17.

621 108 145
                                    

Wayewar garin ranar Alhamis ya tsinci sakon Misriyyah a wayarsa. Tun kwanciyar Ammah a asibiti daya fada mata cewa yanzu bashi da lokacin da  zasu zauna suyi magana saboda wasu dalilai, bai sake ji daga gareta ba. Hasali ma blocking layinta yayi din gaba daya hankalinshi yayi kan Ammah. Yanzun ma da bakuwar lamba aka turo masa sakon kuma bisa dukkan alamu ita ce.

I can't wait any longer for you to clear your head and sort your thoughts. Na so ace mun zauna munyi magana ta fahimta da kai amma baka bani wannan damar ba. Ina maka fatan alheri da samun nutsuwa a rayuwa don nikam na rasa tawa. I'll be leaving the country for a while and I'll not like to get in touch. Thank you.

Ya dan yi jimm yana sake karanta sakon. Ji yayi jikinsa ya masa nauyi. Yayi kokarin kiran lambar sai ya sameta a kashe. Ya gwada daya layin ta wanda yayi blocking din shima a kashe. To idan ya kiratan ma me ze ce mata? Bashi da wasu kalamai masu taushi da zai yi amfani da su. Bai san ma takameme me ze mata ba. Hakuri zai bata? Lallashinta zai yi? Oho.

Kwanaki biyu suka rage mishi kafin ya koma bakin aikinsa don haka yana so ya koma cikin karfin gwiwa. Baya bukatar wani damuwa ko tunani suzo su shige mishi jiki har ma yayi sanadiyyar sake faduwarsa gwaji.

Ajiyar zuciya yayi tare da goge message din a wayarsa sannan ya tashi ya shiga kitchen dinsa don hada abun shan ruwa. Yau da azumin nafila ya tashi kuma Alhamdulillah bai wujijiga shi ba.

Sandwich ya yi wanda yasha kayan lambu da kwai da tuna. Akwai sauran yam balls din da Ammah ta aiko masa ranar litinin da sukayi waya yace mata yana azumi, zai hada da shi ya sha ruwa. Yau ma yayi tunanin ko za ta mishi wani aiken amma shiru.

Yana tsaye anan kitchen din wayarsa ta dauku ruri da kiran sallan Maghreb daga Adhan App dinshi. Dabino ya tauna yayi addua sannan ya kora da orange drink.



●●●●●

A Kano kuwa Fareeha suna ta shirin zuwa gida don sun samu hutun intervals. Sun kammala zana jarabawarsu ta WAEC kuma Alhamdulillah suna fatan samun nasara mai dinbin yawa.

Hutun ya kama ranar Jumu'ah.

Suna tashi da safe kowa tayi duty din ta suka tattara kayayyakinsu zuwa bakin hostel ta yanda zai musu dadin dauka idan an zo daukansu. Bayan sun karya (dukda ba kowa bane yake karyawa ranar hutu) principal ta tarasu a dining hall din ta musu nasiha akan idan sun tafi hutu kar su shagala da wasu abubuwan, su tuna cewa wata jarabawar tana jiransu kuma.

Ko bayan an watse Fareeha da kawarta Sajida suka cigaba da zama a dining din suna 'yar hirarsu. Sai zuwa akayi akace mata wai anzo daukansu. Ta duba agogon cikin dining hall din taga har goma da kwata. Karfe goma kuma ake bude gate. Sun tsaya hira bata ma san har lokacin bude gate din yayi ba.

Nan ta shiga neman Yusrah don suje su dauko kayayyakinsu.

A class dinsu ta sameta itama anata hayaniya da kawaye. Tare suka karasa wajen reception. Suna zuwa kuwa suka ga Anti Bebi ce da kanta tazo. Da gudu Yusrah ta ruga wajen Mamanta ta kankameta. Fareeha ma murmushi ta saka wanda ya nuna jin dadinta.

Suka harhado kayansu suka jawo zuwa gate din. Anti Bebi ta gama signing abunda zatayi signing ta fito suka tafi.

Tana zuwa jikin motan kawai taji jikinta yayi sanyi. Ko ba a fada mata ba tasan shi ne a cikin motan. Kafin tayi wani abu Anti Bebi tace "Ashraf a bude boot"

Ta cikin motar ya bude sannan ya fito ya zagayo don yazo ya tayasu saka kayan a cikin.

"Yaya ina kwana?" Ita da Yusrah suka fada a tare.

"Lafiya kalau. Yau kuna ta jin dadi zaku tafi gida ko?"

Yusrah ce ta bashi amsa inda ita kuma Fareeha idon ta suna kasa. Cuccusa kayan ta tayi a boot din tayi saurin shiga motar.

MaktoubWhere stories live. Discover now