MUGUN ZALUNCI 57-58

281 16 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Masu korafi akan halin da Ruk'ayyatu ke ciki, wasu suna ganin abun yayi yawa, wasu suna kirana in tausaya mata, labarin Ruk'ayyatu, almost true event ne, so dayawa rayuwar wani zatazo da jarrabawa ire-ire, wani tasa rayuwar kamar shi ya tsurawa kansa, duk rayuwa tana tattare da jarrabawa daban-daban, ya Allah ka bamu ikon cinye Jarrabawar rayuwar mu, ka sadamu da alhairinka ya rabbi, masu k'orafi pls, sunan littafinan MUGUN ZALUNCI*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Scorpion* ya kalli Hajiya Batula yace Hajiya ku bani lokaci in shiryawa aikin ku, kisan ha'darin aikin irin wanan sai an shirya masa, sai na nemi sa'a gurin Malami na, inma inada Malamin da nake neman taimako wajen sa.

Hajiya Batula tace shikenan zamu jiraka, Mumy duk ba haka taso ba, dole ta hank'ura da hakan suka wuce, Mimi ma taji haushi sosai, ta matsu Ruk'ayyatu ta bar gidan, duk wani asiri sunyi ko an samu matsala zasu shirya.

*Scopion* ainihin sunan sa Rabi'u Muhammad, Mahaifin sa haifafen garin zaria ne zama ya kawo su cikin garin Kaduna Malan Muhammad Bawan Allah ne, shike bada sallah a Unguwar su, scopion Sam baiyi halin Mahaifin sa ba tun yana yaro.

Shi daya ne Namiji wajen Malan yayunsa duka mata ne, bak'in cikin scopion ya kashe Malan kan halin scopion har takai Malan baya fita waje sai mutanen Unguwar su, sun nuna sa.

Duk wata sata a Unguwar scopion ne, kajin ne cikin Unguwa, fasa shagunan unguwa, karshe scopion ya tattara ya koma *Tafa garin shege da shegiya inkaga Dan halas bak'o ne* komawarsa tafa iskanci yayi yawa.

Daga Tafa ya shiga Abuja, a Abuja ya hadu da Hajiya Batula, duk wani mugun aiki Scopion zai iya yinsa Indai zaa bashi kudi, baida tsoro ko ka'dan, sai shege-shegen Malamin tsibo duk abun da zaiyi sai ya nemi sa'a

Bayan wasu wattani zaman Maimuna da uwar mijin abin yak'i da'di sosai Mahaifiyar Najib ta tsani Maimuna har ta kai Najib ya fara daukar maganar ta, sosai Maimuna ta rame ga ciki haihuwa ko wane lokaci.

Lokacin da cikin Maimuna ya shiga watan haihuwa ta koma gida, sati biyu da komawar ta, ta haifi kyakyawar yarinyar ta, tun da ta haihu ba danuwa Najib da yazo, Najib din ma baizo ba sai wasu friends din sa, sosai Baffa ya shiga damuwa, haka akayi sunan aka sawa yarinya sunan Mahaifiyar Najib, ranar da akayi suna ranar Najib ya turowa Maimuna text din saki, bisa umurnin Mahaifiyarsa.

Ruk'ayyatu ana gobe suna tazo, lokacin da Maimuna ta nuna masu text din kuka sukayi sosai, wanan wulak'ancin yayi yawa, Baffa ya shiga damuwa sosai, jini sa ya hau, tun lokacin rasuwa Inna hawan jini ya shige sa.

Baffa ya fa'dawa Alhaji Jibbo abun dake faruwa da Maimuna, Alhajin da kansa ya samu K'anin Mahaifin Najib, hankuri yaba Alhaji Jibbo, yace Mahaifiyar su Najib matsala ke gareta, duk irin haka ta faru ko yayi mata magana bataji, tun Mahaifin su Najib na raye hankuri yake yi da ita.

Alhaji Jibbo abun ya yi masa ciwo, yasan dole Baffa ya shiga damuwa ga rashin Inna, kwashe kayan Maimuna akayi ta dawo gida, Adda Saudi ma ta shiga damuwa.

Ranar wata jumma'a, Scopion ya kira Hajiya Batula yace ya shirya, Mumy ta kira suka kira Mimi, Mimi ta kira cikin yan aikin Ruk'ayyatu da masu aikin Mimin ne suka kawo su gidan, wani magani suka ba yar aikin ta zubawa Ruk'ayyatu a abinci.

Ruk'ayyatu bata San abun da suke shiryawa, har bayan magrib, Ruk'ayyatu nason fura sosai, tana ajiye fura a fridge, fura yar aikin ta rage ta zuba magana don tasan Ruk'ayyatu nashan fura ta bar abinci.

Ruk'ayyatu bayan ta k'are sallar isha'e ta dauko fura, tasha sosai, tana zaune falo ta fara jin bacci Zara da Aisha ta dauka da suka riga sukayi bacci ta kaisu bedroom, ta kwanta cikin kank'ani lokaci wani nauyayen bacci ya dauke ta.

Wajen shabiyun dare Mimi ta tada Abubakar tace taji motsi bayan gefen ta, Abubakar cikin bacci yace masu gadi fa, Mimi matsawa tayi ya tashi, tashi yayi suka fito waje, k'ofar gefen Ruk'ayyatu a bude, cikin sauri Abubakar ya wuce har falon duka bude.

Bedroom din ya wuce, Ruk'ayyatu kwance, scopion na gefenta, su Zata da Aisha kwance kasan cafet din tsakiyar Bedroom din, Abubakar fita yayi yana ihun kiran masu gadin, Mimi da sauri ta budewa scopion k'ofar kicin ya fita, daman ta shirya masa yanda zai fita gidan.

Bayan scopion ya fita Mimi ta bi Abubakar tana ihun kiran masu gadin bacci suke sosai, har police dog din gidan bacci sukeyi an saka masu magani cikin abinci.

Abubakar zaune yayi yana kuka da hawaye, yana jin mugun tsanar Ruk'ayyatu.

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now