35.

998 105 116
                                    

Dan Allah kuyi hakuri jama'a ta. So many things happened tsakanin December to January and I got so busy. Alhamdulillah I'm still busy din dai haka na samu na dage na cije na yi updating.

I do hope you like this chapter. Thank you all for your patience and unwavering support.

35.

Zuciyar ta bata dena harbawa ko bayan ya fita a dakin. Sai da tayi da gaske tukunna ta samu daidaituwar numfashin ta. Sai a lokacin ne kuma ta nutsu tayi tunanin abun da ya faru.

Tabbas ta ji fargaba a lokacin data waiga taga daga ita sai shi a daki kuma tasan aje aje me ze biyo baya. Baza tace har yanzu bata manta rudanin data shiga ba a lokacin da aka kusa keta mata haddi, saidai a watannin da suka shafe tsakanin shigowar Mu'azzam rayuwar ta zuwa ga auren su ya damuwowi dayawa sun gushe a rayuwar ta.

A yau dinma ta kudurce a ranta cewa ko da me yazo mata da shi zatayi kokari  manta wancan abun da ya faru don shi dai kam tasan bazai taba cutar da ita ba, sai kuma cikin rashin sa'a aka samu akasin hakan.

Kallon kofar dakin ta ke taga ko zai shigo amma shiru. Hakan ya kara tabbatar mata da cewa a can falon zai kwana kenan.

Sam hakan be mata dadi ba.

Ta so ta danne komai kamar yadda shima ya danne komai ya bayyana mata soyayyarsa; don dai tasan duk son dayake mata hakan ba wai ya nuna cewa ya manta da matarsa data rasu bane ko kuma labarin ta ya shafe a rayuwarsa. Shima dauriyar yake yi, don haka ita ma yakamata ta daure.

Share dan guntun hawayen daya gangaro mata tayi sannan ta mike ta nufin falon.

Yana nan kwance a kan doguwar kujerar tsawon lokaci, yayi nisa a sake-saken da yake don haka bai ji fitowar ta ba sai kawai ya ganta a tsaye a kansa.

A hankali ya tashi ya zauna yana fadin "Is everything okay? Kina son wani abun ne?"

Girgiza masa kai tayi, idanunta a kasa.

"Naga ka kwanta a nan ne, ka tashi ka dawo ciki"

Shafa fuskar sa yayi ya dan yi guntun murmushi. "Nan din ma ya ishe ni. Ki koma kiyi kwanciyar ki"

Wani abu ta hadiya kafin nan ta zauna a kasa daidai kafar sa ta cigaba da magana "Idan akan abun da ya faru ne dazu kayi hakuri. Kawai firgita nayi saboda baccin dana keyi a lokacin. Kar kayi tunanin ko gudun ka nakeyi"

Kallon idon ta yake yana so ya hango abin da yake gani a cikins su. Shin tsoro ne yake hango wa a cikin su ko kuwa akasin hakan?

Bai ga laifin ta ba idan ta tsorata a halin da suka tsinci kan su, don za'a iya cewa yau ce rana ta farko da suka tsinci kan su a waje guda. Lokutan da hakan ya faru a baya ya kasance akwai wasu mutane a cikin gidan da su ke, yanzu kuwa daga su sai Rabbis Samawati. Shi kan shi yaji canjin yanayin iskar da ke kai-komo a tsakanin su.

"Ki daina bani hakuri Faree. Ni ban ji haushi ba. Daman plan dina na kwana a nan ne, ba dalilinki bane yasa na dawo nan din. Don haka kije ki kwanta abinki"

Hannu ta sa ta dafa gwiwarsa, cikin raunanniyar murya ta ce "Please".

Ba sai ta sake nanatawa ba.

Hannunta ya kama ya daga ta tsaye sannan suka wuce dakin.

Daga lallausan duvet din da ke kan gadon yayi yana mata nuni data kwanta. Jiki babu kwari ta hau ta kwanta. Bayan ya lullubeta ya kashe wutar dakin sannan ya zagayo ya kwanta ta daya barin.

Idan aka ce mata a wannan lokacin yana jiyo karar bugun zuciyar ta baza ta musa ba saboda yanda take ji karar ya cika mata kunne da kwakwalwa. Jikin ta har wani kyarman sanyi yake dukda hijabin da ke jikin ta da kuma bargon da ya lulluba mata.

MaktoubWhere stories live. Discover now