BABI NA D'AYA

409 12 0
                                    

BAYA DA K'URA....
 

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

1
Y'an mata ne su biyu masu kama da juna saidai kalar fatar jikinsu data bambanta kuma d'aya tafi d'aya k'iba ma'ana dai itace babba.

Dambe suke yi wanda ya zamar musu tamkar d'abi'a idan basu yi ba basa jin dad'i.

Saurayi ne zaune a gefen kan dining table ya haye can sama yana kallon su, baze iya raba su ba sai dai kallon.

"Gaddafi!" Aka k'walla masa kira,dasauri ya juya yana kallon mai kiran nasa,"wane iri ne kai?,kana kallon k'annenka suna dambe bazaka raba su ba".

"Daddy basa jin magana ko na raba su baza su daina ba".

"Azzah", ya kira sunan k'aramar ta juyo tana kallonsa sai hak'i take.

"Kinsan ko kwanakin baya na hanaki dambe da yayarki ko?,oya zo ki wuce ki had'o takardunki gobe nake so na kammala komai jibi zan koma Dubai".

Tana tunzura baki ta bi gefensa ta wuce.

"Nuwaila na haneki da biye mata kuna dambe,k'anwarki ce zata rainaki kuna kai zuciya nesa".

Batayi magana ba ta bi gefensa itama ta shige d'akinsu.

"Dan kinji dady yamin fad'a bashi zai hana in kin dake ni in rama ba". Azzah ta fad'a tana rufe wardrobe din dakinsu.

"Ni kuma wallahi bazan daina bige bakin nan mai shegen surutun tsiya ba, na hanaki afkawa d'akin dady duk yadda kika ga dama idan yana nan amma bakya ji mummuna kawai".

"Hmm idan kin cika ki bari jibi ya wuce ki ga abinda zan miki".

Toilet kawai nuwaila ta shige dan yin alwala ta k'yale fitsararriyar k'anwarta tana mata rashin kunya.

B'angaren Dady ma kallon Gaddafi yayi yace,"watarana zasu illata kansu a gabanka bazaka hana ba big for nothing(babban banza)",komawa yayi d'akinsa inda ya baro mahaifiyar su a kwance.

Murmushi ya sakar mata sannan ya tada ita zaune,"sweetheart zaki fara cin abinci ne kisha magani kiyi sallah ko a fara yin wanka?".

Rufe idonta tayi ta kuma budewa a lokaci d'aya alamar Eh, hannunta ya rik'o yace,"a fara da wankan kenan?",da ido ta kuma bashi amsa, d'agata yayi sai toilet ya zaunar da ita kan kujerar roba daya ajiye a toilet din nasa saboda ita kawai,ruwan wanka ya tara mai d'umi ya shiga cire kayan jikinta yana mata hira,"wannan rigar ta miki kyau idan zan dawo wani lokacin zan siyo miki kala-kala ki ringa yimin kwalliya da su".

Ita dai sai kallonsa take saboda batada bakin magana,bayan ya gama cire mata kaya ya cire nashi yayi wanka sannan ya mata ya d'auraye jikinsa ya d'aukota kamar yadda yayi da farko.

Turo ta yayi kan kujerarta ya mata masauki a dining,kulolin ya shiga bud'ewa nan yaga farar shinkafa da miya kawai,"Dije!",ya kira matar dake kula da abincin gidan dama matarsa idan baya nan.

Kafafuwanta da k'asan zaninta ya jike da ruwa da alama wanki take yi yace,"me yasa aka dafa shinkafa haka babu wani abu da za'a had'a dashi".

Shiru tayi na d'an lokaci sannan ta bashi amsa,"aiki ne yamin yawa yau sannan tun safe Azzah da nuwaila ke fad'a a gidannan nace su yanka kabeji da carrot ko in tsigo zogale su dafa amma babu wanda yamin kallon arziki a cikin su sannan kuma wankinsu na tsaya nakeso a gama yau dan inaso na musu kit...".

"Yi hak'uri Dije"ya katse ta,"ba cewa nayi ki lissafomin ayyukan da kikeyi gidannan ba nadai ji dalilin da yasa aka dafa shinkafa kawai zaki iya tafiya".

Bata k'ara magana ba ta juya ya bita da kallo har ta fita yayi tsaki,"mtsw zaki iya ci ne ko naje in siyo miki wani abin mai dad'i".

Yadda ta saba bashi amsa da ido haka tayi masa ko yanzu,abincin ya zuba a plate ya fara bata shima yana ci har su Nuwaila suka fito cikin kaya daban daban.

