MUGUN ZALUNCI 23-24

274 15 1
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 23⚜24

Mahaifin Munnawara na gurin aiki aka kira sa, lokacin da yazo gidan yaga halin da Munnawara take ciki sosai hankalin sa ya tashi asibiti suka wuce da ita, tsawon awani ba sauk'i, kakan su Munnawara wanda ya haifi Umman su yazo asibiti yana ganin yanayin Munnawara yace su koma gida.

Gida suka wuce, ya fa'dawa Abban su Munnawara asiri ne aka yiwa jikanyarsa, zai kira wani amininsa Malami ne sosai yanada illimi kan irin wayyanen matsalolin, baa dauki lokaci ba Malamin yazo bayan ya diba Munnawara ya fa'da masu asiri ne, wanda aka zuba a ruwa zaa yi amfani da Qu'ran a karya shi, a hankali zata samu lafiya.

Mahaifin Munnawara cikin tashin hankali yace wazai yiwa 'yar sa wannan aikin, Malamin yace Allah masani ko waye watarana zai ga abun sa, yanzun nemawa Munnawara lafiya ne muhimmin abun.

Addu'a sosai aka farayiwa Munnawara, saukar Qur'ani da sadaka, Umma ta mance da maganar Abubakar, kiransa waya da tayi ya kashe, damuwarsu lokacin lafiyar Munnawara.

Tsawon kwanaki biyu ana Abu daya Munnawara taji sauk'i sosai sai dai har lokacin bata koma kamar lokacin da take lafiya lau ba, Malami yace a hankali zata samu lafiya, ciwo keyi gaba daya

Bayan Munnawara ta farajin saukin Abban Munnawara ya kira, yayan Abubakar, yace zasu 'daga bikin har 'yar su ta k'ara jin sauk'i, Alhaji yayan Abubakar yayi shiru yana mamakin batada lafiya ne? tambayar Abban yayi batada lafiya ne? Abba ya kwashe duk abunda ya faru ya fa'dawa yayan Abubakar.

Ran Alhaji Mansur ya baci sosai me ke damun Abubakar wanan ai k'aranta ce, jiya yazo masa da zancen ya fasa auren, yayi masa fa'da yace duk dukiyar da ya kai, mutanen zasu kalle su k'ananen mutane masu magana biyu.

Jin halin da Munnawara take cikin ran Alhaji Mansur ya baci yace don lalura ta samu yarinyar mutane zai gujeta, ya bawa Abban hankuri ya fa'da masa sa, basu San halin da ake ciki ba, yace gobe zasu zo su diba Munnawara.

Bayan sunyi sallama Alhaji Mansur ya kira Abubakar, lokacin yana zaune gaban Mumy sai kace mai neman gaffara, tsawon kwanaki biyu suna jamasa rai, Dadyn su Mimi yace magana na hannun Mumy, duk yanda tace.

Komai na gidan Mumy ke yanke hankuci haka yake kamar rak'umi da akalla, kiran Alhaji Mansur ne ya shigo wayar Abubakar rejecting call din yayi, Alhaji Mansur ya dade rik'e da wayar yana mamakin, ko metting Abubakar keyi ya kirasa zai amsa in shi Alhaji  din yaji alamun yana magana sai ya kashe.

Sai bayan Abubakar ya fita gidan su Mimi ya kira Alhaji Mansur, Alhajin fa'da sosai yayi masa na rashin fa'da masa halin da Munnawara take ciki, Abubakar ko a jikin sa hali da Munnawara take ciki, cewa Alhaji Mansur din yayi gobe zasuyi tafiya da speaker din su bazai samu zuwa ba, shi fa ya fasa auren.

Ya kashe waya, Alhaji Mansur, Dr Ibrahim ya kira yazo yana nemansa, Dr Ibrahim gidan ya wuce yana ganin girman Alhaji Mansur sosai, Dr Ibrahim ya jinjina lamarin bayan Alhaji Mansur yayi masa bayani, me ke faruwa da Abubukar ne, hankuri yaba Alhaji Mansur yace zai masa magana.

Dr Ibrahim kiran Abubakar yayi yace masa yana hanyar gidan sa, juyin duniya Dr Ibrahim yayi Abubakar yaje Maiduguri yace bazaije ba ya fasa auren, Dr Ibrahim cikin fushi ya fita gidan har rasuwar Lami'do yaso ya fa'da masa b'acin rai yasa baice masa komai ya wuce.

Abubakar cewa yayi Allah raka taki gona, duk mai fushi yayi Indai Mimin sa zata dawo gidansa, wani mahaukacin sonta yake ji cikin ransa.

**** ****

Ruk'ayyatu ta fara zuwa Islamiya ba laifi damuwar ta rage, wani lokacin zama takeyi tayi ta kuka, har in ta kalli halin da suke ciki gidan, duk da Baffa na kokari gurin kyakyata masu, Adda Saudi ma tana kok'arin ganin ta rage wasu lalurorin yaranta.

Jarin Inna yayi k'asa sosai yau a dauka gobe a dauka, Ruk'ayyatu tace ta k'ara da kudin su dake hannun ta.

Ranar Jumma'a Faruk ya kira Ruk'ayyatu yace suna hanya zai maida Zainab gida ta damu wajen su Gwaggo zata haihu don watan ta ya tsaya, ya tambayi Ruk'ayyatu me suke buk'ata tace ba komai, Zainab ce ta amshi wayar tace zurfin cikin ki yayi yawa, in bakiso kar ki cuci Zara, kayan tea da Pampers duk an siyo mata, Ruk'ayyatu murmushi tayi tace Allah ya kawo ku lafiya.

Zainab tace ameen ta Dukku zamu fara tsayawa, Ruk'ayyatu tashi tayi tana fa'dawa Inna, Inna tace asiyo nama a dora masu abinci, abinci suka dora.

Ruk'ayyatu na zaune taji gabanta ya fa'di, sunan Allah ta kira Inna tace lafiya, Ruk'ayyatu tace ba komai Inna jin nayi gaba na faduwa , jikina banjin da'din sa.

Wayar Ruk'ayyatu dake gefe ta fara ringin cikin sauri ta dauka tana cewa Inna Zainab in ba taga Zara bazata barni lafiya tun dazu take damuna Zara ta k'ara girma, kamin Inna tayi magana Ruk'ayyatu ta amsa wayar.

Murya wani taji yana fadin yan Sada ne daga hanyar shigowa Dukku masu wanan wayar sunyi hatsari, kamar mata da miji ne duk Allah ya amshi rayuwar su.

Ruk'ayyatu ihu ta k'urma ta zube k'asa a sume, Inna cikin sauri tayo kan Ruk'ayyatu tana kiran sunen ta, wayar ta dauka, har lokacin Dansandar magana yake yi, Inna kuka ta fashe dashi cikin tashin hankali tace FARUK DA ZAINAB.

Baffa ya fito da sauri yana tambayar Inna me ya same su tace sun rasu Baffa ma zama yayi yana sallati.

Muje zuwa

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now