MUGUN ZALUNCI 53-54

284 15 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 53⚜54

Duk wani shire-shige da su Mumy ke tunanin in sunyi cikin Ruk'ayyatu zai zube sunyi ba nasara, sun rufe layu Kala-Kala da aka ce in ta tsallaka cikin zai zube shiru ciki daram, Mumy da Mimi hankalin su sosai ta ya tashi.

Ruk'ayyatu sai murjewa takeyi abun ta tayi fari ta danyi jiki, Zara na zuwa makaranta lafiya lau, in sun dawo ko Nur sun jata gefen Mimi bata zuwa, sai Abubakar na nan, har yarinyar tasan irin zaluncin da Mimi ke mata.

Ruk'ayyatu, yawan mugayen mafalkin da takeyi ta dage ga addu'a sosai, cikin ta ko ka'dan baya bata wahala, bata amai komai batayi, har ta saba da rashin adalcin Abubakar duk inda zai tafi da Mimi yake zuwa, sosai tasan yanda Abubakar din ke shakar Mimi, duk da wani lokacin, zai mata abun da Ruk'ayyatu ma bazai ma ba.

Abun nasa kamar mai aljannu, haka Ruk'ayyatu keta fama gidan Abubakar, cikin ta ya fara girma ta fara zuwa hospital gurin awo, wani lokacin sai ta shirya Driver yace Mimi ta aike sa, in tayiwa Abubukar magana, sai yace ta jira batada hankuri, in abun bai kansa ya kira driven yayi tayi masa fa'da.

Ruk'ayyatu bataje Dukku sai lokacin auren Maimuna, mutane da yawa sunyi mamakin ganin ta da ciki kowa k'in fa'dawa tayi, kunya Fulani, Inna taji da'din ganin Ruk'ayyatu da Zara, cikin kyakyawaar shigar su, duk da Inna ta so ta fahimci kamar Ruk'ayyatu nada damuwa, Inna ta k'yale da niyar in ank'are bikin ta tambaye ta.

Alhairi sosai Abubakar ya aikowa Baffa, Baffa sai albarka yake saka masa da yabon halayensa, cikin rufin asiri akayi bikin Maimuna a Gombe aka kaita, Ruk'ayyatu ce kirjin biki, sosai Abubakar ya sakar mata kudi da zata je gida bikin.

Abubakar ma yaje daurin aure, bayan daurin auren ya shiga cikin gidan su Ruk'ayyatu alhairi sosai yayiwa yan uwanta, da yawa suna ganin Ruk'ayyatu tayi sa'ar miji.

Inna ta tambayi Ruk'ayyatu ko akwai matsala ne, Ruk'ayyatu tace ba komai Inna, Inna tayi shiru, tana addu'ar Allah yasa hakan ne, ta k'ara tuna wa Ruk'ayyatu ta nemi abun yi dogaro ga kai nada amfani ko don gaba, rayuwa baka san inda rana zata fa'di ba.

Ruk'ayyatu tace in ta haihu zata yi nemi sani'ar yi, sun jima suna fira da Inna, Inna tace komai rintsi tayi hankuri da rayuwa, Adda Saudi na gefe, Inna tace kema kiyi hankuri da yanda Allah ya tsaro maki rayuwa kin rasa miji lokacin da kike buk'atar sa.

Ranar har dare yayi sosai suna fira da Inna, Baffa yayi ta jan Inna yana cewa ta saka yara gaba bako kunyar Fulani.

Inna murmushi tayi tace, bari muyi fira wanan rayuwar, mutuwa ko yaushe na iya daukar mutum, Baffa yayi dariya yace ke kam kwanana ko yaushe cikin maganar mutuwa kike, sai kwana sun k'are ake mutuwar nan fa, wucewa Baffa yayi yana cewa in zan tafi in barki da yaranki, Inna tace miyakawo wanan maganar yayi dariya ya shige dakin sa.

Da safe su Ruk'ayyatu sukayi sammakon zuwa Gombe gidan Maimuna ma tsatsaye ta shiga suka wuce airport don da jirgi suka zo suka koma, Mimi taji ciwon abun, har Ruk'ayyatu tayi matsayin tafiya da jirgi.

**** ****

*Bayan wattani shidda*

Mimi ta duk garin Allah ya waye zata shiga gefen Ruk'ayyatu su gaisa kamin ta wuce aiki, in tadawo haka, ranar da ta fara shiga, Ruk'ayyatu mamaki tayi sosai, Mimi kuwa wani aiki Malamin Bargu yayi masu, yace in Ruk'ayyatu ta fara labour a ha'da wani abu da ya basu a daure haka zatayi ta wahala har babyn ya mutu da uwar ma, shine Mumy tace sai ta shiga jikin Ruk'ayyatu yanda in ta fara labour zata ji.

