6.

942 106 22
                                    

Disclaimer: Please read previous chapter again to avoid confusion. Me sef I had to read it again 😅

6.

Muazzam bai yi shirin dawowa gida ba sai bayan la'asar. Hakan ma Mujahid yana ta mishi mita wai daga zuwa zai tafi. Ya dai bashi hakuri yace yana da wasu uzurirrika ne. Shi da Aisha suka mishi rakiya har kofar gida tare da sake tuna mishi zasu kawo masa Hidaya.

Da murmushi a bakinshi ya fita a gidan.

Sai da ya tsaya yayi sallah sannan ya wuce Subway Station.

Yana zaune yana dan danne danne a wayarsa ne yaga email ya shigo mishi. Ya lura kuma  cewa ba daga wajen aiki bane. Don haka ya yanke shawarar sai ya koma gida zai karanta.

Saukarsu da wuya, ya yi tattaki zuwa wani bakery wanda ya shahara wajen yin samfurin biredi iri daban wanda suka samo asali daga kasashe daban-daban na duniya. Layi ne a gaban wajen da ake yin oda,  don haka shi ma  ya bi layin har yazo kanshi. Croissants da Baguette ya ce ya ke so. Aka fada mishi kudin su ya mika katinsa. Bayan an cire kudin aka bashi rasiti ya karasa gurin wanda zai bashi odarsa ya mika masa rasitin. Bayan mutumin da ke bayan kanta ya karanta abunda ke jikin rasitin sai ya dauko masa duk abubuwan da ya bukata ya saka masa a brown paper bag ya mika masa. Da murmushi dauke a fuskarsa ya ce ya gode sannan ya fita.

Bata tsammace shi a wannan yammacin ba don haka da ta bude kofar ta ganshi tsaye sai da ta dan kankance idon ta alamar tambaya.

"Are you okay?" Ta tambayeshi.

Bai bata amsa ba ya jawo ta barin jikinshi suka qarasa cikin falon nata. Kwamfyutarta ya gani a ajiye akan kujera ga kuma wasu takaddu ta bazasu a kan kafet. Da alama tana aiki ya katse ta.

"Na je Long Island ne, shi ne nace bari na tsaya mu gaisa kafin na karasa gida" ya bata amsa yayinda ya wuce zuwa kitchen din ta. Plate ya samo ya zuba  Croissants din a ciki sannan ya dauko fresh milk  cikin fridge ya zuba a kofi ya fito.

Ta maida kwamfyutar kan cinyoyinta tana nazarin abun da ke kai. "Yaya su ke?"

"Lafiya kalau. Su na gaishe ki"

Ta ji dadin cewa yanzu har yana fita ziyara wajen abokai amma bata nuna masa hakan ba.

Shiru ya biyo baya, shi yana cin abincin sa ita kuma tana aikinta. Bayan wani dan lokaci ta kammala sannan ta kashe kwamfyutar ta ajiye ta gefe. Ta zare gilashin idonta ta dan mutsutsuka su sannan ta dube shi.

"Ina da tafiya zuwa Najeriya"

Ya dago ya kalleta, amma bai ce komai ba. Yana jira ta mishi karin bayani.

"Jikin Mama Amina ne yayi tsanani. Ina so naje na dubo ta."

Ya sunkuyar da kai.

Mama Amina ita ce mariqiyar Ammansa tun lokacin da  mahaifiyar ra ta rasu. Idan bai manta ba ma kamar ita ce ta yaye shi. A iya saninsa, ba shi da wata Kaka ta wajen uwa kamar Mama Aminan.

"Allah sarki. Allah ubangiji ya tashi kafadunta."

"Ameen"

"Yaushe ne tafiyar?"

Ta nisa tare da nutsewa cikin kujerar tata mai taushi. "Next month. Ina tunani ko zaka rakani?"

Ya hadiye wani abu mai daci. Baya tunanin zai iya haduwa da kowa a yanayin da ya ke ciki. Tabbas idan suka gamu da 'yan uwansa- wanda dole hakan sai ya faru, yayi amanna sai sun mishi ta'aziyya duk da kuwa an shafe kusan wata shida da rasuwar. Shi kuma a halin yanzu ba abin da baya son ji a rayuwar sa kamar a tuna  masa da cewa Najma ta rasu.

MaktoubDonde viven las historias. Descúbrelo ahora