MUGUN ZALUNCI 69-70

553 26 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI*😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan da ke fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 69⚜70

*LAST PAGE*

Adda Saudi tayi lalaba Ruk'ayyatu ta amince da auren Dr Ibrahim Ruk'ayyatu tak'i har fushi Adda Saudi tayi da ita, tace kina tunanin zamu baki muguwar shawara, Abubakar dinan, ke ce ke son sa, shi ya gama dake, ko kan Humaira ki diba tun da kuka rabu ya waiwayeta, duk wata hidimar ta Dr Ibrahim ne, tun lokacin da Allah ya hadaki da Dr Ibrahim yake taimakon ki.

Baffa ma yayiwa Ruk'ayyatu magana, har Gwaggon Lamido ya kira, Gwaggo tacewa Baffa bazaa yi sake da irin su Dr Ibrahim ba, samun irin su yanada wahala, ya k'ara lalafa Ruk'ayyatu, zasu tayata addu'a Allah ya zafa mata alhairi, Baffa ya samu Alhaji jibbo da maganar, Alhaji Jibbo ma yayi murna da kansa ya samu Ruk'ayyatu, bata iya ce masa aa, tace ta amince, Alhaji Jibbo sosai yayi farinciki, yace insha Allahu bazata yi dana sanin biyayyar da tayi masu ba.

Ruk'ayyatu sosai ta shiga damuwa, duk da bata son nunawa don kar Baffa yaga batayi masu biyayya ba, Gwaggon Lamido ta kirata sai albarka take saka mata, tayiwa Innarta biyayya, ko yaushe Inna cewa takeyi kar su tsallake maganar Baffan su, 'dan k'wrai shi zai yiwa iyayayen sa *Biyayya ko bayan ran su*.

Ruk'ayyatu taji natsuwa, tabbas ko yaushe Innar su na umurta su suyiwa Baffa biyayya.

Lokacin da Baffa ya kira Umman Dr Ibrahim sosai tayi murna, ta fa'da masa gobe zasu turo manya ayi tambayar aure, Dr Ibrahim ta kira tace umurnin take basa ba neman shawara ba, Dr yace yanda take son ayi haka zaayi, albarka sosai ta saka masa, tace insha Allahu bazaiyi danasani auren Ruk'ayyatu ba.

Bayan sun k'are waya Dr yayi shiru yana tunani, uwa uwa ce, badon mahafiya ce ba, bazai auri matar da Abubukar ya saka ba, hannuwansa ya 'daga sama ya rok'i Allah ya sanya wanan auren ya zame masa alhairi, yanda yayiwa majaifiyarsa Biyayya Allah yasa yaransa sunyi masa hakan.

K'anen Mahaifin Dr sunje neman aure an basu sun biya sadaki, an anje ranar Jumma'a mai zuwa zaa daura aure, tun da maganar auren ya taso Dr bai k'ara kiran Ruk'ayyatu ba, ita ma bata k'ara neman sa ba, ya tura mata kudi a acct din ta, tana son kiransa tayi masa godiya tana jin nauyin, ko yaushe ta zauna tunanin takeyi yanda zasuyi rayuwar aure da Dr.

**** ****

Umman su Najib da kanta ta kira Najib tace yazo suje su rok'i Baffa ya taimaka masu a maida auren sa da Maimuna, tayi kure abun da tayiwa Maimuna, baa kwana Najib yazo Gombe cike da farinciki, tsaraba sosai yayiwa Umman sa, taji da'di sosai ta rok'esa ya yafe mata.

Dangin Mahaifin Najib din ta nema suma sun da'din da tagane gaskiya, Dukku suka wuce Baffa na gida suka same sa, Baffa yayi shiru da yaji me ke tafe dasu, Umman Najib sai hank'uri take basa, don ta matsa sai sunzo ta rok'i Baffa, Baffa Maimuna ya kira yace yaji ra'ayin ta, Maimuna ta duk'ar da kanta k'asa tace Baffa duk yanda kace haka zaa yi.

Baffa ya kira Alhaji Jibbo, Alhaji Jibbo yace tunda ta gane kurenta babu matsala ko don yarinyar dake tsakanin su, sun bari ta koma, Baffa yace sun amince ta koma, sun rok'i arzikin a maida auren, makwabta Baffa ya kira aka maida auren Maimuna da Najib, Adda Saudi sai murna takeyi da Ruk'ayyatu.

An aje bayan kwana biyu Najib zai zo ya dauki Maimuna, Umman sa tace komai kar Baffa yayi, Najib din zai siyawa matarsa komai, Baffa yayi murmushi yace angode, suka rabu cikin farin ciki.

**** ****

Lokacin da result din gwajin da akayiwa Mimi ya fito, likitan Abubakar ya nema yana son ganin sa office din sa, Abubakar na police station kiran likitan ya shigo don ya karfi num sa hanun Mimi.

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now