Matar Dr Ibrahim tace duk Ruk'ayyatu taji labour ta kira su, kar ta fa'dawa kowa gidan.

Ranar Jumma'a Mimi ta shiga gurin Ruk'ayyatu, tace in Ruk'ayyatu taji wani abun ta kirata, Ruk'ayyatu tace to, ta gode sosai, ta fita kenan Ruk'ayyatu ta fara jin ciwon mara Anty ta kira yanda take cewa matar Dr, cikin kank'ani lokaci Anty tazo suka wuce hospital, baa dauki dogon lokaci Ruk'ayyatu ta haifi kyakyawar yarinya ta, Abubakar Sak.

Dr Ibrahim Abubakar ya kira cikin murna ya wuce hospital din, Abubakar Mimi ya kira, ya fa'da mata Ruk'ayyatu ta haihu, Mimi wani irin abu taji ya tsaya mata a zuciya, Barka tayi masa tace Meeting zasu shiga, Mumy ta kira, Mumy ma abun yayi mata ciwo, sun sha bari a cikin.

Gida su Ruk'ayyatu suka wuce matar Alhaji Mansur tazo, ta kawowa Ruk'ayyatu cikin yan aikin ta ta kula da ita, dattijuwar ce, Abubakar kamar haihuwar farin, sai murna yakeyi.

Ya kira su Inna, Gwaggo ya fa'da masu, sai dare Mimi ta dawo ko kallon gefen Ruk'ayyatu batayi ba, Anty matar Dr tana gidan har dare sai mamakin Mimi takeyi, ta tausayawa Ruk'ayyatu kishi da wanan jahilar.

Bayan kwana biyu, su Adda Saudi da wasu yan uwan Ruk'ayyatu suka zo, Maimuna Amarya sa biki saura kwana daya tazo,tayi kyau abunta, Abubakar yayi hidima sosai, Mimi ta k'ara haukacewa, ranar suna Yarinya taci sunan Gwaggo Mahaifiyar Lami'do, Aisha, Ruk'ayyatu da kukan ta tanayiwa Abubakar godiya.

Gwaggo ma rasa bikin magana tayi har Bajoga Abubakar yasa aka daukota, bayan an k'are biki Abubakar yayiwa su Adda Saudi alhairi suka koma, Ruk'ayyatu ma ta bata kudi murna sosai tayi, tace zata k'ara Jari don akwai k'okari nema gareta.

*Bayan wattani Tara* da haihuwar Aisha matsalolin suka yi yawa tsakanin Ruk'ayyatu da Abubakar tsanarta yake ji sosai, hankuri sosai takeyi, tayi biyarsa taje gida aga Aisha yak'i barinta, sunyi tafiya da Mimi yafi a kirga har saudiyya da Ummra Mimi taje, Ruk'ayyatu tayi magana Abubakar yace bak'in ciki takeyi tun baida komai yake tare da Mimi.

Ruk'ayyatu shiru tayi, da abun yayi yawa ta fa'da Dr Ibrahim, ranar Abubakar kamar ya duketa yayi mata rantsuwa ta sake kai k'arasa bak'in aurenta, Ruk'ayyatu hankalinta ya tashi rok'on Allah ta shiga yi, ya kawo mata sauk'i wanan *MUGUN ZALUNCI*

Ruk'ayyatu na kwana da safe Adda Saudi ta kirata tana kuku Inna babu lafiya, tashi tayi cikin tashin hankali, Abubukar ta kira yana gefen Mimi yace Baffa ya kira sa, yace ta shirya akai su airport, su wuce Gombe, gobe zaizo, kudi ya bata Ruk'ayyatu ko wanka batayi jallabiya tasa, ta cenzwa Humaira Pampers sunan da take kuranta, Zara ma cenza mata kaya tayi suka wuce.

Koda suka sauka Bala na jiran su, Dukku suka wuce Ruk'ayyatu gabanta na faduwa, tana tuna mafalkin da tayi Inna tana cewa tayi hankuri, tayi mata Bye Bye ta b'ace.

Adda Saudi ta kira da suka shiga ta fa'da masu suna General hospital Dukku, Ruk'ayyatu tace Bala ya wuce hospital din, suna a waje ta samu su Baffa likitoci na diba Inna, Baban likitan ne ya fito, suka biyo sa, yace suyi hankuri Allah yayi mata cikawa.

Ruk'ayyatu ihu ta fasa, ta fa'di zaune, da sauri wata nurse dake bayan Dr ta amshi Humaira.

Baffa ginin wajen ya rik'e yana kiran sunan Allah.

Adds Saudi, zubewa tayi tana zuba kururuwa😭😭😭😭😭.

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now