MUGUN ZALUNCI 7-8

347 18 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

    📝 *Ummu Asma'u (Sa'adatu)*

*Nah Sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar Aure, Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 7⚜8

Soyayya sosai tsananin Mimi da Abubakar, sai dai baya zuwa gidan su, Mumy tak'i amincewa, nata ganin me Mimi zata tsinta cikin auren Abubakar din, guri sosai tasawa auren Mimi.

Mimi tayi juyin duniya Mumy tak'i amincewa, lokacin Mahaifin su Mimi yaje London baya nan, Mimi kuka sosai takeyi duk ta shiga damuwa don Abubakar akwai tsari, irin kallaman soyyayar da yake fa'dawa Mimi, duk ta haukace, irin mijin da takeso kenan.

A haka Daddyn su Mimi ya dawo, Mimi bata bari aka kwana ta fa'da masa duk da ja mata kunne da Mumy tayi kar Daddy yaji maganar, akwai yaron mataimakin shugaban k'asa da sukayi da k'awar ta zata ha'da Mimi da shi, shine duk hankalin Mumy ya tashi.

Mimi ta fa'dawa Daddy abun da ke faruwa yace ta kwantar da hankalin wanda takeso shi zata aura, murna sosai tayi ta wuce dakin ta, lokacin Mumy na wanka.

Daddy komai bai cewa Mumy ba, bincike yasa aka yi masa kan Abubakar ganin yanada aikin yi, yasan tsohon Minister yayan sa, yace Mimi ta fa'da masa ya turo magabatansa, lokacin da ya fa'dawa Mumy ranta ya baci sosai, fa'da tayi ta yi, an maidata banza har zaa ce ya turo bata sani ba.

Sai da Daddy ya ha'da ta da Mahaifiyarta ta yarda ko shi don ba yanda zatayi, biki sosai akayi Amarya ta tare gidan ta, sosai sukayi hidima dangin ango, Mumy duk bata ga sunyi ba, haushin Abubakar sosai take ji, bayan auren duk sukazo gidan tashi take yi ta shige ciki.

Har Mimi tayi haihuwar farin sunan Mumy yasa, duk don k'iyaryar ta rage, bayan haihuwar Nur 'diyar Mimi matsalolin suka fara taso, ko ka'dan Mimi komai bata yi sai yan aiki, tun farko Abubakar ya fara damuwa ganin cikin da ta samu yake ganin in ta haihu zata cenza.

Sai gashi bayan haihuwar komai ya lalace,  in yayi magana tayi fushi, in ta fa'dawa Mumy, tace kar tayi ai ba baiwa suka kai masa ba, Abubakar tun yana k'aramin yake sha'awar siyasa, tun university yayi SUG president, ogan shi a office yayi ritaya ya shiga siyasa shima Dan Gombe ne, Abubukar ma ya shiga siyasar, cikin sa'a aka tsaida shi takara dan majalisa mai wakiltar Dukku, cike da nasara Abubakar yaci zafen.

Likafa taci gaba su Mimi, sai dai matsala ce sosai tsananin ta da abubakar kan haka har ya fara neman mata da kuma shairin shegiya naira yayi ta neman aure Mumy na shiga tana watse auren, don bayan yaci dan majalisa ta fara amsa gaisuwar sa, ranar da Mimi tazo gida tana kuka Abubakar yace zaiyi aure, ranar hankalin Mumy ya tashi.

Wajen Malamin taje, don akwai lokacin da suka samu sabani da Daddy wata k'awar  ta ha'da da Malamin tun lokaci Daddy ko gaddama baiyi mata, asiri sosai sukayi Abubakar duk laifin Mimi da yake gani ya daina sai dai yana neman matan sa, maganar aure babu ita.

Mimin ta sani, tasha ganin comdom a kayan sa in yayi tafiya, ta fa'dawa Mumy tace gara yaje ya nemi matan kan ayi mata kishiya, sunyi masa asiri kan neman matan abun baiyi ba, kudi sosai yake basu, rayuwa irin ta turawa duk yan aikin Mimi basa jin hausa, abincin gidan Sunday ke dafawa, su blessing ke shara da wanke -wanke, lokacin yaran Mimi biyu.

