33.

985 124 49
                                    

Salaam guys! Ya mukaji da abun da ke faruwa a Gaza da ma duniyar baki daya? Allah ya kawo karshe abunnan da alkhairi and May Allah continue to keep the Muslim Ummah safe from oppressors. Ameen.

Bari mu leka gidan Ashraf da Wafiyya muga meke wakana.








33.

Karfe tara da rabi har da minti biyar agogon dake manne a jikin bango ya nuna.

Ashraf ya sauke ajiyar zuciya tare da mikewa ya shiga kitchen din. Ya ga alama Wafiyya bata da niyyar dawowa don haka ya shiga nema wa kansa abin da zai ci.

In da sabo yanzu kam har ya saba don tun da ta koma zuwa shagonsu yawanci sai ya dawo gida ya samu bata nan. Tun yana jiran ta ta dawo ta nema masa abinci har yazo yanzu yana dawowa yaga bata nan to zai nema wa kansa mafita.

Freezer ya bude ya lelleka ko zai ga sauran abincin da zai dumama. Couscous ya gani a cikin wata container wanda akayi shekaranjiya. Ya dauko ya saka a microwave sannan ya hau soya kwai.

Sai da ya kammala ya fito falo ya zauna tukunna yaji tsayuwar motar ta.

Yana jin shigowar su ita da kanwar ta Mumtaz, bai ce musu komai ba.

"Ina wuni Ya Ashraf?" Mumtaz din ta fada tana shigowa niki-niki da ledojin souvenir a hannunta.

A hankali ya dago ya kalleta tare da kakalo murmushi ya amsa da "Lafiya Mumtaz. Sannunku da dawowa"

Gyada kai tayi ta wuce dakin da tayi masauki.

Tsawon sati uku kenan yanzu da ta fara zama a gidan nashi tunda suka samu sabani da daya daga cikin matan babanta har aka kai ga yin dambe, shine da Baban ya tsawatar mata ita kuma taji haushi ta tattaro ta dawo gidan yayar ta.

Shi dai Ashraf ya je ya bawa mahaifin nasu hakuri kuma yace ya hakura, bai dai san dalilin daya sa har yanzun bata tattara kayan ta ta koma gidan su ba.

"Hayaat ka ganmu sai yanzu ko? Wallahi souvenirs muka tsaya rabawa a haka ma wasu ban samesu ba sai taho musu da shi nayi gobe na basu"

A karo na biyu Ashraf ya dago da kansa daga kan abincin sa ya fuskanci matar sa wanda ke tsaye a wajen kofa tana kokarin cire takalminta mai tsini.

Har yanzu makeup din ta yana nan daram a fuskarta kamar ba'a shafe awowi da yin sa ba. Jambakin nan radau akan lebbanta.

Bin shigar da ke jikin ta yayi da kallo.

Lokacin da suka rabu da safe doguwar Abaya ce a jikin ta. Yanzu kuwa wani hadadden leshi ne a jikinta ruwan goro wanda aka masa dinkin fitted gown. Yana tsammanin shine ankon bikin don irin sa ne a jikin Mumtaz.

Dinkin yayi mata kyau matuka gashi kalar leshin ya sake fito da hasken fatar ta.

A ranshi yake tunanin idan shi mijin ta ya shiririce haka wajen kallon ta, to maza nawa ne a yau suka samu damar yin haka?. Saurin kauda tunanin yayi a ranshi dalilin wata tafarfasa da yaji zuciyar sa ta fara yi.

Jinjina kai yayi kawai ya kurbe sauran juice dinshi dake cikin kofi kafin ya mike ya shiga kitchen din dan mayar da plate din sa.

"Hayaati ina ta maka magana ka share ni" Ya jiyo muryar ta a bayan shi. "Ko duk gajiyar office dinne?"

Girgiza mata kai yayi alamar yana bukatar ta kyaleshi.

Tun ba yau ba ta san cewa idan ran sa ya baci baya son ta cika shi da surutu, amma sam taki koya. Idan yaci gaba da tsayuwa a wajen zai iya furta abun da zai yi nadama don haka ya rabata ya fice a kitchen din. Yana isa dakin sa ya saka mukulli ya shige bandaki.

MaktoubWhere stories live. Discover now