MUGUN ZALUNCI 25-26

265 16 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan shafin ga duk Matan da suka rasa mazajen su, Allah yayi masu Rahama, Allah ya ha'da su da Abokanin rayuwa nagari*

*Anty Nice ina maki fatan alhairi, kalma bazata iya nuna godiyar mu a gunki ba*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 25⚜26

Cikin kidemewa Baffa ya karfi wayar hannun Inna jikinsa sai rawa yake yi, Dan sandan yayi masa bayanin tirela ce ta kwancewa driven ta isko motar Faruk duk Allah yayi masu cikawa har mutun biyu dake cikin tirelar.

Baffa sunan Allah yake fa'di idanunsa na zubar da hawaye, ya fa'dawa Dan sandan gasu nan zuwa, sai da yayi sallama da Dan sandan idanunsa su ka kai kan Ruk'ayyatu dake zube, Inna ma lokacin hankalin ta yakai kan Ruk'ayyatu.

Ruwa Inna ta debo ta yayyafa mata ajiyar zuciya ta sauke, tana kuka mai tafa zuciya wanan wane irin masifa ce, duk wanda ke taimakon ta rayuwa shi take rasawa. Baffa jiki sanyaye ya kira K'anin Mahaifin su Lami'do ya fa'da masa abun da ya faru, Baba Malan kansa abin ya girgiza sa ya tausayawa Gwaggo ta rasa yaranta lokaci daya, rasuwar Lami'do ma baa jima ba.

K'anin Gwaggo kawu Bala Baba Malan ya kira, kawun ma abun ya tsorata shi, haduwa sukayi da Baffa a hanya suka wuce inda hatsarin ya faru, koda suka isa yan sandan su kira ambulance asibitin Dukk aka wuce don yafi kusa.

Zainab suka fara diba cikin ta ba alamun rayuwa, Faruk ma ya Jima da cika don a kai ya bugu, Bajoga suka wuce kowa na tunanin yanda zaa yi da Gwaggo, Inna Rabi suka fara fa'dawa Inna Rabi kuka ta fasa, Gwaggo na daki kwance ta fito, kukan tasa don tasan dole wani babban abu ya faru.

Makwabcin su Gwaggo ne ya shigo gidan, bai san basu fa'dawa Gwaggo ya fara yi mata gaisuwa da kawo mata ayoyin  Qur'ani akan hankuri, Gwaggo cikin mamaki tace wace *Zainab da Faruk*?

Alhaji na ganin haka ya tashi yayi waje, Gwaggo kuka ta fasa ta zube k'asa, tana kiran sunan Allah, cikin kuka take fadin Allah na gode maka, kai kade ka iya yiwa bawa haka, Allah kai ka bani ka amsa kar ka barni ga dubura kai na, Allah ka shige min gaba.

Arwalla tayi ta shiga daki, Inna Rabi zaune tayi tana kuka sosai, ta tausayawa Gwaggo, Gwaggo boyar Allah ce, ganin yanda Gwaggo tayi ita ma arwallar tayi tafara sallati.

Mahaifin Faruk su Baba Malan suka kira shima rasuwar ta girgiza, don sunyi waya da Faruk yace suna hanya Dukku zasu fara biyawa, yan gidan su Faruk sai kuka sukeyi sosai, don Faruk mutun ne mai son yanuwansa.

Su Inna' Ruk'ayyatu, Adda Saudi duk sun iso gidan Gwaggo, Gwaggo na ganin Zara lokacin ta k'ara fasa kuka, tace Zara bayan rasuwar Mahaifin ki, yau kin k'ara rasa gata, Allah ya zama gatanki Zara, Ruk'ayyatu Gwaggo ta Kalla, tace kiyi hankuri Ruk'ayyatu tabbas yau kun rasa, kiyi hankuri da wanan jarrabawar, Inna kallon Gwaggo takeyi tana nazarin ta wanan surutun duk na rudewa ce.

Ruk'ayyatu ta zauna kusa ga Gwaggo ta fashe da kuka, duk dakin kuka sukeyi, gidan su Faruk aka wuce da gawar Zainab da Faruk din cen akayi masu sutura aka wuce dasu mak'abarta.

Sai bayan an dawo mutane suka shiga wajen Gwaggo, Gwaggo boyar Allah sai hank'uri take ba Ruk'ayyatu da har lokacin kuka takeyi.

Sai da akayi kwana ukku Ruk'ayyatu ta tuno bata fa'dawa Dr Ibrahim ba, ta kira wayar kashe lokacin yana tiyata, text tayi masa, bayan ya kunna wayar yaga text dinta, a tsorace ya kirata, Ruk'ayyatu tana masa bayani kuka yaci karfinta.

Dr Ibrahim kashe wayar yayi ya zauna yana zubar da hawaye, rayuwa bata da tabbas, tabbas Allah baya bari wani don wani yaji da'di, Ruk'ayyatu tayi rashin mai taimakon ta, Gwaggo ya tuno don lokacin rasuwar Lami'do Faruk yace masa Zainab dai ta rage mata, wanan mata taga jarabbawa, gida ya wuce ya shirya zuwa Bajoga.
**** ****

Da k'yar Mumy ta yardar Mimi ta koma gidan Abubakar, sai da suka garasa son ransu, Daddyn su Mimi da yayiwa Mumy magana cikinsa tayi tace baisan darajar 'yarsa ba, shiru yayi don bayada magana sai wadda Mumy tayi.

Ranar da Mimi ta koma Abubakar murna baa magana duk da tsowon kwanaki da tayi gidan su, Abubakar ya daukarwa Jamcy daki a hotel sabuwar yarinyar da yayi, Abubakar mabuk'aci ne sosai Mimi ta kasa gane hakan.

Sai dare Abokanin Mumy suka rakata, Abubakar dubu dari ya basu su sha mai, Mumy da Mimi sun amshi kudi hanunsa sunfi milion biyar duk da sunan shirin komawa gidan sa.

Dangin Abubakar duk sun saka masa Ido, gidan yayansa ya daina zuwa bamai zuwa gidan sa, sai masu shiri da Mimi, wanda ke zuwa tana wulak'antawa suna mata bauta wani mugun tsoron Mimi yakeyi komai tace an kare, haka suke zaman rayuwar kaf turancin, yaran Mimi ko Islamiya basa zuwa, Malami aka samo gida in yazo sai sunga dama suke zama karatun.

Turancin kamar yaran America ko a gida baa masu hausa, bayan kwana biyu Mimi tacewa Mumy kamar Abubakar har yanzun yana neman mata, Mumy tace su shirya su koma Bargun wajen Malan.

Munnawara taji sauk'i sai dai ba magana, yayan Abubakar da matarsa zuwan su biyu Maiduguri, duk suka dawo zai kira Abubakar waya sai yak'i dauka.

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

08182654508

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now