MUGUN ZALUNCI 1-2

1.3K 49 3
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI*😡

📝  *Ummu Asma'u (Sa'adatu*)

*Nah sadaukarwa da wanan littafin mai suna MUGUN ZALUNCI, ga duk matan da ke fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauki*

*Wanan labari k'irkiraren labari ne banyi don wani ko wata ba*

*Dukkan godiya ta tabbata ga Allah( SAW)*

*Bismillahirahamanirrahim*

Page 1⚜2

*1st July 2019*

*GOMBE STATE, DUKKU L/G*

Kallon ta yayi yana Murmushi cikin sigar lalashi, yace  haba Ruk'ayyatu, Rukayyan Baffa kiyi hankuri, wanan shine zuwan ki na karshe, daga shi kin k'are karatun, Ruk'ayyatu kuwa sai hawaye ke zuba a fuskar ta.

Baffa ya rik'o hannun ta cikin  yaren fulatanci ya ciga da lalashi ta, Inna Mahaifiyar su Ruk'ayyatu na gefe duk takaici ya cika ta, don bata ga abun lalashin Ruk'ayyatu da yake yi ba, ko Maimuna gatan k'aunar Ruk'ayyatun ce ta shirya tsaf don komawa makaranta ba alamun damuwa tare da ita.

Tsukin da ina tayi ne yasa Baffa kallon ta, cikin takaici tace Malan ko zaka kai Maimuna makaranta lokaci na tafiya, in yaso ita Ruk'ayyatun da baya ka kaita.

Baffa murmushi yayi yace zamu wuce, Allah ya huci zuciyar ki, ya kalli Ruk'ayyatu yace ku wuce muje mai mota na jiran mu, Ruk'ayyatu wasu hawaye ne suka k'ara zubo mata, Maimuna har tayiwa Inna sallama ta fita waje, Inna harara Ruk'ayyatu tayi ta wuce daki abun ta.

Baffa ne yaja hannun Ruk'ayyatu suka fito inda mai motar da Baffa ya samo zai kaisu makaranta, Baffa ne ya shiga gaba suka zauna bayan motar, driven yaja motar suka wuce.

*Koriya model girls secondary school* aka rubuta jikin symbol din dake kusa ga gate din makarantar, har cikin gate din driven motar ya wuce dasu, yan makaranta sai dawowa suke yi, kasancewar ranar lahadi, littini zaa fara karatun zagon karatu na ukku.

Har baki hostel driven ya kai su, ya fitar masu da duka kayan su, har lokacin Ruk'ayyatu bata da walwalah,  Baffa sai aikin lalashin ta yake yi, driven motar kallon su yakeyi yana mamakin yanda ita Maimuna k'arama ko a jikin ta, har ta fara daukar kaya tana kai cikin hostel din.

Bayan su Baffa sun wuce Ruk'ayyatu ta dauki ragowar kayan ta wuce hostel, a dakin su har Maimuna ta fara gyara masu coner su, Nafisa ce k'awar Ruk'ayyatu ta shigo dakin cikin ihu tana kiran Ruk'ayyatu, tana dakin su aka fa'da mata Ruk'ayyatu sun dawo.

Nafisa ganin yanda fuskar Ruk'ayyatu tayi allamar
tayi kuka, dariya tasa mata, tace wanan fa shine term din mu na karshe duka ko wata ba zamuyi ba mu fara *SSCE* haba 'diyar Baffa, Ruk'ayyatu murmushi tayi ta kauda kai, jin anfara kiran sallah ta dauko hijjab dinta tacewa Maimuna zasuje masallaci taci gaba da gyara kayan don tasan Maimuna period take yi.

Masallaci suka wuce har Nafisa, suna tafiya suna tafa fira ka'dan-ka'dan har lokacin Ruk'ayyatu bata da walwalah, har ga Allah Ruk'ayyatu bata son karatun, tun tana js1 duk zata je makaranta sai anyi yak'i.

Baffa yaso fitar da ita, Inna Mahaifiyar tace dole tayi karatun, bata da zafi shine dole take zuwa, ba kamar Maimuna ba, sosai take son karatun, duk akayi jarabbawa in batayi k'okari take zuwa na ukku.

Ruk'ayyatu bisa sa'a take yin promotion zuwa wani aji, sai bayan sallar isha'e suka dawo, don Ruk'ayyatu akwai ibadah, duk ta k'are sallar magarib zatayi karatun Qur'ani har zuwa isha'e.

Bayan sun koma, duk Maimuna ta gyara masu kayan su har tayi wanka, Ruk'ayyatu kan gado ta kwanta tace kanta ke ciwo, Nafisa murmushi tayi tace zanje dakin mu sai na fito gobe da safe, Maimuna abincin da suka zo dashi ta diba ta fara ci don tasan Ruk'ayyatu bazata ci komai ranar da suka dawo makaranta.

