*MUGUN ZALUNCI* 😡📝 *Ummu Asma'u 65-66

290 16 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 65⚜ 66

Sai da motar tayi juyi sosai taje ta daki wani k'aton ice dake cikin jejin, icen ya raba biyu rabin sa ya fadarwa motar, lokacin su Mumy basu San inda kan Su yake ba, mai motar dake bayan su yaga lokacin da motar tayi cikin jeji, parking yayi yana tare mutane don a taimaka masu, motoci biyu ne suka tsaya.

Cikin sauri suka isa wajen motar, da k'yar suka dauke icen dake kan motar, Mumy suka fara fisuwa ita ke mazauni mai zaman baza da k'yar suka fito da ita k'afar ta daya ta juye ga dukkan alamu ta samu mumunar kariya a k'afa, bata San inda kanta yake ba, dayan k'afar ma ta ji rauni sosai, gefe suka ajiye ta suka fito Hajiya Batulu ita ma sosai taji rauni, wuyanta baya tsayi da kyau, ita ma ga dukkan alamu wuyan ya samu matsala.

Wani cikin mutanen yace mata akwai k'aramin tunanin, irin wannen hanyar mace zata bi bawani Namiji tare dasu, dayan mutumin yace a nemi wayar su a kira yan uwan su, wayoyin su suka shiga nema cen k'asan sit suka zak'ulu wayar Mumy, duk ta fashe, sa'ar ma ana iya kira.

Last call dinta Mimi sukayi waya ita suka kira, Mimi cikin sauri ta dauka, tana cewa Mumy har kun isa, a dayan bangaren aka ce mai wanan wayar sun samu hatsari, zamu nemi yansanda Mukai su asibiti mafi kusa sai kuyi sauri kuzo, Mimi cikin tsananin tashin hankali tace gamu nan ya kwatanta mata gurin da suke.

Mimi cikin tashin hankali ta kira Dady, Dady cikin mamaki yace hatsari wadda tace suna bikin 'diyar k'awar ta, yace tazo zai nemi ambulance aje basu San yanda abun yake ba, Mimi Abubukar ta kira layin sa baya zuwa cikin sauri ta wuce a hanya suka hadu dasu Daddy da ambulance suka wuce.

Mutanen da suka taimakawa su Mumy yan sanda suka kira aka wuce dasu asibiti, ka'dan suka fita cikin Minna, Minna aka maida su, an isa dasu baa jima su Mimi suka isa, koda suka je an shiga tiyata da su Mumy, likitoci sun kai biyar a kansu.

Bayan mituna talatin babban likitan ya fito yana tambayar yansandan ko yanuwan su sun iso, Dady cikin sauri yace gasu sunzo, likitan yace gaskiya rayuwar su na cikin hatsari, dayan ta samu matsala a wuya da hannu, dayan kuma a k'afafun ta sun samu matsala zai yi wuya ba sai an yanke su ba.

Daddy cikin tashin hankali, yace Dr ko zamu iya ganin su in zai yuyu mu wuce dasu Abuja da ambulance mukazo, likitan yace zai yuyu zamu basu pain relief, tunda da ambulance ne, sai dai suna cikin zafin ciwo.

Mimi na tsaye gefe sai kuka takeyi da tausayin Mumyn ta, duk akan tane wanan abun ya faru, cikin tiyata da su Mumy suke suka shiga, Daddy kallo daya yayiwa Mumy ya kauda kansa yana zubar da hawaye, wanan wace irin kaddara ce, awanni ukku da suka wuce Mumy lafiyar ta lau, yanzun ga k'afafun ajiye,wanda da k'yar in zata k'ara iya amfani da su.

Mimi kuka takeyi sosai, alluran rage zafi akayiwa su Mumy da Karin ruwa da jini aka wuce dasu cikin ambulance, Gudu sukeyi sosai don su isa Abuja, su Mumy na cikin mawuyacin hali, sai da sunka fara hanya Daddy ya kira mijin Hajiya Batula shima yace ce masa tayi zasu je sunan k'awar su da Mumy, National hospital ya wuce don Daddy yace masu sunyi kusa.

