MUGUN ZALUNCI 13-14

325 20 0
                                    

😡  *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u (Sa'adatu)*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure, Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 13⚜14

*Bayan wattani Tara*

Duk wani shire-shiren haihuwa Lami'do yayi, dai-dai karfin sa, komai ya siya, Ruk'ayyatu cikin ya tsufa haihuwa kowane lokaci.

Inna taso a mayar da Ruk'ayyatu Dukku ta haihu gaban su, Gwaggo Mahaifiyar Lami'do tayi tsaye a wajenta zaa haihu, Lami'do Bajoga ya mayar da Ruk'ayyatu duk da yaso sai ta haihun a Gombe, Gwaggo tak'i.

Bayan kwanaki ukku da komawar Ruk'ayyatu a Bajoga, ranar Jumma'a ta tashi da labour, Ruk'ayyatu kin fa'dawa Gwaggo tayi, Gwaggo ce ta fahimci halin da take ciki, Faruk ta kira, don ko yaushe Lami'do ya kira rok'on Gwaggo yake yi, in lokacin yayi suje asibiti kar a barta gida.

Cikin kank'ani lokaci Faruk yazo suka wuce asibiti, koda suka isa asibitin Ruk'ayyatu taji jiki sosai, labour room aka wuce da ita, cikin taimakon Allah bata da'de ta haifi kyakyawar yarinya jajir da ita.

Lokacin da Nurse ta fito tana fa'dawa Gwaggo an haihu, hannuwanta ta'daga sama tanayiwa Allah godiya cike da murna da farinciki, Lami'do  Faruk ya kira, cikin tsananin farinciki yace yana hanya.

Su Inna Gwaggo ta kira tana masu albashir, murna sosai sukayi, ba'a sallami su Ruk'ayyatu daga asibiti Lami'do yazo, Ido ya tsurawa yarinyar yana kallo, kamar sa sak, farin ta ne na Ruk'ayyatu.

Kallon Ruk'ayyatu yayi cike da tsananin so, yace na gode Ruk'ayyatu kinyi min komai a rayuwa kin haife min mai kama dani na gode Allah yayi maki albarka, Ruk'ayyatu duk'ar da kanta tayi cike da kunya, sam Lami'do ya mance Gwaggo na wajen.

Gwaggo tashi tayi tana murmushi, tabbas ita ma Ruk'ayyatun ta birgeta don yarinyar duk Lami'do ne farin Ruk'ayyatu ta biyo, addu'a sosai Gwaggo tayi masu, tasan ba k'aramin so Lami'do keyiwa Ruk'ayyatu ba.

Duk da ta lura ko Ruk'ayyatu komai na Lami'do babba ne a gurin ta.

Gida suka wuce bayan an sallame su, kowanen su cike da farinciki, Lami'do hutu ya dauka ya dawo Bajoga, tsawon kwanaki da akayi kamin suna hidima sosai sukayiwa Ruk'ayyatu komai takeso Gwaggo da kanta zata girka mata.

Dakin Gwaggo Ruk'ayyatu ke jego, su Inna da sukazo ganin baby yan kallo suka koma, Ruk'ayyatu sai kace ita ce 'diyar Gwaggo.

Ranar suna Yarinya taci sunan Gwaggo *Fatima* suna kiranta *Zara* , Dr Ibrahim har Bajoga yaje da matarsa,sosai Lami'do yayi murna da zuwan su, yana ta mamakin halin Dr baya girman kai ko k'adan, sai da akayi sati da suna Lami'do ya koma cike da kewar Zara da Ruk'ayyatu.

Duk hidimar Zara Gwaggo ce, Faruk ya k'are boye boyen sa ya nunawa Zainab yana sonta, Faruk ya Jima yana son Zainab har Lami'do ya fahimci hakan, Gwaggo tayi murna sosai, lokacin da Lami'do yaji murmushi yayi don yasan Faruk ya Jima yana son k'aunar tasa.

Nafisa ma ta samu miji Bajoga iyayen sa suke, Abuja yake aiki.

Maimunatu cike da nasarori ta shiga ajin karshe a secondary, Inna sosai take jin da'din yanda Maimunatu ke karatu, ko fuska Maimunatu bata ba masu zuwa wajenta ba, tace sai ta kammalla karatun secondary ta fara wani.

**** ****

Bayan sunan Zara da sati biyu Zuri'ar Baffa Buba suka tashi cikin tashin hankalin rashin mijin Adda Saudi, hankalin su ya tashi sosai.

