Amir

7K 669 3
                                    

Na jima ina shafa fuskata dan da gaske marin ya shige ni but I deserved it. I deserved everything that has happened to me. Bawai na gaya wa Hafsat abinda ya faru bane dan tayi min fada ko wani abu ba, na gaya mata ne saboda ta bani shawara akan abinda ya kamata inyi yanzu sannan kuma ina da tabbacin cewa ba zata tona min asiri ba. Hausawa sunce mai neman shawara sirrin sa baya rufuwa amma kuma aikinsa baya baci. Na jima anan a zaune ina ta lissafe lissafe a raina, ina juya zoben Sultan a hannuna. I desperately wanted to know how he was, amma kuma bazan iya kiransa ba. Nasan kuma shima yana son yaji daga gareni, amma ba zai iya kirana ba. I just wanted someone to act as intermediary. Har nayi shirin kwanciya na kwanta babu Hafsat babu labarinta. A raina nace tayi fushi dani.

Da safe na tashi na yi wanka na shirya sannan na fita, a kitchen na same ta ita da maid dinta suna hada breakfast, ko kallon inda nake bata yi ba har suka gama aikin ina zaune ina kallonsu, suka shirya dining sannan ta tafi yin wanka. Naje na zauna nayi serving kaina ina cikin ci sai ga Zayed nan, daga yadda yake yi min magana na fahimci cewa Hafsat bata gaya masa maganar da mukayi ba, wannan yana daga cikin dalilan da yasa na iya gaya mata, baza ta gaya wa kowa ba. Muna breakfast muna hira sai gata ta fito kamar amarya, tun kafin ta karaso Zayed ya mike ya taro ta suka fara zuba soyayya ni dai ina ta kallonsu. Ko wata rana ni ma zan samu wannan farin cikin?

Da sauri sauri ya gama ya shirya ya fita asibiti. Nan muka zauna awkwardly ni da Hafsat, maid dinta tana cleaning table din. Can dai tace "yanzu how do I even know you are intact?" Na harare ta nace "ko in bude miki ki gani?" tayi ajjiyar zuciya tace "yanzu me kike so daga gareni" nace "so nake ki bani shawarar abinda ya kamata inyi" ta bude baki da mamaki tace "yanzu ke har sai na baki shawara? Kina nufin kice min da akwai sauran alaka a tsakanin ku? After what he did to you?"

Na sunkuyar da kaina a hankali nace "I love him" tace "you are crazy" a raina nace "maybe I am" can ta sake cewa "yanzu in na baki shawarar ki rabu dashi, zaki rabu dashi?" Na girgiza kaina ba tare da na kalleta ba. A fusace tace "then what do you want from me?" Na dan jawo kujera ta kusa da ita nace "so nake ki bani shawara, me kike ganin ya dace inyi?" Tace "bayan rabuwa da shi? Banga wani abu da zaki yi ba kuma" na girgiza kaina da sauri "rabuwar mu is not the solution Hafsat. In na rabu dashi ban san wanne hali zai shiga ba. He is a really good guy, he is not what people think he is. I don't want abinda ya faru tsakanin mu yayi affecting dinsa negatively. Please Hafsat, so nake ki gaya min hanyar da zam bi mu daidaita ba tare da abinda ya faru tsakanin mu yayi affecting relationship din mu ba. Ina so kiyi acting as intermediary in baki number din sa ki kira shi........." ina magana kamar zanyi mata kuka amma banga alamar tausayi sam a fuskar ta ba, sai ma tsabagen mamaki na da take yi, cikin mamakin ta katseni tace "You want me to call him? In kira shi ince masa me for God's sake? Thank you for trying to rape my sister kike so ince masa ko me?" Na dakatar da ita da sauri nace "He did not try to rape me, what happened wasn't entirely his fault, ni ma da laifi na a ciki" kafin in karasa ta mike da sauri kamar wadda ta manta wani abu, taje bakin kofar palour ta bude kofa ta juyo tana kallo na cike da tsantsar takaici tace "get out of my house" banyi mata musu ba na koma bedroom dinta na jayo akwatina wanda dama ko bude shi banyi ba kayan ta nake sakawa, nazo na fice daga ni har ita babu wanda ya kalli wani. Ina fita na tari taxi nace ya kaini Nigerian embassy.

Ina zuwa gida zan iya cewa kusan na manta da komai saboda farin cikin ganin family na. Sai wani ji dani suke yi kamar zasu goya ni. Kwana na biyu na warware sosai ina ta harkoki na amma ta ciki na ciki dan dai dai da second daya ban manta da Sultan ba. I terrible missed him. Kullum zan budo number dinsa a waya ta inyi ta kallonta amma ba zan iya kira ba. Duk sanda kuwa naji kira ya shigo waya ta sai naji gabana ya fadi ina tunanin ko shine amma shiru makatau. Last seen dinsa a Whatsaap shine a day to barowa ta America.

One week ya wuce, two weeks ma haka. Ni kadai nasan yadda nake ji a zuciya ta tunda babu wanda zan gaya wa in ji dadi, ita wacce na gaya wan ta dauki abin da zafin da haushi na take ji sosai. Har aka yi mana fixing ranar defence na project din mu. Meaning mun gama karatu kenan. Na zama busy sosai ina tsara yadda zan presenting project dina, neurology zan fara sannan a week later in yi psychology. Duk sanda tunanin Sultan ya dame ni sai in dauko waya ta inyi ta kallon pictures din mu, wani inyi hawaye wani dariya. Ko na dauko waya ta zan kira shi sai in tuna abinda ya faru sai in kashe, kunyarsa nake ji sosai, ima so in ganshi amma kuma bana jin zan iya haɗa ido da shi.

MaimoonWhere stories live. Discover now