MUGUN ZALUNCI 43-44

269 17 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI*😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 43⚜44

Sai bayan sati daya Alhaji Mansur ya ciyo kan Abubakar aka kammalla gyara inda Ruk'ayyatu zata zauna duk yayi masa magana zai ce aiki yayi masa yawa, Dr Ibrahim ma sai da ya nuna masa b'acin ransa, sau biyu Abubakar na zuwa Gombe, baya kwana yini yake yi, in zai tafi sai yacewa Mimi aiki yayi yawa, ko suna da bak'i, duk zuwan da yayi ko ruwa bazai sha ba sai ya nemi Ruk'ayyatu, cen k'asan zuciyarsa Ruk'ayyatu daban ce a cikin mata.

Ya rasa me yasa yake tsoron Mimi, a ranar da aka kare gyaran gefen Ruk'ayyatu Abubakar ya fa'dawa Mimi Ruk'ayyatu zata dawo, masifa sosai ta zuba masa yace ta kwantar da hankalin ita dabance, bayason yayansa yaga baiyi masa shine ya auro masa Ruk'ayyatu, kuma Ruk'ayyatu ba ajinta ce ba, yar tallakawa ce gaba da baya, hankurin zama ne kurum yake yi da ita, Namiji sai a barshi.

Mimi taji da'di a ranta tace ashe yar matsiyata ce, ta zaci 'diyar wani Don ce, Mimi tace kar ya ha'da matsayin su Abubakar yayi murmushi yace bazaku ma hadu ba Gimbaya ta, kudi ya sakarwa Mimi, yace zaije dauko Ruk'ayyatu tace yasa Driver ba inda zai je, Abubakar vduk yaji ba da'di don yacewa Ruk'ayyatu zai zo ya dauko ta, Driven office ya turawa Ruk'ayyatu, yace kaya dai zata zo dasu na sakawar ta,komai ya siye.

Ruk'ayyatu taso taje Dukku yace sai wani lokaci a waya sukayi sallama da Inna dasu Gwaggo, Larai Bala Driven ya mayar da ita Dukku, Driven sai yammah ya iso ya kwana da safe sukayi sammako, koda suka isa Abuja sha biyun rana, Mimi taje office, Abubakar yana office ya dawo gida.

Ya dawo bada jimawa su Ruk'ayyatu suka iso, Ruk'ayyatu sai kallon gidan takeyi, gefenta suka wuce Abubakar ya nuna mata wajen 3bedrooms ne da falo biyu, dayan dakin nata daya nashi, dayan yace zaa kawo mata masu aiki, falo daya nata daya nasa, sai kicin.

Ruk'ayyatu godiya sosai tayi masa, Abubakar kallonta yayi yana mamakin halayenta komai godiya ake masa, ko don bai saba samun haka ne a wajen Mimi, Driver Abubakar ya aika yayi masu take away, bayan sun k'are ci Abubakar yaja Ruk'ayyatu dakin sa.

Sai bayan la'asar suka tashi, Abubakar fita yayi yace zaije ya dawo, Ruk'ayyatu k'ara gyara gefen tayi tasa turaren wuta, ta kira Dr Ibrahim suka gaisa ta kira matar Dr, shewa tayi tace zamo zo muga Amarya Honorable.

Ruk'ayyatu kici tashiga ta dora abinci ita ko ka'dan batason abincin siyawar wanan, ka'dan ta dora, batasan yanda tsarin gidan yake ba, komai akwai a kici, gas dinma an ha'da duk tasan yanda ake amfani dasu zamanta da Lami'do, shinkafa ta dafa ta ha'da salad, tana kici tana aiki taji ana zuba hon zaton ta ko Abubakar ne.

A tagar Falon ta lek'a kyakyawar mota taga ta shigo tana lafe har motar tayi parking, maigadin da yan aikin gidan duk suka fito, Mimi ce ta fito cikin Black suit tayi rolling da black Vail haaka take zuwa office wani lokacin, Ruk'ayyatu baki ta bude ko ita ce matar gidan, takalmin dake k'afarta ta Kalla, masu tsini kallonta takeyi tana tunanin yanda zaa yi tafiya dasu.

Mimi fitowa tayi tana 'dagawa yan aikin hannu, gefenta ta wuce, tana tafiyar kamar tana tausayin k'asa har ta shege Ruk'ayyatu na tsaye tana kallonta, Ruk'ayyatu kici ta koma tana tunanin yanda zaman zai kasance.

Abubakar sai dare ya dawo gefen Mimi ya fara shiga, da gudunta tazo tana masa oyoyoyoyo, Abubakar tsaye yayi yana mamaki Mimi ce ko? cikin daki ta jasa ta ha'da masa ruwa yayi wanka suka wuce dining, abinci ka'dan yaci suka zauna falo, sam Abubakar mancewa yayi da wata Ruk'ayyatu a gidan.

Ruk'ayyatu tun dawowar Abubakar take zuba Ido har ta fara jin bacci, a tunanin nan zai kwana tunda ita tazo, ganin shiru tayi masa text tana masa sannu da zuwa, yana kwance Mimi na jikinsa text ya shigo ganin sunan Ruk'ayyatu ya tashi da sauri sam ya mance da ita, Mimi k'ara shige masa tayi tace lafiya ina zakije?

Abubakar kwantawa yayi yace zanje in deba Ruk'ayyatu sam na mance da ita,Mimi kallonsa tayi, kallon raini tace ba inda zataje girki nane in nafita kaje, kwantawa yayi yace angana gimbiya.

Mimi tun zamanta da Abubakar bata tafa shan kayan mata da sunan gyarawa ba sai da ya auro Ruk'ayyatu bata ma yarda dasu, dayawa k'awayenta na bata tace bataso, sai yanzun.

Ruk'ayyatu tun tana zuba idanu ko Abubakar zai zo har bacci ya dauke ta, bata falka sai ukkun dare, cikin tsoro ta tashi, me kenan Abubakar bai zo ba? Zama tayi tana nazari ganin zaman baiyi ta tashi ta wuce toilet arwala tayi ta fara sallah.

Bayan ta sallame ta shiga tunanin wane irin zama ne wanan, ta zaci zai zo ya kaita su gaisa da mutanen gidan, ta zaci girkin tane yau ita da tazo, wasu hawaye ne masu dumi taji sun zo mata me ke faruwa da Abubukar ne ko ya mance tazo ne?

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now