3.

3.2K 256 62
                                    

It's been a while. I'm really sorry.

3.

Ranar da Baffa Dattijo yazo, saida ya tsaya yaji bayani daga wajen Umma harda ma ita Anti Mamin. Don haka washegari da safe tareda Mamin suka bar garin zuwa Kano inda zata cigaba da iddarta a gidan sa. A cewar sa, wannan ne kadai abinda za'ayi wanda zai kade fitina tsakanin Umma da Abbansu Bilaal tunda har yace ta bar gidan. Umma bataso hakan ba, amma babu yadda ta iya.

Kamar daga sama ta ganshi. Shi da yace kwana hudu zaiyi sai gashi da hantsin ranar Alhamis.

Dayake duk yaran suna makaranta don haka ita kadai ce a falon tana sauraron rediyo. Shigowarshi ta razana ta don batayi tsammanin ganin shi a wannan lokacin ba.

Abun mamaki, da sallama a bakinshi ya shigo falon. Da qyar harshenta ya amsa sallamar tsabar kaduwa da kuma mamaki.

Ya samu waje ya zauna a kan 'yar kujerar falon. Umma ta zuba mishi ido. Mutuminda idan ya shigo falon a bakin qofa yake tsayawa yau shine harda zama. Yau tana ganin ikon ArRahamanu.

"Sannu da dawowa" Kawai tace a taqaice.

Kai ya gyada mata sannan ya cire hularsa. Sukayi shiru. Tana so ta tashi, ko da ruwa ne ta kawo masa amma tana tsoron kar ya gwasaleta. Don haka ta sake nade qafarta tana jiran jin alkaba'in daya shigo dashi.

"Ina Mariya?"

Jin tambayar tayi wata banbarakwai. Ita ke auren Mariya ne da zata san inda take? Ko kuwa dai da wata manufa yayi tambayar?

"Dama ba tare kukayi tafiyar ba?"

Idanu ya zubo mata kamar a lokacin ya fara ganin ta. Ya saukar da murya "Zuwa ina?"

Kasa gasgata abinda ke gabanta take. Wai yau Abban Bilal ne yake magana kamar an mishi saukan ruwan qanqara? Sai wani saukarda murya yake. Lafiyarsa kuwa? Koma dai meye manufarsa a shirye take da ta hadiye duk wani rashin mutunci.

Ta tabe baki. "Haka tace zata maka rakiya"

Ya yi wata doguwar ajiyar zuciya kafin ya miqe. Ya dauki hularsa, saidai bai maidata kanshi ba. "Idan bazaki damu ba keda yaran kuje Shira ku dan kwana biyu" ya fadi yayinda ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro 'yan dubu-dubu guda uku ya miqa mata "ga kudin mota sauran kuyi tsaraba".

Umma dai tsaya wa tayi tana jiran taji wani ya tabata ko wani dalilin da zai sa ta farka daga wannan mafarkin da ta keyi.

Dubu uku? Mene? Rabonta da....

"Ki karba mana"

Sai a lokacin ta dawo hayyacinta. Ya na nan tsaye ga kudin a hannunshi na dama yana miqa mata.

Hannu na rawa ta sa ta karba. "Angode"

Ya zura takalmansa "A gaida su Dada Yelwa" abinda yace kenan kafin ya fice daga sashen.

Ai yanda kasan an shukata haka ta zauna a wajen babu abunda bai zo ranta ba. Kodai bashida lafiya ne? Halan yaje an gano yana da wata mummunar cutar shine yake so ya lallabasu a rabu lafiya kafin ya mutu. Ko kuma dai wata muguntar yake shirin mata. Wataqil ma gidan zai siyar shine zaice taje gurin qanwar mahaifiyar ta ta.

Kanta ya kasa yin lissafin wannan al'amari. To gashi baice yaushe zata dawo ba. To zama zatayi har sai yace ta koma? Sa'ar ta daya su Lawiza a gidan Antinsu zasu kwana tunda washegari Mariyar zata dawo.

Ta nisa. Sam hankalinta bai kwanta da wannan tafiyar ba.

Allah shine masani akan komai.

Tana shiga daki sai ta dauro alwala. Sallah raka'a biyu ta gabatar, inda ta shafe lokaci mai tsayo tana addu'o'i cikin sujadarta. Roqon ubangiji take, wannan sabon al'amarin daya bullo, Allah ya sanya alkhairi a cikin sa. Kuma Allah ya bata ikon jure duk wani qalubale dazaizo ya wuce a 'yan wannan kwanakin. Hawaye jiqe a fuskarta a lokacinda ta sallame sallar. Ta sharesu, sannan ta jero wasu Azkaar din.

MaktoubWhere stories live. Discover now