MUGUN ZALUNCI 3-4

532 29 1
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI*😡

📝 *Ummu Asma'u (Sa'adatu*)

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauki*

*Bismillahirahamanirrahim*

Page 3⚜4

*ASALIN LABARIN*

*Abubakar Bube, Baffa*, haifafen garin Dukku ne cikin jihar Gombe, Fulani ne gaba da baya, shi daya ne namiji gurin Mahaifan su, duk yan uwan sa mata ne, bayan Baffa da K'anin sa sunyi aure Mahaifin su ya rasu, kiwo shannu shine sani'ar da suka tarad Mahaifan su nayi.

Bayan Mahaifin su ya rasu aka raba gado, duk shannu ba wasu masu yawa ne ba, Baffa ya dauki nasa ya bawa yan uwan sa nasu.

Baffa da matar sa *Inna* auren saurayi da budurwa sukayi, Inna Habi sunan ta, ita ma fulanin Dukku ne, Inna fara ce sosai, kyakyawar gaske irin kyawon fulanin usuli, Baffa kyakyawa ne, bak'in bafulatani, zama ne na Fahimta tsakaninsa Inna da Baffa, tun farkon auren ta da Baffa.

Bayan rasuwar Mahaifin su Baffa, Baffa ya siyar da shanun sa ya siye gidan Mahaifin su ya biya k'anen sa mata kudin gadon gidan su, shawara Inna ce, tace ko ba komai in sunada muhali asirin su zai rufu.

Yaran Baffa shidda, Adda Saudi ce babba, sai sani na biyu Ruk'ayyatu ce ta ukku, Maimuna ce ta hudu, Bello, sai kabiru, Adda Saudi tayi aure yaranta biyar, mijin ta Fulani ne suna zaune cikin garin Gombe, ba laifi mijin ta nada rufin asiri.

Yaran Baffa, Ruk'ayyatu ce tayi farin Inna Habi sosai, Ruk'ayyatu kyakyawa gaske ce fara sosai, farin ta har ya fi na Inna, in ka ganta da su Maimuna zaka ce ba ciki daya suka kwanta ba, sai dai kamar su, su bak'aken kalar Mahaifin su, ita fara ce,duk da suma sunada kyau, duk Ruk'ayyatu ta shafe su kasancewar ta fara mace(alkibar mata).

Baffa irin bak'aken Fulani kyakyawan, duk yaran Baffa gashi ke gare su Mazan ma sai anayi ana ragewa, ko sunyi aski lokaci l ka'dan zai fito, Ruk'ayyatu gashin ta har gadon baya, haka Maimunatu, Adda Saudi ce nata baiyi tsawon nasu ba, Ruk'ayyatu nada idanu masu daukar hankali, farare sosai.
Sunada tarbiya sosai yaran Baffa, Inna Habi tsaye take sosai kan yaranta, Inna ta samu tarbiya tun gurin Mahaifan ta.

Shigar su Ruk'ayyatu makaranta ne suka fara jin hausa, duk suna gida fulatanci sukeyi, duk inda sukaje da sunyi magana daya zaa fahimci fulane don hausar tasu.

Baffa ya samu aikin gadi a gidan gonar wani Alhaji jibbo nan cikin garin Dukku ba laifi Alhaji na kyautatawa Baffa, dashi yake lalurar iyalinsa, Hadi da sana'oin mata da Inna keyi cikin gida, bayan su aurad Adda Saudi ma mijin na taimaka masu dai karfin sa.

**** ****

Baffa Bube datijjon kirki ne, duk garin Dukku kowa yasan irin dattakon sa, haka yaran sa suna tarbiya sosai, rayuwar su dai irin ta mai k'aramin karfi da wadatar zuci, Inna Habi ba abun da take so irin yaranta su samu illimin zamani.

Abun na birgeta sosai, ganin ita da maigidanta ba wanda ya samu karatun, tana ra'ayin yaranta suyi karatu, a gefen Baffa kuwa ganin yake yi ko secondary suka kare ya isa, lokacin da Adda Saudi ta kammalla secondary, sosai Inna taso tacigaba da karatun, Saudin ta nuna bata da ra'ayin yin hakan Baffa ya biye mata suka aurad da ita.

Sani ma tun daga secondary baije gaba ya fara koyon dinke tela, har kan Ruk'ayyatu wanda gara kowa da ita da k'yar ta k'are secondary, Maimuna ce mai ra'ayin karatun boko, su Bello lokacin suke primary.

**** ****

*Abubakar Sadiq Lami'do* haifafen garin *Bajoga* ne cikin Unguwar wuro biriji, Mahaifin sa bafulatani Bajoga ne, su biyu ne tal gurin Mahaifan su, Mahaifin yayi karantasuwa primary kamin yayi ritaya, ya Jima bayan auren sa da Mahaifiyar su Lami'do bai samu Hhaihuwa ba, bayan Zainab haihuwar ta dauke.

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now