31.

905 116 72
                                    

Can na hango wani comment wai ana cewa those that have my contact should start calling me 🤣. Nace babbar magana. Barin zo nayi updating kafin a fara sallama a kofar gidan mu a na nema na a dalilin labarin Fareeha da Uncle Captain dinta.

Assalamu Alaikum my darlings ❤. Ba ni da kalaman da zanyi amfani da su wajen baku hakuri. Life happened. I didn't know it'd take this long before I updated another chapter, but here we are.

Please accept this as a token of apology. I really do hope you love this chapter.


31.


Abun mamaki sun bar Azare shiru-shiru kamar ba biki ake ba, suna isa Kano sai ga jama'a cike a gidan Ammah, har sai da tayi mamakin yanda aka tarkato kan jama'ar ganin cewa auren yazo bagtatan.

Motar su na tsayawa aka bude murfin kofar baya sai ga Yusrah ta leko kai.

"Wa nake gani haka kamar amaryar Uncle Captain ?"

Fareeha ta banka mata harara, hakan yasa Yusrah tuntsure wa da dariya.

"Su Uncle Captain za'a sha tsiwa kam. Yanzu ni dai lullube fuskarki na rakaki ciki"

Hannunta Yusrah ta mika mata ta taimaka mata ta fito a motar kanta a kasa. Nan da nan sauran jama'ar da ke harabar gidan suka zagayeta ana ta maraba da zuwan amarya.

Har falon Ammah suka rakata inda Amman ita ma ke zagaye da jama'arta.

Sanya ta tayi cikin rikon ta tana mai farin ciki da shigowar Fareeha cikin zuri'ar ta. Addu'o'i ta jero mata kafin nan ta zaunar da ita akan kujerar da ta tashi akai. Anti Bebi ce tazo ta zauna kusa da ita tana dan dafa kafadar ta. A hankali ta rada mata 'Barakallahu lakuma wa Baraka alaikuma wa jama'a baynakuma fii khair'.

Zata iya cewa a lokacin kaf wajen bayan Ammah a farin ciki sai ita.

Tun bayan da Ashraf yayi aure ta shiga zullumi kan batun yarinyar. Dama shi ne take tunanin zai taimaka mata kan kudurin da ta dauka akan Fareehar, sai gashi shi kuma ba hakan yake tunani ba.

Ashe ashe Allah ya shirya wani babban lamari a kansu. Gashi yanzu Fareeha ta zama matar kaninta.

Allah kenan. Shi ba ruwanShi.

Bayan an gama shigowa kowa ya natsa sai Anti Balaraba ta fara jawabi da godiya wa Allah da ya nuna musu wannan ranar tare da yin 'yar takaitacciyar naseeha zuwa ga amarya.

Fareeha dai tana kudundune cikin mayafi ta ma kasa dagowa taga su waye a falon.

Haka dai tayi ta jin muryoyi kowacce da dan guntun shawarar da zata bayar hade kuma da yin addu'a.

Bayan an kammala aka shigar da amarya daga ciki domin ta yi sallah ta dan huta.

Tun da suka shiga dakin kuwa Yusrah ta kasa barin ta ta sha iska in banda zolaya ba abinda take mata.

"Nikam ba ce min kikai babu komai tsakanin ku ba? Har da ce min wai gaisawa kawai kuke. Gashi yanzu gaisuwa ta kawo mu zuwa nan"

Fadila ce ta zungureta amma hakan bai sa tayi shiru ba.

Fareeha dai kawai murmushi tayi don kwata-kwata bata da karfin mayar mata da martani a lokacin don gaba daya jikinta wani sanyi yayi.

Bandaki ta shiga tayi alwala ta zo ta gabatar da sallar la'asar. Tana idarwa kuwa sai ga shi an fara kiran Maghreb don haka ta tashi ta sauke farali.

Anti Balaraba ce ta shigo dakin tare da wata mata da Fareeha ta lura suna kama da Ammah.

"Yusrah ku je ku shigo mata da abinci idan ta ci sai ku tayata shiryawa." Anti Balaraba ta fada tana ajiye wata leda me kyau a kan gadon dakin. "Ga wannan ki saka inji angon ki"

MaktoubWhere stories live. Discover now