MUGUN ZALUNCI 27-28

267 14 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Wanan shafin nake Matan da suka rasa mazajen su, Allah ya ha'da ku da Abokanin rayuwa nagari*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 27⚜28

Addu'a sosai akewa Munnawara cikin ikon Allah, bakin ta ya bude, ta fa'dawa Umman su abun da ta gani ranar da tafara rashin lafiya, Abban su yayi shiru yana nazari, Abubakar ta tambaya? Umman su, bata boye mata komai tayi mata bayanin rashin zuwan sa sai Alhaji Mansur da matarsa da suka zo.

Munnawara taji ciwon yanda Abubakar ya guje ta kenan ba son gaskiya yake yimata ba, tace ba komai Allah ya ha'da kowa da rabonsa, Abban su ta Kalla tace ta amince yaron Gwaggo kareme ya fito, tun farko shike son ta tace batason sa, Gwaggo kareme tace baza'ayi mata dole ba.

Gwaggo kareme k'aunar Abba ce uwa daya uba daya, Mijin ta hamshak'in mai arziki ne, Babban yaronta Najibu keson Munnawara kamar yayi hauka, Abba hamdala yayi har ga Allah yafi son auren Munnawara da Najibu, ko ka'dan bayason yaransa su auri hausawa don akwai bambamci al'ada.

Umma ma taji da'din haka don Gwaggo kareme mutuniyar tace sosai, bata mance tsayawar da tayi bazaa yiwa Munnawara dole ba, don tasan in wata ce yanda Abba yace sai anyi zata biye masa.

Cikin kwanaki aka saka ranar Munnawara da Najib, murna gurin Najib ba'a magana, duk da har lokacin bawani sake mashi Munnawara keyi ba.
**** *****

Zaman Abubakar da Mimi abun har ya wuce tunanin mai hankali, bayan sunje Bargu sun dawo abun k'ara lalacewa yayi wani mugun shakkar Mimin ya k'aru sai dai Malamin yayi masu bayani raba Abubakar da neman mata sai a hankali, Abubakar mabuk'aci ne mace daya bata yi masa.

Mumy tace gara yayi ta neman su a waje kan ayiwa tilon 'diyar ta kishiya, Malamin ya yi masu aiki sosai, rubutu ayoyin Qur'ani yayiwa Mimi a jiki, yana rubutun yana nishi, daman haka yakeyi, wasu matan har tarawa yakeyi dasu.

Wayyanda suka bashi sha'awa sosai, in sun ki amincewa sai yace suje su dawo kamin su dawon zaiyi aiki kansu da sun shigo dakin sai hankalin ya bace, wasu ma bazasu gane ya kwanta dasu ba sai sun koma gida.

Mimi yana nishi tana hararasa, ganin ta gimtse fuska ya kama kansa don yana mugun samun kudi hannusu da Mumy, amman yasha alwashin sai ya tara da Mimi watarana yanzun zai kama kansa bayason su kubce masa, don ya lura Mimi ba irin matan dake zuwa ne ba, kanta a waye yake.

Dr Ibrahim na shirin tafiya Bajoga call din Abubakar ya shigo, yak'i dauka don tun kan maganar Munnawara basa wani kula juna, yayi ta kira yak'i dauka, karshe ma kashe wayar yayi.

Dr Ibrahim na kok'arin fita get din gidan sa Abubakar na kunne hancin motar sa, blocking hanyar yayi yanda Dr bazai iya fita ba, Abubakar ya fito ya isa wajen da ya mik'a masa hannu yana masa sallama Dr ya amsa ba yabo ba fallasa, cikin ha'de rai yace ka tare mun hanya zanyi tafiya ne, Abubakar ya bude gefen mai zaman bazan ya zauna yana Murmushi yace Allah ya huci zuciyar likita.

Nayi kure ayi min afuwa, na rasa meke damu hakan ko sunan Munnawara Bana son inji wani irin k'iyaryar  ta nakeji a raina wallahi, Dr Ibrahim yayi shiru yana nazari  Abubakar duk ya rame, tabbas yasan auren Mimi na cikin jarrabawa da Allah yayi masa rayuwarsa.

Ko jiya Alhaji Mansur ya kira yana basa hankuri ya saurari Abubukar din don Dr Ibrahim bai boye masa ya fa'da masa bazai k'ara shiga harkar Abubakar din ba, Dr ya kalli Abubakar ba natsuwa ko ka'dan a tare da shi.

Dr yace ba komai ya wuce yanzun zan tafi Bajoga, Faruk Allah yayiwa rasuwa, Abubakar cikin mamaki yace wane Faruk? Dr Ibrahim yace Faruk Bajoga wanan junior mu a Makaranta, Abubakar yayi shiru sosai mutuwar ta tafasa

Cikin sanyi jiki yace yaya wanan Abokin sa zaiji ko? wayyanda muka hadu sunzo asibiti me ma sunan sa, Dr Ibrahim yace Lami'do shi ma Allah yayi masa cikawa Abubakar Ido ya zubawa Dr yana fadin Innalilahi wa inna ilaihin rajiun, yaushe? Dr Ibrahim yace ranar da naje gidanka, naje har rasuwar in fa'da maka baka sauraren ba.

Abubakar idanunsa sunyi ja, yace kabar motarka gida muje gida in dauki kayan tafiya zan bika muje, gefe Abubakar ya koma ya kira Majority leaders su a house don sunada Sitting gobe ya fa'da masa anyi masa rasuwa zaije ta'aziya.

Gaisuwa yayi masa sukayi sallama, Dr Ibrahim ya maida motar gida suka wuce maitama gidan Abubakar, tun a get din gidan sauti ke tashi kamar club, Mimi ce da k'awayenta.

Dr Ibrahim a mota ya zauna yana jiran Abubukar,  ko ganin Mimi bayason yi don yasan ba alhairi ce a rayuwar Abubakar ba, Abubakar mutumina arziki ne ga alhairi, Abubakar falon Mimi ya sameta yace zaije Gombe anyi rasuwa, hannu ta 'daga masa, ba tambayar wa ya rasu balle Allah ya jik'an sa, dakin sa ya wuce ya ha'da kaya Kalla biyu a k'aramin trolley bag ya fito, wani yaro dake masu hidima yaba yace yakai mota.

Driven sa ya kira, cikin mintuna yazo suka wuce Mimi ko kallo bai isheta ba, a hanya duk shiru sukayi Abubakar sosai mutuwar ta tafasa, juyowa yayi ta gefen Dr yace ya wanan matar Lami'do ta haihu, Dr Ibrahim yace akwai yarinya 'daya tsanin su.

Faruk dashi da matarsa suka rasu, Abubakar shiru yayi yana kiran sunan Allah a zuciya, Dr Ibrahim yace Ruk'ayyatu da Gwaggon Lamido ne abun tausayi, Gwaggon su biyu ke gareta duk sun rasu, a Faruk gidan su sunada yawa Mahaifin su nada rufin asiri.

Abubakar yace Ruk'ayyatu yar ina ce? Dr yace Dukku, Mahaifin ta tallaka, yanda Faruk ke fada min Lami'do ne mai taimakon su, don akwai yayarta da mijin ya rasu ya barta da yara, Abubakar yace yanzun wane taimako kake ganin zamuyi masu?

Dr Ibrahim yace bari mu isa in kaina abun da nake nazari kenen, duk shiru sukayi kowa da abunda yake sak'awa a ransa.

*Ummu Asma'u( Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now