MUGUN ZALUNCI 35-36

275 20 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 35⚜36

Sai bayan kwana biyu da dawowar su Abubakar Mimi ta dawo, cikin kwana biyun sosai suke magana da Ruk'ayyatu a waya, cikin gidan da Mimi take aka fara gyaran gefe daya, gefe biyu ne, dayan na Mimi dayan suka barsa kamar guests house, Dr Ibrahim da Alhaji Mansur sun bu'dawa Abubukar wuta sosai dole yasa aka fara gyaran gefen, ba kicin a gefen aka fitar da kicin.

Ranar da Mimi ta dawo Abubakar ya fita gurin aiki, cikin mamaki take kallon gefen gidan bak'in me ake gyara a wajen? tambayar da takeyi a zuci, tunaninta ko bak'i zaiyi aiko in yanuwansa ne zasu ga tsabar rashin mutunci, sam  Mimi bata kawo aure a ranta ba.

Cikin gidan ta wuce yan aiki ta sai kwasar gaisuwa sukeyi tana 'daga masu hannu, Sunday ta kira babban Cook dinta, tana tambayar sa gyara me akeyi a guest house? ya fa'da mata suma basu sani ba oga ne yakawo masu aikin.

Fita maganar guest house tayi ta ciga da hidimomin ta, Abubakar na office Dr Ibrahim ya same sa, Dr ya tambaye sa in ya fa'dawa Mimi? Abubakar yace koda muka dawo taje Lagos da Mumy, Dr cikin mamaki yace amman banji kana maganar zasuyi tafiya, ranar da muka dawo ma naga kana tambayar ya zakayi da ita.

Abubakar kauda kansa yayi yace na mance ne, Dr Ibrahim murmushi yayi don yasan ya fa'di ne kurum don kar yayi masa magana ko yaga laifin Mimi, Dr Ibrahim tashi yayi yace gara ka fa'dawa matarka kwanakin  suna tafiya, muncewa mutanen cikin sati biyu zata tare, Dr yace kayi addu'a kamin ka tunkari Mimi don tsoron da kake yi mata mamaki yake bani, Abubakar ha'de fuska yayi don ko ka'dan bayason a fa'di laifin Mimi.

Bayan Dr ya wuce kayansa ya ha'da zuwa gida Sam bayada natsuwa ya rasa yanda zai fa'dawa Mimi, koda ya isa gida Mimi na falo hakimce tana kallo, cikin jin da'di ya shiga falon yace ashe kun dawo sannun ku da zuwa, Mimi tayi murmushi tace Honorable ya aiki, Zama yayi gefenta ya janyo ta jikin sa yace gani na dawo Gimbaya, kwantawa tayi jikinsa tana murmushi, Abubakar da'di ya cika sa duk da yasan in irin haka ta faru abu biyu ne.

Ko Mimi nason kudi ko tanan son ya tara da ita, su Mimi manya duk ajin nan😂, bed room din Abubakar din suka wuce, bayan komai ya lafa, Abubakar yace Mimi ta fa'di duk abun da takeso zai mata, kallonsa tayi ta k'ara rungumesa tunaninta abun da tayi amfani dashi ne don zuwan su Lagos, an ha'da su da wani tsohon bayarbe ya basu wani turare ita da Mumy na mallaka ne zaka shafa kasa a k'asanka, shine ta kasa bari har dare ta gwada.

Wasu Abubuwan in Mumy ta amsowa Mimi zata amsawa kanta, buk'atar kowa ya mallaki mijin sa, Mimi tace maganar bude Super Market dina da saloon, ka bani Jari in fara zuwa Dubai business, Abubakar jiki na rawa yace an k'are Gimbaya, shiru yayi yana tunanin ina zai fara, tuno addu'a da Dr yace yayi, sunan Allah ya fara kira a zuciya.

Natsuwa yaji, kamar wanda aka budewa baki, yace nayi aure a Gombe, bayan sati biyu zata tare, shine ake gyara guest house, Mimi a tsorace ta tashi, dariya ta fashe dashi, tace haba Honorable banason irin wanan wasar is too expensive, Abubakar kallon ta yayi Ido cikin Ido yace an daura min aure da Ruk'ayyatu, a Dukku, bayan sati biyu zata tare.

Mimi ihu ta k'urma, ta shak'o wuyan Abubakar cikin tsananin tashin hankali tace kayi ka'dan Abubakar baka isa ba, in zaka ci amana wallahi yau ko in ko kai a gidan nan, nafi son rasa rayuwata da kayi min kishiya.

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now