Kallonsu Azzah tayi ta koma kusa da Nuwaila tana mata magana a kunne,"dagaske naga Dady d'azu yayiwa momy kiss a baki nace miki yana sonta sosai wallahi kalli yadda yake bata abinci a baki".

"Wallahi yau sai na fasa bakin ki insha Allah kuma sai na fad'awa Gaddafi abinda kike yi kuma kinsan babu kyau".

"Nuwaila mai kuke wa k'us-k'us ne haka",Dady ya tambayesu yana murmushi.

Murmushi Suma sukayi suna kallon juna sannan suka k'arasa kusada momynsu suna gaisheta.

Kallonsu kawai take tana murmushi da gefen baki.

Abincin suka zauna suna ci har Gaddafi ya fito shima ya zauna anan yake fad'awa Dady.

"Ni nake da duty yau da dare sannan akwai aiki da zanyiwa wata yau da dare yakamata a nemo mai gadi kafin ilu ya dawo".

"Ko kana nan mai zaka iyayi idan ma wani abu zai faru k'annenka suna dambe ma ka kasa raba su balle wani kula da gida,ai inaga daga can gefen zan fara maka gini".

Azzah ta saki dariya mai d'an k'arfi tace,"Dady ya Gaddafi matsoraci ne Allah".

Zuciyar Gaddafi tazo wuya amma shi ba gwani bane wurin hayaniya hakan yasa bai k'oshi ba ya ajiye abincin ya tashi,kallon momy Azzah tayi taga irin kallon da take mata idan tayi laifi ne mik'ewa tayi da gudu tabi bayan Gaddafi ta rik'o hannunsa.

"Yaya kayi hak'uri wasan yaya da k'anwa nake maka fa,kazo Kaci abincin ka momy bazataji dad'i ba idan ka zauna da yunwa".

Bai yi magana ba ya juyo tana rik'e da hannunsa suka zauna,abincin kowa ya cinye nashi Dije ta shigo a lokacin Dady ya musu sallama zai fita.

Kallon da momy ke ma Dije yasa tayi murmushi ta rik'o hannunta,"hajiya karki damu naci nawa a kitchen tun dazu",lumshe ido kawai tayi tana murmushi alamar taji dad'in hakan.

Kwanukan Dije ta shiga had'awa Azzah da Nuwaila suka taya ta,momyn su takanyi fushi dasu idan Dije na aiki basa taya ta dan haka idan a gabanta ne har jikinsu ke rawa su sa hannu a aikin dan kar ranta ya b'aci.

Da dare suna zaune a Palo Dady ya kwantar da momy kan kujera yayi mata matashin kai da cinyoyinsa suna kallo ya kalli Azzah,"ki shirya fara zuwa makaranta nan da wata d'aya karki yi wasa dan kinga bana nan this week(wannan satin) admission ze fito"

"Dady to wa zai ringa kaini?",ta tambayeshi.

"Ke zaki ringa kai kanki shine amfanin koya miki mota","uhm to Dady baka siyamin mota ba ai".

"Kinada hayaniya Azzah,tunda nace ke  zaki kai kanki ki dawo da kanki ai kinsan dole a baki mota ko?,da motar momynku zaki ringa zuwa tunda ba fita ake da ita ba".

Dan murna sai da tayiwa Nuwaila peck a kumatu,"Dady na gode Allah ya k'ara bud'i".

Sai da ya kalli fuskar momy yaga tana murmushi alamar abin ya mata dad'i itama sannan ya amsa da"Ameen d'iyar Dady,amma fa ki sani jami'a ba wurin dambe bane karkije kina zubar da mutuncin ki,Azzah rawar kanki tayi yawa idan naji kink'i karatu wallahi cireki zanyi na miki aure ba ruwana da shekarunki".

Fuskar tausayi tayi kamar zata yi kuka kafin tayi magana Gaddafi ya fito zashi wurin aiki kallon agogo Dady yayi yace.

"Karfe tara zaka tafi?".
Murmushi yayi yana sosa k'eya sannan ya lalibo abin cewa,"matar abokina ce babu lafiya zan duba ta suna jirana yanzu ya kirani a waya".

"To Allah ya bata lafiya",Dady ya amsa.

Daga haka Nuwaila da Azzah suka yiwa Dady saida safe suka shige shima d'aukar momy yayi suka shiga d'aki.

BAYA DA K'URAKde žijí příběhy. Začni objevovat