MUGUN ZALUNCI 47-48

285 12 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI*😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 47⚜48

Ruk'ayyatu tun da tayi sallar subahin bata kwanta, karatun Qur'ani tayi har gari ya waye, cikin gidan tafara gyarawa, bayan ta k'are kicin ta wuce ta fara hadawa Abubakar break fast, dankali da Kwai ta soya tayi warming ragowar ferfesun da tayi da dare, ta shirya table ta wuce dakin ta tayi wanka.

Cikin kank'ani lokaci ta shirya cikin riga da zane na atamfar Holland, cikin ire iren dinkuna da matar Alhaji Mansur tayi mata, , duk tunanin Ruk'ayyatu Abubakar na bacci dakin sa, dakin ta wuce ba Abubakar ba alamarsa, ta diba toilet baya ciki, Ruk'ayyatu falo ta zauna tunanin ko yaje diba mutanen cikin gidan ne.

Tana zaune falo taji ana bude get din gidan da sauri ta isa wajen window falo, labulen ta 'daga Abubakar ne da Mimi zaune bayan mota driver na Jan su, Mimi cikin shirin zuwa office, Abubakar din ma yasha manyan kaya, Ruk'ayyatu idanun ta suka ciko da hawaye, wanan wace irin rayuwa ce, cikin falon ta koma ta zauna, ranta ya baci sosai, wayar ta dauko da niyar kiran Abubakar,  jin tayi bazata iya kiran sa ba.

Zaune tayi tana zubar da hawaye, tana jin yunwa ta kasa cin abincin, tana nan kwance, taji text ya shigo, Abubakar ne, yace zai aiko driver ya amsa masa abincin, Ruk'ayyatu to kawai tace, Abubakar shiru yayi bayan ya kashe wayar, baya son b'acin ran Mimi yana kwance ta kira sa, gefenta ya wuce yayi wanka ya shirya, daman tace kayansa suna gefenta, tunda ko ina gidan sa ne, ba tunanin komai ya barsu.

Komai baici ba suka fita, bayan ya aje Mimi ya isa office yace driven ya koma ya karfo abincin, Ruk'ayyatu abincin ta ha'da a basket aka wuce da shi, ranar Abubakar da ya dawo office gefen Mimi ya wuce, sai dare ya shiga wajen Ruk'ayyatu, abincin da ta sake girkawa ka'dan yaci suka kwanta, Ruk'ayyatu komai batace masa.

Bayan kwana biyu Abubakar ya koma gefen Mimi, a cikin kwanakin girkin Ruk'ayyatu yanda suka ga dama haka suke mata, ta kasa yiwa Abubakar magana, damuwa sosai ke cin ta ga kadaici, ita daya gefen ta, tun lokacin da Mimi ta amshi girki Ruk'ayyatu bata k'ara ganin Abubakar ba, sai dai taji shigowar sa da fitarsa.

Sunday ne cook din Mimi yazo yace ta fa'di abunda takeso asiyo mata inji oga zaije kasuwa cefane, Ruk'ayyatu tace masa bata son komai, Sunday cikin gurbatata hausar sa yace baijin abunda take fa'di, Ruk'ayyatu duk ya bata haushi tace masa NO, Sunday sai mamakin yake yi ko bata gane mi yake nufi, wucewarsa yayi.

Sai ranar da Ruk'ayyatu ta amshi girki Abubakar yazo ko shi sai goman dare, abinci ya fara ci, sosai yaci don yunwa yake ji, bayan ya k'are, suna zaune, Ruk'ayyatu tayi shiru, Abubakar yace gobe zamuyi tafiya da Mimi, zanje London wani aiki, Ruk'ayyatu tace Allah ya kaiku lafiya.

Ruk'ayyatu ta kalli Abubakar tace yanzu kana ganin yandakayi dai-dai ne, tun kakoma gefen cen ban k'ara ganinka ba, ko nayi maka wani abun ne, Abubakar cikin b'acin rai yace ranar da ba girkin ba, dole ne sai na shigo nan,i n nazo me zan maki? Bana son k'ananen maganganu haka tsari na yake haka zanyi.

Ruk'ayyatu cikin mamaki take kallonsa tana tunanin me yayi zafi haka, hankuri ta basa ta wuce daki, Abubakar zamansa yayi falo, har dare ya fara yi kamin ya wuce ciki, akan sallaya ya samu Ruk'ayyatu, kwanciya yayi, Ruk'ayyatu bayan ta k'are ta kwanta gefen sa, ta zaci yayi baci, taji yana lalabarta.

Abubakar bayan sun natsu, ya bata hankuri yanda yayi reacting, Ruk'ayyatu cikin damuwa tace ya bari taje Gombe kamin su dawo, Abubakar yace ko ina bazata je ba, zai sa a dauko Zara daman yanada niyar hakan, Ruk'ayyatu shiru tayi, zaman Zara zaiyi a wanan gidan ko?

Abubakar yace ki shirya gobe kije ki dauko Zara, kwanciyarsa yayi, Ruk'ayyatu cike da tunani ta kwanta, bayan gari ya waye breakfast ma Abubakar baiyi gefen Ruk'ayyatu ba a wajen Mimi ya shirya suka fito zuwa airport, yaranta gidan Mumy suka je, Abubakar ya shiga gefen Ruk'ayyatu yace zasu wuce Ruk'ayyatu na kwance falo tace Allah ya tsare.

Yace gobe zaku tafi dauko Zara Ruk'ayyatu tace Allah ya kaimu, sosai taso tayi kwana biyu Dukku yak'i barinta, Mimi ce ta kirasa tana ta fa'da an fasa tafiyar ne ta koma ciki, yaje ya zauna ya barta tsaye, Abubukar hankuri ya bata gashi nan, cikin sauri ya wuce.

Ruk'ayyatu hawaye taji sun zubo mata a fuska, wanan wace irin rayuwa ce haka, *Lami'do* ta furta me yasa ka tafi ka barni?

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now