MUGUN ZALUNCI 49-50

295 16 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI*

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Ina godiya sosai gareku makaranta MUGUN ZALUNCI, masu korafi akan rayuwar da Ruk'ayyatu tasamu kanta a gidan Abubakar, da yanda Mimi ke samun nasara asirin da take yi, rayuwa kowa da irin tasa jarrabawa, duk abun da Allah ya kaddara maka bazaka tsallake shi ba, Ruk'ayyatu ta hadu da jarrabawa a rayuwarta, duk irin ibadar ta, Mumunai bayun Allah su Allah ke jarrabta a rayuwa don ya gwada imanin su, Mutane irin su Mimi akwai su da yawa a duniya, da wayyanda ma suka fi Mimi, akwai wata mata, Mutane da yawa sun San neman maza take yi da auren ta, mijin tayi masa asiri sai yanda tace, uwarsa  dubu daya shawa take bata, duk shekara sai tayi aikin Hajji, wani lokacin har Ummra, rayuwa kamar ita taba kanta, lafiya lau ba ciwon komai a jikinta, irin wayyanen me zaa ce masu? Wasu Allah nayi masu uziri, duk rayuwa tana tattare da jarrabawa, Allah ya bamu ikon cin jarrabawa mu, Allah yasa mu dace Ameen*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 49⚜50

Ruk'ayyatu ta dade kwance tana tunanin rayuwar ta da Lami'do, addu'a sosai tayi masa,tayi kuka har idanunta suka kumbra har dare bata ci abincin kirki ba, tea kadai take sha, abincin da ta girka wa Abubakar maigadi ta ba, tace in bayaci yayi sadaka.

Amsar abincin yayi yanajin da'di, don abincin yan aiki daban ake masu a gidan Mimi duk yanda aka ga dama haka ake basu abincin, godiya sosai yayi mata yace in akwai abunda takeso ayi mata tace ba komai, ta wuce bangarenta.

Washe gari Ruk'ayyatu ta shirya suka wuce Bajoga daukr Zara, ta kira Inna ta fa'da mata, Inna tace ba komai ta fa'dawa Gwaggo, Gwaggo batason a dauki Zara kar ta batawa Ruk'ayyatu tayi shiru, lokacin da suka isa gidan Gwaggo, Gwaggo sai kallon Ruk'ayyatu takeyi tana mamakin ramarta, ko ciki ke gare ta? Ruk'ayyatu taba su Gwaggo kudi, Zara  sai da'di take ji da taga mamanta.

Basu Jima suka wuce, duk da driven na gudu sosai sai shabiyun suka shiga Abuja, a gajiye Ruk'ayyatu ta shiga gida, Zara tayi bacci a mota, sosai rashin barin ta zuwa wajen su Inna yayi mata ciyo.

Tun lokacin da Abubakar suka wuce har akayi kwana biyu bai kira Ruk'ayyatu ba, soyyayya abun suke yi da Mimi, in yaje wajen aikin da ya kai sa da safe da yammah in ya dawo su sha wanka su tsuke cikin k'ananen kaya su fita, siyayya sosai  Mimi keyi, Abubakar ya samu yanda yake so, komai yake so shi Mimin sa keyi.

Sai bayan sati daya Abubakar ya kira Ruk'ayyatu, ya tambayi Zara tace gata nan, kudi yace zaa kawo mata duk abunda takeso sai ta aika driver, tayi masa maganar tanason zuwa gidan Dr Ibrahim da Alhaji Mansur yace driver ya kaita, cikin kwana biyu ta fita taje gidan Dr da Alhaji Mansur.

Bayan sati biyu su Abubakar suka dawo, Mimi tayi kyau abunta, an kashe kudi sosai, ranar da suka dawo Ruk'ayyatu ganin su dai tayi don baice kirata zasu  dawowa ba, tana kici tana girki ta gyara gidan kamar tasan zai dawo, dariyar Zara da tabari falo tana kallon cartoon yasa ta fito da sauri, a tsorace ta kallesa.

Ganin irin kallon da taje masa yace yayi kiranta bai samu ba, gefen Mimi ya wuce, Zara ta lak'e masa ya wuce da ita, Ruk'ayyatu duk bata so ba don tsoron halin Mimin takeyi yanda tayi mata ranar da taje gefen ta, Mimi na bedroom Abubakar ya shigo da Zara, suna falo driven su Mumy ya kawo yaran Mimi, suna ganin Zara suka fara wasa.

Mimi jin hayaniya tayi yawa ta fito, Ido ta zuba tana kallon Zara Abubakar ta Kalla tace waye wanan? Abubakar yace 'diyar Ruk'ayyatu ce wadda nace maki Mahaifin ta ya rasu, Mimi mai aikinta ta k'wallawa kira, tace ta dauki Zara ta mayar da ita, Abubakar cikin mamaki yace mai aikin ta bace masa da gani.

Mimi Ido ta bude, tace mai aikin  ta wuce hannun Zara ta ja, Abubukar yace ta sake ta, ko kallon sa batayi ba, Nur ce ta biyo Mimi tana fadin Mumy live her she is my new friend, Mimi tsawa ta daka mata, Nur ta koma gefe tana kuka, Zara ma kuka take yi.

Mimi waje ta turata ta rufe k'ofar, Abubakar ransa ya baci ya fara fa'da ya fa'di Mimi ta fa'di, Ruk'ayyatu na gefen taji kukan Zara da sauri ta fito, ta na zaune k'ofar shega gefen Mimi tana kuka, Ruk'ayyatu daukota tayi tanajin hayaniyar Mimi, Abubukar yayiwa Mimi rantsuwa Zara bazata bar gidan ba.

Mimi ranta ya baci, me ke faruwa ne haka, dole ta tashi tsaye, Ruk'ayyatu wucewa tayi tana godewa Allah, tun tafiyar su addu'a sosai take yi don lokacin da taje gidan Dr, matar Dr tace mata ana zargin Mimi da yiwa Abubakar asiri ta tashi tsaye da addu'a, ba abunda yafi karfin addu'a.

Abubakar gefen Ruk'ayyatu ya wuce, yayi wanka ya shirya ya dibo wasu kayansa a gefen Mimi, abinci yaci ya fita, bayan fitarsa, Ruk'ayyatu na zaune Falo ganin Mimi dai tayi kanta, kamin tayi tunanin komai Mimi ta kwashe tada Mari, Ruk'ayyatu da karfi ta tashi ta dauke Mimi da mari, suka fara dambe, Mimi da azaba tayi mata yawa ta fara ihu😂 ta mance Fulani suna suka tara Ruk'ayyatu tashin k'auye ce, ita ko tashin bariki ce , masu aikin gidan suka shigo suka raba su.

Duk fuskar Mimi ta  kumbura, Ruk'ayyatu Mimi da taji wuya ta cizo mata kunce, Zara da su Nur kuka sukeyi, Mimi Abubukar ta kira tana kuka ta basa hankuri tace taje gefen Ruk'ayyatu ta bata hankuri ta dauko Zara, Ruk'ayyatu tafara zaginta har da duk duk fuskar ta ta kumbura da k'yar yan aikin suka amshe ta.

Abubakar cikin b'acin rai yace gashi nan zuwa, bazai daukar ma Ruk'ayyatu iskanci ba, Shifa ya gaji da wanan auren, yana zaune lafiya ya jajibo ma kansa wahala, Mimi tayi shewa tace kin dake in yau za kiga iskanci, yanda ki shigo gidan haka zaki fita, zan ta kulla maki tugu, makirci da asiri.


*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now