MUGUN ZALUNCI 41-42

296 18 2
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Wattpad Bachaka uwani Sa'adatu(Uwani Bachaka*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 41⚜42

Bayan kwanaki biyar, a ciki kwanaki biyar Ruk'ayyatu ta fahimci akwai raunin addini sosai a Abubakar, ga son bariki, Abubakar ma a cikin kwanaki biyar ya fahimci Ruk'ayyatu nada rashin wayewa, har mamakin yakeyi ance tayi secondary school, amman ya fahimci ba wani turanci take ji ba, a cikin kwanakin kowa da irin kallon da yake yiwa wani.

Abubakar sosai yake son Ruk'ayyatu, yana samu gamsuwa sosai da ita, sai dai rashin wayewar, ya sha alwashin zai rabu da dukkan yan matan da yake tare dasu, yasan ko ba Mimi Ruk'ayyatu na biya masa buk'atar sa, Ruk'ayyatu sosai take girmama Abubakar komai nasa yanada muhimmaci a wajen ta.

Abubakar ma yana jin da'din hakan don yasan zaman sa da Mimi bai samu hakan ba.

Ruk'ayyatu da Abubakar zaune falo suna kallo, Abubakar ya tashi da karfi har Ruk'ayyatu ta tsorata cikin mamaki tace lafiya, dakin ya wuce ya fito cikin shirin tafiya, yace mata zaije Abuja, zuwa gobe ko jibi zai dawo, Ruk'ayyatu cike da mamaki tace Allah ya tsare hanya.

Kallonta yayi yace ba rakiya? wajen gidan ta rakasa rumgumeta yayi yace take care sai na dawo, akwai kudi a daki, zan kira Bala driver duk abunda kikeso, Ruk'ayyatu tace Allah ya tsare hanya, Abubakar ya fita get din gidan yayi da sauri.

Ruk'ayyatu cikin gidan ta wuce tana tunanin lafiyar sa, jiya yace mata saura ka'dan a gama gyaran inda zata zauna, kafarsa kafarta, zasu koma Abuja, har tashiga falon tunanin takeyi sai da Larai yaruwar ta tace Anty lafiya?

Ruk'ayyatu tace ba komai, Abubakar ne ya wuce Abuja, Larai tace Allah ya kaisa lafiya, Ruk'ayyatu tace ameen.

Abubakar gudu yake yi sosai, Mimi yakeson ganin, zaije ya rok'i su yafe masa, ya ma akayi yayiwa Mimin sa haka, Allah ne yakai Abubakar Abuja lafiya, gidan su Mimi ya wuce, suna zaune Falo  ita da Mumy, duk abu ya dame su Malan yace kwanaki biyu gashi har anyi biyar.

Sallamar Abubukar ce ta hana Mumy maganar da zatayi, Mumy hamdala tayi a ranta, Abubakar na shigowa gaban Mimi ya zube yace ki yafe min nayi  nadamar abun da nayi maki, Mimi tashi tayi ta wuce cikin gidan Abubakar binta yayi yana rok'onta, Mumy shewa tayi tace Dan iska ashe kai k'aramin shege ne, Hajiya Batula ta kira, sai dariya suke yi, Mumy tace gashicen ya bita daki

Hajiya Batula tace kuyi kokari yaci maganin da Malan ya bada, sallama suka yi ,Mumy sai murna takeyi, Mimi falo ta dawo Abubakar na biyar ta, Dady ne ya shigo falon ya dawo cikin gari, Abubukar gaishe sa yayi yana k'ara basu hank'uri, Dady yace Mimi tayi hankuri ta koma dakin ta.

Daddy Mumy ya Kalla yace kuyi hankuri Balki, Mumy tace yaje zata dawo Abubakar zubewa gaban Mumy yayi yace Mumy muje tare mana, nasa yan aikin su gyara gidan, Abubakar zaune yayi masu, sai da Mimi ta ha'da kayan ta suka wuce gida a dare.

Mimi ranar kudi sosai ta amsa hannun Abubakar, sai bayan sunje gida yaga miscall din Ruk'ayyatu don ya bar wayarsa a mota da zai shiga gidan su Mimi, waje ya fita ya kirata, Mimi ce a gabansa, amman yanaji yayi kewar Ruk'ayyatu, gaishe sa tayi cike da ladabi, hankuri ya bata yace baya kusa ga wayar, amman kar ta kira yana aiki in ya natsue zai kirata, kashe wayar yayi ya koma wajen Mimi.

Yanda ta saba haka tayi duk zai tara da ita sai yayi rok'on ta, da safe ma abinci yan aiki suka girka Mimi na cen na bacci, office ya wuce, har yammah bai kira Ruk'ayyatu ba, boyar Allah tana son kiransa gasa yace kar ta kira, sai dare Abubakar ya koma gida, Mimi bata gidan ta fita wanka yayi yaci abincin ka'dan, Ruk'ayyatu ya kira, suna magana yaji tsayawar motar Mimi yace zai kirata ya kashe wayar.

Kiran Dr Ibrahim ne ya shigo, bayan sun gaisa Abubakar yace yana gari ya dawo da Mimi Dr mamaki yayi yace baka kirani ba, Abubakar yace zamuyi magana an jima ya kashe wayar lokacin Mimi ta shigo falon.

Sannu da zuwa Abubakar yayi mata, zama tayi tace nagaji sobo ta fisuwa cikin leader tace gidan Mumy tayi na dauko maka, cup ta kawo ta zuba masa,amsa yayi yace Mumy tasan ina son zobe, sha ya fara yi, ba bismila, Mimi murmushi tayi ta wuce daki.

Dr Ibrahim Alhaji Mansur ya kira yana fa'da masa Abubakar ya dawo har ya mayar da Mimi, Alhaji sallati ya fara yi, Dr Ibrahim ya rok'i Alhaji da yasa Abubakar ya dawo da Ruk'ayyatu Abuja in ba hakan yasan auren zai iya lalacewa.

Alhaji Mansur yace ba matsala, kaima Dr sai kasa baki, insha Allahu zata dawo Abujan.

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now