15.

679 115 127
                                    

Masha Allah guys. Thank you so much for loving this book. I see you all my loyal readers and I appreciate you all. Kullum kuna commenting kuna voting, you guys give me ginger. Sending all my love❤.

"Yanzu Adda sai yaushe?"

Fareeha ta yi murmushi a yayinda take tankade flour dake cikin rariyar hannunta. Wainar flour zata yi musu ita da su Inayaah. Tunda ta dawo a hutu suke damunta cewar suna so su ci shine sai yanzu ta samu daman yi musu.

Ta kalli Maman Walid dake  zaune a kan kujerar tsuguno a tsakar gidan tasu. Bata jima da shigowa ba ta kawo mata cin-cin da dakakken yajin tafarnuwa. Ita kam bata gajiya. Duk sanda taji Fareeha zata koma makaranta sai ta samu abinda zata kawo mata ta tafi dashi.

"Wata bakwai zamuyi Maman Walid. Saboda jarabawar da zamu rubuta don haka bamu da hutu, zamu tsaya extension har kashi biyu. Sai bayan munyi WAEC tukunna zamu dan dawo hutun intervals"

Maman Walid ta rike habarta cikeda mamaki. "Wata bakwai? Kai amma zakusha zama. Allah dai ya sa wa karatun albarka"

"Amin Amin" Fareeha ta amsa bayan ta mike da niyyar shiga kitchen dinsu. Ita kanta bata son komawa makaranta wannan karon saboda dadewar daza suyi. Shekara biyu kenan ana neman na uku yanzu amma sam ta kasa sabawa da yin nisa da gida. Kowani komawa kuwa babu fashi sai tayi kuka. Wannan karon dai farin cikinta daya shine suna dawowa za ai bikin Adda Samha. Ta ji Anti Bebi ma tana cewa abinda yasa aka daga bikin saboda suma su samu ne.

Shiri ake tayi ba kakkautawa don Anti Bebin ta kasa zama waje daya. Siyayya take ta yiwa 'yar tata ba kama hannun yaro. Kayan daki ma tace a Turkey zataje ta siyo mata su. Shi dai Bappah yace kudin hannunsa na yin gado a Gandun Albasa ne, bashi da kudin zuwa Turkey. Kayan kitchen kam dai jirgi ta hau har Lagos taje ta kwaso mata su himili guda. Babu abun da bata bari ba.

"So nake na gama komai tukunna sai na zauna na fara shirin yadda za a tsara bikin. Banaso na hada hidimar siyayya ta da sha'anin event planning, kai na zai kulle" abinda tace wa Bappah kenan da yace yakamata ta tsagaita da siye-siyen nata tunda bikin da saura.

"To duk ke zakiyi komai? Ki bada wasu ayyukan ma wasu mana"

"I want everything to be perfect"

Fadila dai tayi wa Yusrah da Fareeha alkawarin zata tsaya tsayin daka ta tabbatar an musu dinkuna masu kyau kuma an siya musu komai dazasuyi amfani dashi a bikin me kyau. Ita dai Fareeha fatanta daya ne, Allah yasa Ya Ashraf ya dawo a lokacin bikin don tun wannan zuwan dayayi bata kara saka shi a idonta ba. Kuma babu abinda takeso illa ta ganshi din.

Tuni ta gane cewa ba komai bane yake faruwa da ita illa sonshi daya shige zuciyarta ya kwanta luf.

Lokuta dayawa takanji Fadila na cewa sunyi chatting da shi a Facebook kuma yace yana gaishe su duka. Yakan kira kuma su gaggaisa amma ita bata taba karambanin cewa a bata su gaisa ba. Hasali ma, gabanta ne yake faduwa duk sanda taji ana waya da shi, sai tayi sauri ta bar wajen.

Ranar dai tayi subutar baki ta tambayi Yusrah ko yaushe Ya Ashraf zai dawo? Yusrahn tace sai ya kammala defense dinshi na thesis kuma yana dan daukan lokaci.

Abun mamaki tun ranar dataji haka, sai ta samu kanta da yi masa Addu'a duk sanda tayi sujjada akan Allah ya bashi nasara ya kuma dawo dashi lafiya. Kaman hakan bai ishi zuciyar ta ba kuma, sai gashi tana zana harafin  a littafinta ko a jikin locker dinta ko kuma a tafin hannunta. Wani lokaci har dan heart take zagayewa a jikin harafin.

Ranar da kawarta Sajida Modibbo ta gani ta tambayeta meye A? Sai tace "Abubakar mana. As in  Hauwa'u Abubakar". Ita kanta abun ya bata dariya data tuna daga baya.

MaktoubWhere stories live. Discover now