*Labarin Mimi da Abubukar kenan*

Ranar Mimi cikin wani yanayi ta yini, bak'in kishiya ke cinta, Abubakar sai karfe shabiyu  daren ya dawo gida, Mimi na zaune falo ya shigo, kamin tace komai ya fara kawo mata uziri, haka suke ko yaushe, wanka yayi yaci abincin ka'dan don kar tace bai ci ba.

Yasan yan aikin suka girka, dakin sa suka wuce, Mimi duk kok'arin kar hawaye su zoba sai da Abubakar ya gane, rarashin ta ya fara, yace ta fa'di abun da take so, kudi ne ko yaushe ta nema, transfer yayi mata, ya rungumeta suka kwanta,  Mimi kwana tayi da tunanin gobe zata kaiwa Mumy kudin a k'ara Sabon aiki.

**** ****

Amarya Ruk'ayyatu zama yayi da'di tsakaninta da Lami'do, zama ne na Fahimta, sosai take girmama sa da Mahaifan sa, sun k'ara shak'uwa da Zainab, Nafisa tana yawan zuwa gidan.

Komai Lami'do yiwa Ruk'ayyatu yake yi, duk lokacin da sukayi waya da Inna takan ce mata tayi kokari ta koma makaranta, yafi zama hakan, ko ta nemi sani'ar yi.

Lami'do na makarantar dayake aiki, aka turo masa text yazo interview, yayi apply aiki a INEC, cikin jin da'di ya wuce gida, Ruk'ayyatu na falo kwance ya shigo falon daukar ta yayi suka fara Zagayar falon.

Bayan ya sauke ya fara bata labarin, murna sosai tayi, da gari ya waye Abubakar yayi samakon zuwa Gombe, cikin nasara ya samu aiki da INEC nan Gombe akayi posting din sa, da farko weekend yake zuwa a Bajoga, da baya ya samu hayar gida ya dauki Ruk'ayyatu suka wuce Gombe.

Gata ba wanda Abubakar baiyiwa Ruk'ayyatu ba, duk ayi salari zai yi mata Sabon dinki, abinci komai siyowa yake yi, duk karshen wata suke zuwa diba iyayen Abubakar wani lokacin har Dukku suke zuwa.

Wani zuwa Inna tayiwa Abubakar maganar karatun Ruk'ayyatu, bayan sun koma Gombe ya siyowa Ruk'ayyatu form din poly, result din na Secondary ya amso mata a Dukku, Ruk'ayyatu na ganin form ta matsi fuska, tashi tayi ta wuce kicin, Lami'do yayi juyin duniya Ruk'ayyatu tace baza iya ba.

Inna ya kira yayi mata bayanin yanda sukayi da Ruk'ayyatu don bayason taga kamar shine baiso, Inna kiranta tayi, tayi ta lalashin Ruk'ayyatu, shiru Ruk'ayyatu tayi, haka sukayi ta lalafa ta, karshe Lami'do ya fahimci Ruk'ayyatu bazata iya ba.

Wani form yazo dasu gida na office din su,  yace ta cika masa, yana fa'da mata abun da zata rubuta, duk bata rubuta dai-dai ba, shiru yayi yana mamakin daman matsalar kenen, tun lokacin bai k'ara damun ta da Maganar makaranta ba, ya kudurci zai nema mata kasuwancin yi, ko don yanda Inna ta damu.

Matsalar ciwon Suga ya damu Mahaifin sa, duk maganin  abinci shike siye wani lokacin koda zaa yi albashi matse yake, cikin hakan komai Ruk'ayyatu takeso zaiyi mata ko yaya ne.

Mutanen cikin compound din gidan har gulmar suke yi,  yanda Abubakar kema Ruk'ayyatu, Ruk'ayyatu ma komai Abubakar Lami'do keso shi takeyi, tun zaman su basu tafa fa'da ba, in Abubakar baya office yana gida.

Wani lokacin da yamma fita sukeyi suyi yawo a unguwa ko suje Park su sha iska, abinci wani lokacin shikeyi, matan gidan har leken sa sukeyi, Ruk'ayyatu tayi fari ta yi k'iba ka'dan

Wanan jin da'din zai dore Ruk'ayyatu

Muje zuwa

*Ummu Asma'u (Sa'adatu*)

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now