MUGUN ZALUNCI 51-52

285 14 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 51⚜52

Lokacin da Abubakar ya iso gidan Ruk'ayyatu ta fito wanka tana shafa mai, da karfi ya bude k'ofar bedroom din, Ruk'ayyatu cikin tsoro ta tashi tsaye, Abubakar masifa ya fara yi, duk yanda taso tayi masa bayani ya k'i sauraren ta.

Shiru tayi , yayi mata rantsuwa duk ta sake yi masa dambe cikin gida sai taje gidan su, don shi bazai dauki iskanci ba, tun da yake da matarsa ba'a tafa jin su ba sai da tazo gidan sa.

Imani sosai yayiwa Ruk'ayyatu yawa, ranta ya baci me mutanen nan keson maidata? cikin b'acin rai tace, ka sauraren mana, in ta fa'da maka ka sauraren kaji nawa, Abubakar cikin b'acin rai yace me zan saurara? Yan aiki sun fa'da min da k'ayar suka debi ki jikinta.

Ruk'ayyatu ganin yanda ya hau k'yale sa tayi ta cigaba da shafa Manta, idanunta sun cika da hawaye sosai ranta ya baci, Ruk'ayyatu akwai zuciya in ranta ya baci, tanada hankuri sosai, in tayi fushi ba kyau.

Abubakar fita yayi yana ta fa'da, Mimi na bangarenta ta, duk hayaniyar da Abubakar keyi ana ji, da'di taji sosai, shawara Mumy da Hajiya Batula zata dauka, sunce ta ha'da da makirci mata, Abubakar na shigowa falon Mimi ta taso tana cewa da ka k'yale ta bakayi mata magana ba, aini saboda kai ne banason mu zubar maka da girma a gaban yan aiki.

Shine ban biye mata ba, in ma nayi kure korar Zara da nayi kayi hank'uri gobe zanje makaranta su Nur in siyowa Zara form ta fara zuwa school, Abubakar duk da ransa bace yake, yaji da'din yanda Mimi tayi,  yanason Zara, yanada burin kyautata mata.

Tun daga lokacin Mimi ta shiga k'ullawa Ruk'ayyatu makirci, asirin ma basu zauna ba, su Mumy na zuwa Bargu, Malamin yayi Mimi tazo tak'i kudin da suke sakar masa, yake masu aiki sosai, Mimi tasa Zara makaranta Ruk'ayyatu bata ce masu komai ba, komai tayiwa yaranta zatayiwa Zara Indai Abubakar zai bada kudi, zama tsakanin Abubakar da Ruk'ayyatu yak'i da'di ko yaushe ganin laifinta yake yi.

Yan aiki biyu aka nemowa Ruk'ayyatu, shawara su Mumy ne zasu rik'a ganin me Ruk'ayyatu ke ciki, masu yiwa Mimi aiki suka nemo duk ba musulmai ne ba, Ruk'ayyatu tace bataso Abubakar yace tsarinsa kenen, shara, wanke-wanke da mopping sukeyi, duk abun da Ruk'ayyatu keyi zasuje su fadawa Mimi, Mimi tasha basu Laya su saka a gefen Ruk'ayyatu.

Addu'ar da takeyi Allah ke k'are ta, Mummy ce ta kira Mimi, cen bedroom ta shiga ta rufe k'ofar, Mimi cikin damuwa take fa'dawa Mumy, tayi ta k'ullawa Ruk'ayyatu makirci, sai dai Abubakar yayi fa'da yayi fushi da ita kwana biyu a shirya.

Mumy tace ta kwantar da hankalin ta zata yi tunanin abunyi.

Ruk'ayyatu na girki a kici, tafasar da nama keyi taji amai na taso mata, toilet ta wuce da sauri ta fara amai, sai da ta rufe hancin ta ida girkin, cen zuwa maraice zazafi ya rufeta, koda Abubakar ya dawo tana kwance, abinci yaci yace ta tashi suje hospital.

Suna fitowa Mimi na fitowa, cikin mamaki ta kallesa, don duk lokacin da Ruk'ayyatu zata fita driver ke kaita, yau ogan da kasan, wayyancewa tayi tace lafiya naga fuskar ki ta cenza take tambayar Ruk'ayyatu, Abubakar yace bata da lafiya zamuje hospital, Mimi tace bari muje tare, zan je gidan Mumy ne, Abubakar yace angode, Mimi gaban motar tayi saurin shigewa.

Ruk'ayyatu duk ta matsu ta zauna don Jiri take gani bayan motar ta zauna, Mimi sai famar sannu take mata, Ruk'ayyatu mamakin halin Mimi takeyi, makira k'warai ce, tana addu'ar Allah ya kareta shairin Mimi, bama abunda ke damunta irin yanda Zara ke wahala wani lokacin duk aka dauko su Makaranta tana kuka, ko in taje gefen Mimi ta korota in Abubakar bayanan.

In yana nan har daukar Zara takeyi, hospital din da suke zuwa, sukaje, gwajin farko aka gano Ruk'ayyatu nada ciki, Abubakar murna sosai yayi, yana son yara, yayi Mimi ta bar planning tak'i.

Auren sa da Ruk'ayyatu ta daina haihuwa shiru tak'i zuwa, magunguna aka bawa Ruk'ayyatu suka wuce gida, Mimi zuciyar ta har zafi take yi kan bak'in ciki, in ka kalleta da kyau kasan tana cikin damuwa.

Abubakar sai kiran yanuwansa da Abokanin yake yana masu albishir, koda suka je gida Mimi motar ta dauka ta wuce gidan Mumy, tana shiga gidan Mumy na zaune Falo ta fa'da jikinta ta fashe da kuka, Mumy cikin tashin hankali tace lafiya?

Mimi tace hospital suka je Ruk'ayyatu ciki ne da ita, Mumy ashar ta yi tace sai dai ta haifi dabba badai mutun ba, ko tsirara zanyi yawo sai Munga bayan cikinan yanda bakida Dan uba diyanki bazasu yi ba wallahi, sai lokacin Mimi taji sanyi.
**** ***

A dukku,  Maimuna cike da nasarori ta samu shiga school of Nursing a Gombe, Baffa ya matsa sai an aurad da ita akwai wani anan Dukku da yake nemanta aure, Inna tayi juyin Duniya Baffa yace bazata k'are makaranta bai aurada ita ba.

Inna Ido ta zuba masa, Adda Saudi ma taso Baffa ya bar Maimuna, Rayyan wanda ke neman Maimuna yace Inna ta kwantar da hankalin ta, bazai  hana Maimuna karatu ba, a Kaduna yake aiki, zai barta Gombe tayi karatunta.

Inna taji da'din haka, anyi tambaya har da sadaki ansa lokacin biki wata biyu, Abubukar yayiwa su Inna aikin kudi da abinci har wajen Gwanggon Lami'do Gwaggo da kukan ta, tace tabbas wata uwa ke haihuwa 'da wata uwa ke cin amfani gata tana cin arzikin Ruk'ayyatu, Dr Ibrahim ma yana yi mata aike don Faruk da Zainab.

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now