Ha'darin mota yayi a hanyar su ta dawo daga Lagos inda yake kasuwancin ci, ha'darin yayi Muni sosai,akasarin Mutanen da suka mutu nan inda akayi suka cika ko asibiti baa samu kai su ba.

Sunyi kuka sosai, Adda Saudi sumar ta ukku, sosai hankalin Inna ya tashi, mijin Adda Saudi ya rasu ya barta da yara biyar duk babban shekarsa goma don haihuwar rurutsa ce.

Duk dangin su Rabi'u mijin Adda Saudi shine mai rufin asirin, da yawa yanuwan su shi ke taimaka masu.

Bayan anyi sadakar bakwai su Inna suka koma, Ruk'ayyatu saboda rasuwar suka koma Gombe, sun shirya Adda zata tsaya nan Gombe tayi takaba, in ta k'are zata koma Dukku ita da yaranta, gidan da suke ciki gidan haya ne.

Sosai Inna ta damu, tana jinjina yanda rayuwar zata kasance, abun da yasa taso Adda Saudi tayi karatu ko ta nemi kasuwancin yi tun mijinta na nan ko don yaranta.

Yaran sun rasa Mahaifi su lokacin da suke buk'atarsa.

Sosai Lami'do ke taimakon Adda Saudi, duk da suna ta shirin auren Zainab da Faruk.

**** *****

Mimi aiki yayi aiki, duk yanda taga dama haka takeyi Abubakar sosai yake shakar Mimi, buk'atar ta daya ce bata biya ba, neman matan sa sai abun da yayi gaba.

Ba abun da ya fasa, kwanciya sai taga dama takeyi da shi, ko wani abun takeso jiki na rawa zai yi mata.

Dangin sa ba kallar rashin mutunci da batayi masu, duk mai son wani abun gun Abubakar sai ya biyo hanun Mimi, duk wani bak'in Malami Mimi tasan da zaman sa, abun nata har yafi na Mumy.

Wani abun sai tayi take fa'dawa Mumy, ba k'wafa Mumy zata ce kinyi dai-dai, wani lokacin Abubakar cewa Mimi yakeyi zaiyi tafiya, Hotel yake komawa yayi kwanciyarsa, ko yayi tafiyar da mace zaiyi lokuta da dama.

Ko yan aikin gidan su San yanda Abubakar ke shakkar Mimi a gaban su sakar masa magana ta keyi.

Wani zuwa da Dr Ibrahim yayi mamaki ne ya cika, a gaban sa Mimi ke zubawa Abubakar masifa sai hank'uri yake bata, Dr Ibrahim tsaye yayi yana kallon su, sosai ya tausayawa rayuwar Abubakar, to me ke faruwa ne a gidan Abubakar din?

Cikin tsananin takaici Dr Ibrahim ya bar gidan, a gefen titi yayi parking mota ya dade yana mamakin Mimi, godiya sosai yayiwa Allah da ya ha'da sa da mace ta gari, duk da yasan rayuwar su da Abubukar din ba daya ba tun a secondary school.

Dr Ibrahim dan tallakawa ne gaba da baya, tun suna secondary k'ok'ari garesa sosai, gwabnati ta turasu karatun likitanci a waje, sanin inda ya fito yasa ya mayar da hankalin sa sosai yayi karatu har ya kawo matsayin da yake yanzun.

Tun lokacin da Abubakar na neman Mimi ya rakasa gidan su Mimin tun lokacin Dr Ibrahim yasan Abubakar ya dibo da zafi, duk da yasan yayan Abubakar din nada hali.

******

Bayan wata biyu aka yi auren Faruk da Zainab, Nafisa da angonta, Ruk'ayyatu Sune manyan biki, lokacin Lami'do yasamu promotion a office yana taimakon Baffa sosai.

Adda Saudi bayan ta k'are wanka Dukku ta koma gidan su. Watarana Lami'do na office ya fara jin zazafi da ciwon kai mai tsananin, gida ya wuce, tuk'in ma da k'yar ya isa gida.

Ruk'ayyatu nayiwa Zara wanka ya shigo rik'e da kai cikin tashin hankali ta fitar da Zara cikin robbar wanka ta riko shi.

Cikin falo suka shiga yace kansa ke ciwo yana jin zazafi sosai, Faruk ta kira ya kai su asibiti, hankalin Ruk'ayyatu ya tashi sosai.

*Ummu Asma'u (Sa'adatu*)

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now