Ina nan kwance har akayi sallar azahar na tashi naje nayi sallah, ina idarwa na koma nayi kwanciya ta, na dauki waya na kira Hafsat tace min sun fita da Zayed da little Khairat, ina nan a kwance sai ga Ummee ta shigo, ta tsaya a bakin kofa tana kallona sannan tace "waye zaiyi serving mijinki abinci da kika zo kika kwanta?"

Na dan tashi ina dariya, ta daga gira tace "he has been asking for you, yaki cin abincin ma, wai shi kunya ta yake ji" na tashi na gyara veil dina muka fita tare. A dining na same shi ya tisa abinci a gaba ya zuba uban tagumi, na dan yi gyaran murya, ya juyo da sauri, ina kallonsa har da ajjiyar zuciya ya taso ya taho, na fara waige waigen Ummee amma naga bata gurin, na karasa nima gurinsa na shige cikin kirjinsa ya rufe ni da hannayensa, a tare muka sauke ajjiyar zuciya, sosai nayi missing mijina, na lumshe idona ina shakar kamshinsa da yake kwantar min da hankali a koda yaushe, nace "I missed you, mijina" ya danyi dariya yace "ba zan yi magana ba ni, a aikace zaki ga kalmar missing din" na dan ture shi nace "nan dai gidan Ummee ne ba gidan mu ba, dan haka mind your steps"

Na fara tafiya dining ya biyo ni, yace "ai itama tasan ba zata hanani matata ba, in kuwa ta gwada to akwai rigima" na jawo masa kujera ya zauna, na sunkuya dai dai fuskarsa nace "albishirinka?" Yace "goro" nace "a dakin Ummee nake kwana a kan gadonta tare da ita" ya yamutsa fuska yace "da kenan, lokacin bana nan, yanzu nazo dole a bani matata" nace "to idan tazo sai ka gaya mata" yace "kunyarta nake ji. Shine dazu kika gudu kika barni tare da ita ko?"

Na fara bude masa dishes din gurin nace ya zabi wanne zanyi serving dinsa first, amma ga mamaki na sai naga sam bai wani rude akan abincin ba kamar yadda nayi tunani, ni kawai yake kallo, nace "food always come first, hausawa suna cewa ci shi yake gaba da sallah ma" ya daga gira yace "not to me"

Sallamar Ummee mukaji, ina kallon Sultan ya wani sunkuyar da kansa kasa, kamar zanyi dariya na maze na fara zuba masa abinci, ummee ta karaso ta zauna tana kallonsa yadda yake juya cokali a cikin abincin, ta kalleni tace "in bashi yake so ba ki zuba masa wani mana" ya dago kai yana kallona yace 'it is OK, am just tired ne, shi yasa" tace "try to eat something then, sai kaje kayi wanka ka kwanta ka huta"

Yana kallona nayi sauri na dauke kaina na tafi na fara serving Ummee, nima na zuba abinci na na fara ci, Ummee gaba daya hankalinta a kansa yake, nima ina kallonsa ta gefen idona, a hankali ya fara cin abincin kuma, sai kuma ya fara ci da dan sauri, muka hada ido da Ummee mukayi murmushi.

Yace "this food is really good" nace "Ummee ce ta yi shi, for you, ita ta girka all this food, for you" yana shafa kai ya dan kalleta yace "thank you" tace "bani kadai nayi ba ai, tare da Maimunatu mukayi" ai kuwa Sultan ya zage yaci abincin sosai, kusan komai sai da na zuba masa yaci, yana ci kuma yana santi, bakinsa ya fara budewa kuma, Ummee sai tsokanar sa take yi yana zuba mata zance, kunyar ta fara tafiya.

Muna gamawa Ummee tace "an kai maka kayanka dakinka, Maimunatu sai ki raka shi yayi wanka ya huta ko?" Na dan bata rai irin ni bana so din nan, ya mike ya fara tafiya, har yakai bakin kofa ya juyo yana kallona yace, "ban san gurin ba fa, sai anzo an nuna min" Ummee ta harare ni tayi min alamar go da hannunta, ni dai duk kunya ta ishe ni, na bishi a baya.

Muna fita nayi gaba, nasan gurin dama ummee ta nuna min sanda ta zagaya dani gidan, katon palo ne da two bedrooms, komai na gurin red and cream ne, hatta electronics din gurin. Muna shiga ya rufo kofa yana kallona, nace "welcome to gidan ka da baka san dashi ba" kallo daya yayi wa dakin yace "wato da ba zaki zo ba ko?"

MaimoonWhere stories live. Discover now