A daren ranar Ruk'ayyatu batayi baccin kirkir ba, kiran farko a kunnen ta, kusan a tadda sallah ta wuce masallaci, bayan an k'are sallah suka shirya zuwa cikin makaranta a hanya suka hadu da Nafisa, ba laifi Ruk'ayyatu ta dan saki ranta.

Share-share makaranta aka saka yara, yan SS3 su Ruk'ayyatu principal ta tara su, tayi masu bayanin kwanaki ka'dan suka rage su fara rubuta jarabbawar su ta karshe, wanda daga shi sun k'are makaranta, Ruk'ayyatu murna baa magana, zata k'are karatun ta huta.

Ranar Ruk'ayyatu cikin murna ta koma hostel Maimuna sai dariya take yi mata.

Bayan wata daya akayi visting, Baffa yaje kamar yanda ya saba duk visting, yayi masu siyayya dai karfin sa, Inna ta dafa masu abinci, Ruk'ayyatu murna baa magana cikin tsale ta rik'e Baffa, Baffa yaji da'di ganin Ruk'ayyatu bata rame kamar lokutan baya in yazo visting zai samu ta rame sosai.

Nafisa tazo ta gaida Baffa, Baffa ya bata naira dari da k'yar ta amsa, Nafisa tacewa Ruk'ayyatu tazo ta gaida yan gidan su, Ruk'ayyatu duk bata so zuwa bata son 'dagawa kusa ga Baffa, dole ta tashi, Baffa a fuskar ya fahimci bataso ba, murmushi yayi yace taje ta dawo.

Wajen yan gidan su Nafisa suka je, Ruk'ayyatu ta gaida Maman Nafisa da yayun ta, Mamar  Nafisa kudi tana Ruk'ayyatu sai da tayi mata fa'da ta amsa.

Sai yammah Baffa ya wuce gida, bayan sati daya su Ruk'ayyatu suka fara rubuta SSCE, ko ka'dan Ruk'ayyatu bata karatu, burin ta duk bai wuce su kammalla jarabbawar ta koma gida.

Wasu teachers na taimaka masu, in zaa yi subject din su, shine Ruk'ayyatu zata rubuta abun kwrai, haka lokaci yayi ta ja har suka kammalla jarabbawar, ranar da zasu wuce gida Ruk'ayyatu baccin kirkir batayi ba, lokacin da Baffa yazo daukar Ruk'ayyatu Maimuna tayi kuka shine Karon farko da tayi kukan makaranta, Baffa ya lalashe ta, ya bata kudi da kayan da yazo mata da shi.

Ruk'ayyatu sai dariya takewa Maimuna, wani matashi na gefe yazo daukar k'aunar da ta k'are exams, tun da ya kyallah Ido yaga Ruk'ayyatu yake kallon ta, da ganin ta, tana cikin farinciki.

K'aunar shi ce ta fito rik'e da sauran kayan ta, har ta aje kayan hankalin sa na kan Ruk'ayyatu, maganar da tayi ne ya dawo dashi, tace yaya muje, motar ya bude ta zuba kayan, har ya zauna motar hankalin sa naga Ruk'ayyatu.

K'aunar sa Zainab ya Kalla yace wace wacen?  yana nuna mata Ruk'ayyatu, Zainab tace Ruk'ayyatu ce, aji mu daya wanan Mahaifin su ne, yazo daukar ta, yayan Zainab yace yan nan garin ne? tace eh, zan tambayi Nafisa itace k'awar ta sosai.

Jin tace Ruk'ayyatu k'awar Nafisa ce, yace su wuce don yasan abun zai zo da sauki don Nafisa garinsu daya k'aunar abokin sa ce.

Baffa da Ruk'ayyatu sallamar Maimuna sukayi suka wuce gida, Inna tayi murnar kammalla karatun Ruk'ayyatu, tasan badon ta jajirce Rukayya bazata yi karatun ba.

Bayan sati daya da k'are makaranta su Ruk'ayyatu, Zainab da yayanta Abubukar  da Nafisa k'awar Ruk'ayyatu da yayan ta Habib sukazo garin su Ruk'ayyatu, basu sha wahalar samun Nafisa ta rake su don yayan Nafisa abokin Abubakar ne, duk tare zasu je

Sosai Ruk'ayyatu ta tarbe su, tayi mamakin ganin har Zainab gidan su, Inna ma ta tarbe su sosai, Nafisa tacewa Baffa tare suke da Bak'i, Baffa ya shigo dasu cikin zauren gidan tabarma aka shimfida masu inna ta aiko masu fura da ruwa.

Bayan sun gaisa, yayan Nafisa Faruk yayiwa Baffa bayanin sunzo ne daga garin *Bajoga* abokin sa yaga Ruk'ayyatu  Baffa yayi murmushi  yace su nemi so wajen Ruk'ayyatu, duk da akwai masu nemanta sai dai ba wanda yayiwa alk'awalin auren ta, godiya sosai sukayi Baffa ya wuce ciki yacewa Ruk'ayyatu taje tayi bak'i.

*Asalin Labarin*

*Ummu Asma'u(Sa'adatu*)

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now