Suna isowa aka wuce dasu tiyata, bayan wani lokacin likitan ya fito yana share zufa ya kira Daddy da Mijin Hajiya Batula, yayi seconds yana tunanin yanda zai fa'da masu, Hajiya Batula ta samu matsala a kanta, zaiyi wuya tunanin ta ya koma dai, zata koma tana rayuwa irin ta mahaukata, hannunta daya sai an yanke, ta samu matsala a wuyanta, Mumy k'afafun ta yanke su zaa yi don basa da amfani duk sun samu matsala, haka ya daure yayi masu bayani, sosai abun ya tafa su, Daddy yace ko zasu fita waje su gani ko zasu iya yi masu wani abun kamar Germany, likitan xtray din da aka yiwa Mumy da Hajiya Batula ya nuna masu yayi masu bayani komai.

Basu da zafi suka saka hannu, Mimi kamar zatayi hauka kuka takeyi sosai, Abubakar ta k'ara kira ya dauka ta fa'da masa, suna asibiti, ya same su har an shiga tiyata dasu Mumy, Mimi wani mugun zazafi taji ya rufeta sai rawa sanyi takeyi.

**** *****

Ruk'ayyatu ta kira Dr Ibrahim ya fa'da masu suna Gombe, Gombe suka shirya suka wuce ita da Baffa, bayan sun sauka mota, Dr yasa aka dauko su, Dr Ibrahim ya kai Baffa gidan su Munira suka yi masu gaisuwa, yan uwan Dr sosai suka tarbi Ruk'ayyatu, Umman su Dr sai jan Ruk'ayyatu takeyi da fira tace Dr ya tafa bata labarin ta.

Kwanan su daya, suka koma Dukku, Umman su Dr taba Ruk'ayyatu num ta ta karfi na Ruk'ayyatu tace zasu gaisa, Dr yasa driven sa ya maidasu Dukku, da zasu wuce kudi ya kira Ruk'ayyatu gefe ya bata tace bazata amsa ba, sai da ya matsa ta amsa, su Amma yan tagwayen Dr da Ruk'ayyatu zata wuce suka rik'e ta sai sun bita, da dabara aka rabasu.

Umman Dr sai kallon su Amma takeyi yanda suka rik'e ma Ruk'ayyatu hannu tana k'isisima wani abun a ranta.

Sai da akayi sati biyu da rasuwar Munira Dr ya fara shirin komawa Abuja da Umman sa zai tafi, su Amma sunfi saboda ita don tana zuwa Abuja akai-akai, ranar da suka koma Abuja Umman Dr tacewa Dr ya nemi auren Ruk'ayyatu, Dr cikin tsoro yace matar abokin sa, bazai iya ba, duka yaushe Munira ta rasu da zaiyi aure, Umma tace shawara ce yaje yayi tunani, Dr duk ya shiga damuwa ko ka'dan bai tafa tunanin neman Ruk'ayyatu ba.

Ruk'ayyatu ta kira num Dr Ibrahim sau biyu bai 'daga ba, tana son taji ko sun isa lafiya, ya kirata yace zasu wuce da Umman sa, num Umman ta kira, Ummun tace zata fa'da masa ya kirata, Umma tace Ruk'ayyatu ta turo mata num Baffa zasuyi magana.

Ruk'ayyatu bata kawo komai ta tura mata, Dr yana ganin call din Ruk'ayyatu ya kasa dauka,sosai yake ganin rashin dacewar ya auri matar Abubakar, yaushe Munira ta rasu?

Scopion duk ya rame yayi baki yayi ta kira num Hajiya Batula bata zuwa, shi kam ya gaji, yana son ya nemi Ruk'ayyatu ta yafe masa, zai nemi Abubakar ya fa'da masa gaskiya sharri aka yiwa matarsa.

Ya tuba zai rok'i Allah gaffara duk wani mugun aikin da ya aikata, tun nan duniya ya fara ganin azaba, a mafalki ma kenan, macijan nan dayake gani suna fitar da wuta mai zafi, ko kusan wutar yayi zafi yake ji, bayada halin runtsi idanuwansa da sunan bacci.

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now